You are here: HomeAfricaBBC2021 03 09Article 1199374

BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

Mo Ibrahim: Shugaba Issoufou na Nijar ya lashe kyautar dala miliyan 5

Shugaban Jamhuriyyar Nijar mai barin gado Mahamadou Issoufou Shugaban Jamhuriyyar Nijar mai barin gado Mahamadou Issoufou

Shugaban Jamhuriyyar Nijar mai barin gado Mahamadou Issoufou ne ya lashe lambar girma ta Gidauniyar Mo Ibrahim da kuma kyautar dala miliyan biyar, da ake bai wa shugaba na gari a nahiyar Afirka ta bana.

Gidauniyar ce ta sanar da hakan a ranar Litinin 8 ga watan Maris din 2021, bayan kammala taron da kwamitin bayar da kyautar ya shirya.

Shugaba Issoufou ya mulki Jamhuriyyar Nijar a karo biyu na shekara biyar-biyar kuma nan gaba kaɗan ne zai miƙa mulki bayan ƙarewar wa'adinsa.

Shi ne mutum na shida da ya lashe kyautar ta shugaba na gari ta Afirka ta Gidauniyar Mo Ibrahim.

An ƙaddamar da kyautar gidauniyar ne da nufin fito da shugabannin da suka yi fice wajen bunƙasa ƙasashensu, kuma suka nuna ƙwazo da jaddada dimokraɗiyya da kuma kare dokokin ƙasar don amfanin al'ummarsu.

Gidauniyar ta yabi Shugaba Issoufou ne kan ƙoƙarinsa na jagorantar ƙasar da a lokacin da ya karbi mulki ke cikin kasashe mafiya talauci na duniya, da dumbin kalubalen da ya fuskanta.

"Duk da dumbin kalubalen siyasa da tattalin arziki da rikice-rikice da ake fama da su, Shugaba Issoufou ya jagoranci mutanensa a wajen ci gaba.

"A yau yawan wadanda ke cikin talauci a Nijar ya ragu da kashi 40 cikin 100 daga kashi 48 cikin 100 cikin shekara 10 da suka wuce. Duk da wadannan kalubale Shugaba Issoufou ya cika alkawuran da ya yi wa 'yan Nijar ya kuma kawo ci gaba.

"Bayan yin nazari sosai, sai kwamitin ya gano cewa shi ne wanda ya fi cancanta da wannan kyauta ta Mo Ibrahim," a cewar sanarwar.

Ta kuma kara da cewa: "A tsawon lokacin da ya shafe a kan mulki, ya ƙarfafa tattalin arzikin kasar, ya yi biyayya ga hadin kan yankin da kuma kundin tsarin mulki, sannan ya yi tsayuwar daka wajen ƙarfafa dimokradiyyar Afirka."

A shekarar 2011 ne aka zabi Mahammadou Issoufou shugaban kasa na mulkin dimokradiyya, bayan shafe shekaru ƙasar na ƙarƙashin mulkin soja. Sannan an sake zabarsa karo na biyu a 2016, ya kuma yarda an yi zabe a 2020 don mika mulki.

Wadanda suka taba samun kyautar tun farkonta

Shugaba Nelson Mandela na Afirka Ta Kudu

Shugaba Joaquim Chissano na Mozambique

Shugaba Festus Mogae na Botswana

Shugaba Pedro Pires na Cabo Verde

Shugaba Hifikepunye Pohamba na Namibia

Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta Liberia

Mahammadou Issoufou na Jamhuriyyar Nijar.