You are here: HomeAfricaBBC2021 03 09Article 1199668

BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

Hirar Meghan da Harry: Na gaji da rayuwa - Meghan

Duchess ta Sussex Meghan Markle Duchess ta Sussex Meghan Markle

Duchess ta Sussex ta ce ta fuskanci ƙalubale na rayuwa a masarautar Birtaniya inda har ta kai a wasu lokuta take jin "ta ɗauki ranta".

A wata hira ta musamman da aka yi da ita ta talabijin, Meghan ta gaya wa Oprah Winfrey cewa ba a taimaka mata idan ta nemi hakan.

Ta ce wani abin takaici shi ne lokacin da wani daga cikin masarautar da ba ta ambaci sunansa ba ya tambayi Harry cewar "yaya ɓakar" fatar ɗansu Archie za ta kasance.

An tambayi ma'auratan ko sun yi ƙaura daga Birtaniya ne saboda wariyar launin fata, kuma Yarima Harry ya amsa da cewa: "yana cikin dalilan."

A wani ɓangare na bidiyon hirar da ba a saka ba a hirar ta asali, Yariman ya ce an ba shi shawarar kada ya fallasa irin wariyar da matarsa ke fuskanta a masarautar ga ƴan jarida.

Kuma an faɗa masa matsayin Birtaniya a matsayin "mai tsananin son kai". Amma ya musanta hakan da kuma batun jaridun Ingila da aka faɗa masa cewa "suna sa son rai."

Ya ƙara da cewa: "Idan har tushen wani bayani ya kasance gurɓatacce ko kuma nuna wariyar launin fata da kuma son zuciya, to wannan wata izina ce ga al'umma."

Hirar ma'auratan da Oprah wadda ta ja hankali, an watsa ta ne a Amurka.

Wasu mahimman bayanai daga hirar:

Ma'auratan sun sanar da cewa suna fatan samun ƙaruwar mace a bazara

Sun yi wa juna alƙawali a bikin da Archbishop na Canterbury ya jagoranta a "bayan gidansu" kwanaki uku kafin bikin aurensu a watan Mayun 2018

Harry ya ce ɗan uwansa da mahaifinsa "sun kasance cikin tsaka mai wuya" a tsarin masarautar

Ya ce an hana ma shi kuɗi a farkon shekarar da ta gabata kuma mahaifinsa ya daina ɗaukar kiransa

Amma Harry ya ce yana ƙaunar ɗan uwansa kuma yana son gyara dangantakarsu da kuma mahaifinsa

Meghan ta ce ta kira Sarauniya ta waya lokacin da Duke na Edinburgh yana asibiti a watan jiya

Ma'auratan sun koma Califonia da zama bayan sun sauka daga matsayinsu a masarautar a watan Maris na 2020, kuma a watan da ya gabata aka sanar da cewa ba za su dawo ba a matsayinu na ƴan gidan sarautar Birtaniya.

Meghan ta ce ta fara fuskantar rayuwar kaɗaici lokacin da aka shata mata iyaka kan abin da za ta iya, inda ta bayyana cewa akwai lokacin da ba ta fita daga gidan na tsawon watanni.

Ta ce har an kai lokacin da ta fara tunanin cewa "ba za ta iya rayuwa cikin wannan kaɗaicin ba", kamar yadda ta shaida wa Oprah.

Lokacin da Oprah ta tambaye ta cewa ko ta yi tunanin cutar da kanta da kuma tunanin kashe kanta a wani lokaci, sai ta amsa cewa: Eh. wannan haka yake, tabbas akwai ban tsoro. Ban san wanda zan dogara da shi ba a wannan yanayin."

Meghan ta ce ta shiga "wani yanayi" kan wani hoton da aka ɗauka a wani babban taron da ta halarta tare da Harry a babban ɗakin taro na Albert Hall yayin da ta ke ɗauke da juna biyu.

"Dole muka fice daga wajen taron, mun yi maganar da Harry a wannan safiyar," in ji Meghan.

Winfrey ta tambaye ta: "cewa kamar kina jin kin gaji da rayuwa?"

"Eh," Meghan ta amsa.

Ta ce ta halarci tarn tare da Harry a wannan daren saboda tana ganin bai dace ace "ba ta je ba" kuma ta tuna yadda Harry ya riƙe hannunta sosai a wajen taron.

Oprah kuma ta tambaye ta dalilin da ya sa ba gidan sarauniyar bai ayyana ɗanta Archie a matsayin Yarima ba - wanda Meghan ta ce tana ɓukata domin samun kariya daga ƴan sanda.

Ƴaƴan Duke da Duchess na Sussex ba za su zama Yarima saboda wata tsohuwar doka tun 1917 - har sai Sarauniya ta shigo ciki.

"A watannin da nake da ciki, muna tattauna cewa ba zai samu kariya ta tsaro ba, ba zai samu sarauta ba, haka kuma akwai damuwa da bayanai kan launin fatansa idan an haife shi," in ji Meghan.

Ta ce ana yi wa Harry magana kan kan launin fatansa kuma yana faɗa mata.

Sai dai ta ƙi ambatar suna, tana mai cewa: "Zai kasance abn kunya gare su."

Harry ma ya ƙi yin ƙarin bayani, yana mai ce: Wannan batu ne da ba zan taɓa faɗa ba."

"A lokacin abin ba dadi, na yi mamaki," in ji shi.

Oprah ta faɗa wa shirin safe na kafar CBS cewa Harry ya faɗa mata cewa ba Sarauniya ko Duke na Edinburgh ba ne suka yi faɗi kalaman - amma bai faɗi suna ba.

Ɗan gidan sarauniyar mai shekara 36 ya ce babu wani daga cikin ƴan uwansa da suka yi magana domin nuna goyon baya ga Meghan kan wariyar launin fata da suka fuskanta da shi da matarsa daga kafafen yaɗa labarai.

"Babu wani daga cikin dangina da suka ce uffan a tsawon shekaru uku, abin da zafi," in ji Harry.