You are here: HomeAfricaBBC2021 03 14Article 1204084

BBC Hausa of Sunday, 14 March 2021

Source: BBC

'Yan bindigar da suka sace ɗliban kwalejin Kaduna sun nemi miliyoyin kuɗin fansa

Wasu rahotanni na cewa 'yan bindigar sun buƙaci naira miliyan 500 a matsayin kuɗin fansa Wasu rahotanni na cewa 'yan bindigar sun buƙaci naira miliyan 500 a matsayin kuɗin fansa

'Yan bindigar da suka sace ɗaliban makarantar aikin noma ta Jihar Kaduna sun saki wasu bidiyo, inda ɗaliban ke roƙon gwamnati ta biya kuɗin fansa domin ceto su.

'Yan bindigar sun kai hari kwalejin ce da misalin ƙrfe 11:00 na daren Alhamis kuma suka yi awon gaba da mutum 39, 23 mata da kuma maza 16.

'Yan fashin sun yi amfani ne da shafukan ɗliban wurin wallafa bidiyon a Facebook. A ɗya daga cikin bidiyon, ana iya ganin yadda suke dukan ɗliban mazansu da matansu da tsabga a wani wuri da ya yi kama da tsakiyar daji.

"Waɗannan mutanen sun kewaye mu kuma sun ce duk wanda ya yi ƙoƙarin zuwa ya cece mu za su kashe mu," in ji ɗaya daga cikin ɗliban wanda ya yi magana da harshen Ingilishi.

Ya ƙara da cewa: "Sun yi mana duka har sun ji mana raunuka sosai. Wasu daga cikinmu na kukawa kan raunkan da suka ji. Idan gwamnati ba ta zo ta cece mu da wuri ba muna cikin gagarumar matsala."

Wata mace da ta yi magana da Hausa ta bayyana cewa "mutanen nan sun faɗ mana cewa idan sojoji suka yi yunƙurin cetarmu ko ɗaya daga cikinmu babu wanda zai koma gida".

A wani bidiyon, ana iya jin ɗalibai mata da ke zaune a bayan mazan suna cewa "ku ba su kuɗin fansar kawai su sake mu don Allah" cikin Hausa da Ingilishi.

Wasu rahotanni na cewa 'yan bindigar sun buƙaci naira miliyan 500 a matsayin kuɗin fansa, kamar yadda wasu iyayen ɗliban suka shaida wa jaridar Daily Trust.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sha bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa yi wa 'yan fashin dajin afuwa ba yayin da maƙotan jihohi ke cewa sun ga amfanin sulhu da su.

Sai dai ita ma gwamnatin tarayyar ƙarƙashin Muhammadu Buhari ta tabbatar da cwea ba za ta shiga maganar sulhu da 'yan fashin ba.

An ceto wasu daga hannun 'yan bindigar - Gwamnatin Kaduna



Tun farko, wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya fitar ta ce sojoji sun yi nasarar ceto ɗlibai da yawa kafin 'yan bindigar su gudu da su.

"Sojojin Najeriyar sun samu nasarar ceto mutanen 180; dalibai mata 42, da malamai takwas da kuma dalibai maza 130. Amma kuma har yanzu ba a gano sauran dalibai maza da mata kusan 30 ba", in ji Aruwan.

Kawo yanzu kusan ɗalibai 800 aka sace tun watan Disamba kuma wannan ne karo na uku da aka sace ɗalibai daga makarantunsu a shekarar 2021 a Najeriya.

A jihar Kaduna kaɗi, 'yan bindiga sun kashe mutum 937 sannan suka yi garkuwa da 1,972 a shekarar 2020.

Sanarwar ta kara da cewa dakarun soji ne suka kai dauki cikin makarantar, inda suka fafata da 'yan bindigar.

Wasu daga cikin daliban da aka ceto sun samu raunuka, kuma ana duba lafiyarsu a wani asibitiin sojoji na Kaduna, a cewar sanarwar.