You are here: HomeAfricaBBC2023 05 15Article 1767629

BBC Hausa of Monday, 15 May 2023

Source: BBC

Ƴar gudun-hijirar Syria da aka raba da iyayenta bayan tilasta musu komawa gida

Wani da tashi hankali a Syria ta sa ta rasa gida Wani da tashi hankali a Syria ta sa ta rasa gida

Muna cikin yanayi na dar-dar a mota yayin da muke tuki ta tsaunuka domin isa Lebanon, gidansu 'yan uwan Raghad.

Tattaunawa da wata yarinya da ta rabu da iyayenta da kuma ba ta da tabbacin lokacin sake tozali da su.

Amma muna yin tozali da ita, sai kuma samu saukin faduwar da gabanmu ke yi. Raghad na sanye da sutura masu haske an daure mata gashinta zuwa baya. Ta yi kokarin yi mana fara'a sai idonta ya sake haske.

Sakin jikin da ta nuna ya kwantar mana da hankali.

Raghad ta ƙi yin magana, don haka kawunta ya fada mana abin da ya same ta da iyayenta.

Yarinyar ta yi shiru tana sauraro. Lokaci guda da ta yi magana shi ne da ta yi kokarin yi wa kawun nata gyara lokacin da ya ke bayar da labari, ya shaida cewa shekarunta 7 lokacin da abin ya faru, ita kuma ta masa gyara tare da dagewa a kan cewa shekarunta 8 a lokacin. Nan fa aka soma muhawara. Yanayi na barkwanci a labari mai sosa rai.

Raghad a yanzu na rayuwa a wata kasa ta daban da iyayenta kuma ba ta taba samun damar yin bankwana ba.

A ranar 19 ga watan Afirilu, kwanaki biyu kafin Sallar Idin kammala Ramadana, a wannan rana sojojin Lebanon suka kai samame gidansu Raghad.

Wa'adin takardun iyayenta ya cika. Ba tare da wani ankararwa ba, an cafkesu tare da mayar da su Syria. ''Sun ce mu sanya kayanmu sannan mu dauki duk wani abu mai muhimmanci, a cewar mahaifinta ta wayar tarho.

Da misalin karfe 9 na safe ne lokacin Raghad tana makaranta. Mahaifinta ya fadamana cewa ya roko sojoji su jira ta dawo amma suka ki.

Raghad ta dawo gida ta kwankwasa kofa, amma babu kowa. Nan fa ta fashe da kuka.

''Na tsorata sosai,'' a cewarta. Wata makwabciyarsu ta iso gareta cikin gagawa. Yanzu haka gidanta Raghad take zama.

Mayar da iyayen Raghad gida na cikin tsarin tilastawa iyalai komawa Syria saboda ana musu kallon masu zama ta haramtacciyar hanya.

Iyayenta sun shafe tsawon shekaru 12 suna zaune a Labanan tun soma yakin Syia.

An haifi Raghad a Lebanan, amma iyayenta sun fito ne daga Idlib da ke arewa maso yammacin Syria, wurin da ake tafka yaki kuma har yanzu ake rigima da 'yan tawaye.

''Ka yi tunanin rayuwa a kasa na tsawon shekaru 12 lokaci guda a koreka. Ga shi ba zamu iya komawa garinmu ba saboda yanayin da muke ciki, a cewar mahaifin Raghad, wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda tsaro.

Iyayen Raghad na zama da abokai a birnin Damascus na Syria.

Na yi musu tambata kan ko suna kokarin dauko Raghad zuwa Syria, amma sai suka shaidamun sun fi son komowa Lebanan su same ta. Ba abu ne mai sauki ba.

Nuna kyama ga Syria

Mahukunta Labanon, da goyon-bayan abin da ya kasance kamar juyin-juya hali na nuna dawa da Syria a fadin kasar, sun ce suna son 'yan gudun hijira su koma kasarsu.

Lebanan na dauke da 'yan gudun hijira mafi girma a duniya idan aka kwatanta da girman al'ummarta.

Kusan 'yan Syria 800,000 aka yi wa rajista a Majalisar Dinkin Duniya, duk da cewa mahukunta Labanan sun kiyasta cewa alkaluman ya ninka wannan adadi.

A lokuta da dama a shekarun baya, anyi ta samun nuna kyama ga 'yan Syria da tsaurara dokoki da tsare-tsare domin takura musu.

Amma a wannan lokaci, muhawarar ta daban ce, sannan ana ta yada yarjejeniya kan mayar da su gida.

Gwamnatin Lebanan ta ce ba zata iya daukar nauyin 'yan gudun hijira ba, adaidai wannan lokaci da suke fuskantar matsi a fanin kudade da tattalin arziki a tarihin kasar. Sun ce 'yan gudun hijirar Syria na sake ta'azzara lamarinsu.

Haka nan sun kum daura musu alhakin matsalolin tsaro da karuwar aikata laifuka da ake samu.

Yawaitar haihuwa tsakanin 'yan Syria ya zarta haihuwar yara da ake samu a Lebanan.

Korafe-korafen sun tilastawa mahukuntan kasar tsaurara matakai kan 'yan Syria.

Garin Bikfaya a da ke kan tsauni a Beirut ya sanya dokar hana fita. ''Babu inda aka taba samun wurin da aka yiwa 'yan Syria maraba a duniya kamar yada muka karbe su,'' a cewar Magajin gari Nicole Gemayel, yana mai kare tsarin, da kungiyoyin kare hakki ke cewa na tattare da wariya.

Magoya bayan tsarin sun kuma dauko batun tsaro a Syria, inda suke cewa ana samun arangama da sojoji.

Mahukunta Lebanon sun ce dukkanin wadannan dalilai ya kamata su kawo karshen matsalar 'yan gudun hijira.

Sun kuma bayyana abin da suka kira 'balaguron da ba a halasta ba' a kan iyakoki a matsayin babban kalubale.

Sun ce wannan matsala na sake nuna bukatar mayar da 'yan Syria gida.

Sai dai sojoji na cewa su dokoki suke amfani da su, don haka mayar da 'yan syria zai kasance bisa tsari na doka.

Wasu hamshakan 'yan siyasa sun nuna a Labanan sun zargi kasahen ketare da daidaikun kungiyoyin duniya da kokarin ganin 'yan Syria sun makale a Lebanan, suna mai cewa taimakon Majalisar Dinkin Duniya na nuna kawai su zauna a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta musanta wannan batu sannan ta ce duk wanda zai koma Syria ya kasance bisa raddin kai.

Sai dai ga Raghad, duk wannan ba matsalar ta ba ce. Tayi kewar iyayenta kuma tana burin komawa gida tare da su.