You are here: HomeAfricaBBC2021 03 14Article 1204075

BBC Hausa of Sunday, 14 March 2021

Source: BBC

Halin da na shiga lokacin da na ga 'ya ta a bidiyon da masu garkuwa suka saki - Mahaifin ɗalibar kwalejin Mando

Cikin bidiyon an ga ɗaliban suna roƙon gwamnati ta biya kuɗin fansa domin ceto su Cikin bidiyon an ga ɗaliban suna roƙon gwamnati ta biya kuɗin fansa domin ceto su

Mahaifin ɗaya daga cikin ɗaliban Kwalejin Nazarin Gandun Daji ta Tarayya dake Mando da ƴan bindiga suka yi awon gaba da su a ranar Alhamis ya shaidawa BBC halin da ya shiga, lokacin da ya ga 'yarsa a biyon da masu garkuwar suka saki a shafukan Internet,.

Cikin bidiyon an ga ɗaliban suna roƙon gwamnati ta biya kuɗin fansa domin ceto su, sannan kada a tura jami'an tsaro don ceto su, suna cewa hakan na iya haifar da haɗari ga rayuwarsu.

Wannan mahaifi wanda ya shaidawa BBC cewa ya ga 'yarsa ra'ayal aini a bidiyon ransa ya yi matuƙar ɓaci sakamakon ganin 'yarsa a halin ƙunci da ya ganta.

Ya roƙi hukumomi su tashi tsaye wajen ceto waɗannan ɗalibai, musamman laakari da cewa mata basu da juriya kamar ta maza.

"Yadda muka ga bidiyon ba shakka suna cikin matsanancin hali, wasu ma ba riga gasu nan a ƙasa, don haka muna jira muga matakin da gwamnati za ta ɗaila don ceto su'' a cewar mahaifin yarinyar da muka sakaye sunansa.

An ceto wasu daga hannun 'yan bindigar - Gwamnatin Kaduna

Tun farko, wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya fitar ta ce sojoji sun yi nasarar kuɓutar da ɗalibai da yawa kafin 'yan bindigar su gudu da su.

"Sojojin Najeriyar sun samu nasarar ceto mutanen 180; dalibai mata 42, da malamai takwas da kuma dalibai maza 130.

Amma kuma har yanzu ba a gano sauran dalibai maza da mata kusan 30 ba", in ji Aruwan.

Kawo yanzu kusan ɗalibai 800 aka sace tun watan Disamba kuma wannan ne karo na uku da aka sace ɗalibai daga makarantunsu a shekarar 2021 a Najeriya.

A jihar Kaduna kaɗai, 'yan bindiga sun kashe mutum 937 sannan suka yi garkuwa da 1,972 a shekarar 2020.

Sanarwar ta kuma cewa dakarun soji ne suka kai dauki cikin makarantar, inda suka fafata da 'yan bindigar.

Wasu daga cikin daliban da aka ceto sun samu raunuka, kuma ana duba lafiyarsu a wani asibitiin sojoji na Kaduna, a cewar sanarwar.