You are here: HomeAfricaBBC2023 02 17Article 1716416

BBC Hausa of Friday, 17 February 2023

Source: BBC

Ƴan sandan Kenya na tuhumar ɗan majalisa da ɗaukar nauyin ƴan bindiga

Yan majalisa a Kenya Yan majalisa a Kenya

‘Yan sanda a Kenya na tuhumar wani ɗan majalisa da ɗaukar nauyin ‘yan bindiga a yankin Rift Valley da ke arewacin ƙasar.

Jami’an sashin binciken manyan laifuka ne suka kama ɗan majalisar mai suna David Pkosing na mazaɓar Kudancin Pokot a ranar Alhamis da yamma, inda suka sake shi daga bisani bayan amsa tambayoyi.

Lauyansa ya ce ɗan majalisar zai bayyana a gaban masu bincike a ranar Juma’a domin amsa wasu tambayoyi da za a ƙara yi masa.

Mista Pkosing shi ne ɗan siyasa na farko da hukumomi suka gudanar da bincike a kansa kan alaƙa da ayyukan ‘yan bindiga da ya janyo rasuwar fararen hula 100 da kuma jami’an tsaro 16 a cikin watanni shida da suka wuce.

Sojojin Kenya da ‘yan sanda za su gudanar da wani samame a ranar Juma’a kan ‘yan bindiga da masu satar shanu a yankin arewacin ƙasar da ke fama da rikice-rikice.

Jami’ai sun ce samamen mai suna “Operation maliza uhalifu” zai yi aiki wajen ganin ya kakkaɓe masu rike da maƙamai ba bisa ka’ida ba a yankin.

An kawo karshen wani atisaye a ranar Alhamis bayan wa’adin kwanaki uku da shugaba William Ruto ya bayar na ganin haka.

Yunkuri da wasu gwamnatocin baya suka yi na kakkaɓe ‘yan bindigar da ke cin karensu babu babbaka ya ci tura.

Gwamnati ta ayyana dokar ta-ɓaci kan lamarin a arewacin ƙasar, inda ta kuma sanya dokar takaita zirga-zirga na tsawon kwanaki 30.

Yayin da ake kai waɗannan hare-hare, a ɗaya bangaren kuma, ana satar dubban shanu a kowane wata da kuma yanka wasu domin sayar wa a ƙanana da kuma manyan kasuwanni.

Rikicin kabilanci da ‘yan siyasa suka haddasa da kuma ƙoƙarin mallakar albarkatun ƙasa na cikin abubuwan da ke ci gaba da janyo ƙaruwar ayyukan ‘yan bindiga.

Masana sun ce ya kamata gwamnati ta samo hanyoyin magance matsalar kamar zaman tattaunawa da farfado da yanayin tattalin arziki na al’ummomi waɗanda aka mayar saniyar ware tsawon lokaci.