You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853936

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Ƴan sandan Najeriya na kokawa kan hare-haren da ake kai musu

Hoton alama Hoton alama

Babban sufeton 'yan sandan Najeriya ya bayyana takaici kan yadda ya ce ana samun ƙaruwar hare-haren da ake kai wa 'yan sanda a sassan ƙasar.

Egbetokun Olukayode Adeolu, ya kuma yi kashedi da kakkausan harshe game da hakan.

Shugaban 'yan sandan ya bayar da umarni a gudanar da cikakken bincike kan ire-iren waɗannan hare-hare, don a zaƙulo waɗanda suke aikata hakan, kuma a hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

CSP Al-Mustafa Sani, babban jami'i a ofishin hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Najeriyar, ya yi wa BBC ƙarin bayani dangane da lamarin.

Ya ce, "A wannan ɗan lokacin da muke ciki a hare-haren da ake kai wa ƴan sanda ba a wajen aikinsu kaɗai ba har gidajensu ake binsu ana kai musu wannan irin hari wanda yakan kasance mai tsanani wanda ake ƙoƙarin kashe su ko kuma a illata su a harin."

"A kwanakin baya ma a nan Abuja an aje gidan wani supeto na ƴan sanda aka kai masa wannan hari inda aka sassara shi da adda aka ji masa munanan raunuka, wanda yanzu yana can asibiti yana karɓar magani, da kuma ire-iren waɗannan," in ji shi.

Ya ƙara da cewa, " a kwanakin baya ma can an kai wa wani DPO hari wanda suna wajen aiki aka same shi, shi ma aka halaka shi."

Sakamakon irin waɗannan hare-haren ne jami'in ya ce Babban Sufeton ya bayar da umarni ga dukkanin kwamishinonin ƴan sanda da kuma masu ruwa da tsaki a gidajen ƴan sanda waɗanda suke da haƙƙin kula da kuma tura ƴan sanda aiki da su tashi tsaye su tabbatar an yi bincike kan irin waɗannan ƙorafe-ƙorafe.

Rundunar ta ce duk wani korafi da yake ƙasa da ba a yi bincike ba gaggauta gudanar da bincike a kai domin waɗanda suka yi laifi a hukunta su daidai da abin da doka ta tanada domin kare jami'an.

Babban Sufeton na ƴan sanda na ganin masu kai wa jami'an nasu hari suna yin haka ne da zummar karya wa jami'an gwiwa abin da ya ce ko lama ba za su bari hakan ya kasance ba.

Rundunar ƴan sandan ta Najeriya ta karfafa ɓangaren gudanar da bincike na sirri da ake kira FIB, domin rage ta'asar da ake aikatawa, inda yanzu aka sanya wannan sashe ƙarƙashin kulawar muƙaddashin sufeto janar na ƴan sanda saɓanin da da yake ƙarƙashin mataimakin sufeto janar.

Dangane da ƙorafe-ƙorafen da ake yi na zargin cin zarafi da ƴan sanda ke yi wa jama'a kuma Babban Sufeton ƴan sandan ya umarci dukkanin kwamishinonin rundunar a jihohi su buɗe wani sashe da ake tanadar domin gabatar da irin wannan ƙorafi.

A bisa tanadin da hukumara ta yi na samar da da wannan sashe da ake kira CRU (Complaint Response Unit), duk mutumin da yake da ƙorafi a kan ƴan sanda zai iya gabatar da korafinsa ta hanyoyin sadarwa na zamani ba sai yaje ofishinsu ba, domin a bi masa haƙƙinsa.