You are here: HomeAfricaBBC2023 08 21Article 1829075

BBC Hausa of Monday, 21 August 2023

Source: BBC

Ɗan jaridan Ghana ya lashe kyautar BBC ta Komla Dumor ta 2023

Marigayi Komla Dumor tare da Paa Kwesi Asare Marigayi Komla Dumor tare da Paa Kwesi Asare

Ɗan jarida, kuma mai gabatar da shirye-shiryen talbijin na Ghana, Paa Kwesi Asare, ya lashe kyautar Komla Dumor ta BBC a bana.

Matashin ɗan shekara 36, shi ne na takwas da ya samu wannan lambar yabo, amma na farko daga Ghana, kamar dai marigayi Komla Dumor.

A yanzu haka, Asare shi ne shugaban sashen kasuwanci na tashar talbijin ta TV3 mai zaman kanta a Ghana, inda yake aiki tsawon shekara bakwai a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu gabatar da labarai.

An ɓullo da shirin ba da lambar yabon ne, don karrama Komla Dumor, mai gabatar da labarai a tashar talbijin ta BBC World, wanda ya yi mutuwar fuju'a a 2014, yana da shekara 41.

Ya yi aiki ba-ji-ba-gani don bayar da labaran Afirka cikin salon da ya fita daban ga al'ummar duniya, inda ya riƙa haska wata fuskar Afirka mai cike da ƙwarin gwiwa da fahimtar rayuwa da kuma ƙoƙarin neman na-kai.

Komla Dumor: Fuskar Afirka

Ƙarfin sanin aikin jaridan Asare da gwanintarsa ta yin bayani kan fannoni masu sarƙaƙiya cikin matuƙar gamsarwa da iya fayyacewa, sun burge alƙalan gasar.

"Wannan a gare ni, wani muhimmin canjin rayuwa ne a fagen aikina kuma wata dama ce da zan runguma hannu bi-biyu," cewar Asare, wanda zai shafe wata uku yana aiki da rukunin 'yan jaridan BBC da ke ɓangaren talbijin da rediyo da kuma intanet a birnin London.

Mai gabatar da shirye-shiryen talbijin ɗin na Ghana, zai kuma samu horo, kuma zai yi aiki tare da ƙwararrun 'yan jaridan BBC.

A wani ɓangare na ƙwarewar da zai samu, Asare zai yi tafiya zuwa wata ƙasa a Afirka inda zai ɗauko rahoton da za a gabatar wa masu bibiyar BBC a faɗin duniya.

"Na ji matuƙar farin ciki da na lashe Gasar Komla Dumor ta BBC," Asare ya ce.

"Wannan mai yiwuwa ita ce lambar yabo mafi ƙima ga duk wani ɗan jarida na Afirka. Ina tsananin begen baiwar da Allah ya bai wa Komla, kuma kasancewata ɗan jaridar da aka zaɓa ya taka sawunsa, ba kawai abin murna ba ne, wata babbar alfarma ce a gare ni."

'Yan jaridan da suka ci kyautar a baya, su ne Dingindaba Jonah Buyoya da Victoria Rubadiri da Solomon Serwanjja da Waihiga Mwaura da Amina Yuguda da Didi Akinyelure sai Nancy Kacungira, wadda ta fara lashe gasar.

Bara ne, Jonah Buyoya ya je ƙasar Seychelles don ɗauko rahoto a kan yadda tsirran cikin teku, za su iya taimakawa wajen shawo kan sauyin yanayi.