You are here: HomeAfricaBBC2023 05 15Article 1767626

BBC Hausa of Monday, 15 May 2023

Source: BBC

Ɗan ƙwallon Najeriya da ya guje wa yaƙin Sudan da gajeren wando

Fada ya ɓarke a ƙasar ranar 15 ga watan Afirilu a Sudan Fada ya ɓarke a ƙasar ranar 15 ga watan Afirilu a Sudan

Charles Collins na fatan zuwa wasansu na gaba a gasar Firimiyar Sudan lokacin da faɗa ya ɓarke a ƙasar ranar 15 ga watan Afirilu, lamarin da ya mayar da birnin da yake zaune filin daga.

Ɗan ƙwallon wanda ya kasance ɗan Najeriya yana buga wa Ƙungiyar Khartoum ta Haidob en Nahud.

Ya ce dole ta sa ya bar duk abin da ya mallaka ya fice daga birnin, sanye da gajeren wandon da ke jikinsa lokacin da yaƙin tsakanin sojoji da dakarun RSF ya barke.

Yana daga cikin ƴan Najeriya 396 da suka koma Abuja daga Masar cikin wannan makon, bayan da suka tsere daga Sudan a abin da da yawa suka bayyana a matsayin tafiyar tsawon kwanaki mai haɗarin gaske.

"Na dawo gida da wannan kaɗai, bargona kaɗai," ya faɗa wa BBC a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Abuja, yana juyawa domin nuna baƙar jakar da ke rataye a bayansa.

"Na tsere daga gidana sanye da gajeren wando kawai, wani yanayi ne na tashin hankali," in ji shi.

Haidob, ƙungiyar da ta samu ci gaba zuwa matakin pirimiya a kakar bana, tana hanyar samun gurbin buga wasa a gasar zakaru ta CAF Confederations Cup - gasa ta biyu mafi daraja a Afirka.

Tawagar ta yi rashin nasara a hannun Kober SC Bhari da ci 1 - 0, mako ɗaya kafin soma yaƙin amma ta ci gaba da zama ta huɗu a gasar da a yanzu aka dakatar.

Amma bayan yanayin da ya fuskanta, Collins ba ya tunanin komawa Sudan domin ci gaba da buga ƙwallo.

Wasu ƴan wasa daga babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya sun koma Sudan cikin shekaru inda suka samu manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da ke fafatawa a gasar da ake yi a matakin nahiya.

'Yanayi ne na tashin hankali'

Collins, wanda ya shafe shekara uku da rabi a Sudan bayan da ya je ƙasar daga ƙungiyar Mauritius ta Richie Moore Rovers, ya ce ya rasa duk wani abu da ya mallaka a ƙasar har da tsabar kuɗi dala 20,000 - kwatankwacin pam 16,000.

Yana haɗa ƙwallo da sana'ar shigar da gashin da mata ke ƙarawa zuwa ƙasar domin sayarwa kuma ya kai wasu kayayyaki kwana takwas kafin faɗan ya ɓarke, wanda a yanzu ya rasa su.

"Akwai mutane da yawa da suka dawo ba tare da komai ba. Ba laifi, ni na dawo da bargo," kamar yadda ya ce da isarsa Abuja, inda yake nuna wani mutum riƙe da baƙar leda.

"Ya dawo da abincinsa kaɗai."

An yi jigilar mutanen da aka kwaso a jirage biyu - ɗaya na kamfanin Air Peace, ɗayan kuma na sojoji - daga Aswan a Masar mai maƙwabtaka. Sun shafe kwanaki maƙale a iyakar Masar saboda matsalolin da aka fuskanta da takardunsu na visa.

Kafin faɗan ya ɓarke, fiye da ƴan Najeriya 5,000 ake tunanin suna zaune a Sudan, akasari ɗalibai. Ƙasar ta yi fice kan ilimin addinin Musulunci da Larabci, wanda da yawan ƴan Najeriya ke karatu a kai.

Ƴan Najeriya sun kuma yi suna wajen zuwa karatu a kwalejojin koyar da haɗa magunguna da aikin likita da ke da sauƙin kuɗin makaranta.

An ga yanayin farin ciki a filin jirgin saman na Abuja lokacin da ƴan Najeriyar da aka kwaso suka gana da iyalansu da jami'an gwamnati.

Sai dai kuma har yanzu tashin hankalin da suka gani sabo ne a zukatansu.

Zainab Abdulqadir, wata ɗaliba, ta shaida wa BBC cewa "tafiya ce cike da tashin hankali."

Ta ce ƙafafunta sun kumbura saboda zaman da suka yi har cikin dare a mota yayin da suke tserewa daga Sudan ba tare da abinci ko ruwa ba.

"Yanayi ne na tsananin tashin hankali da tsoro da kuma rashin kwanciyar hankali," in ji ta.

Abdulazez Muiza, wata ɗaliba a Jami'ar Africa International, da ke Khartoum, wadda ƴan Najeriya da dama ke karatu a wajen, ta ce da farko ta yi zaton tartsatsin wuta ne da ta ji harbe-harben bindiga a ranar da aka soma faɗan.

"Da gajiya sosai, wasu a cikinmu na ɗauke da juna biyu... amma mun gode wa Allah cewa mun dawo gida."

Ms Muiza, wadda ke ajin farko a jami'ar, ta ce tana fatan za ta koma Sudan idan aka kawo ƙarshen yaƙin.

Jakadan Najeriya a Sudan, Muhammad Yusuf, shi ma ya yi kira ga ƴan Najeriyar da suka dawo saboda rikicin Sudan su duba yiwuwar komawa da zarar an samu dawowar zaman lafiya.