You are here: HomeAfricaBBC2023 03 28Article 1739531

BBC Hausa of Tuesday, 28 March 2023

Source: BBC

Ɗan bindiga ya harbe ɗalibai da malamai a wata makaranta a Amurka

Wani shugaban yan sanda a Nashville Wani shugaban yan sanda a Nashville

Wani mahari ya buɗe wa mutum shida wuta - waɗanda suka haɗa da yara uku da malamai uku a birnin Nashville na ƙasar Amurka.

Uku daga cikin yaran da lamarin ya rutsa da su ba su haura shekara tara ba da ke karatu a wata makaranta ta ƴan addinin kirista.

Ƴan sanda sun bayyana sunayen yaran da Evelyn Dieckhaus da Hallie Scruggs da William Kinney.

Sauran malaman da suka mutu sun haɗa da Cynthia Peak, mai shekara 61 da Katherine Koonce, mai shekara 60, da kuma Mike Hill, mai shekara 61.

Makarantar ta mabiya addinin kirista na da ɗalibai sama da 200. Tana koyar da ɗalibai ƴan shekara uku zuwa 12.

Ms Peak ta kasace tana aiki a makarantar a ranar da lamarin ya faru.

Ƴan sanda sun ce wanda ake zargi da kai harin Audrey Hale, mai shekara 28, mutum ne da ya sauya jinsinsa.

Ƴan sanda sun harbe shi daga bisani, inda suka samu bindigogi uku da kuma harsasai a jikinsa.

Sun ce sun samu labari kan lamarin ne da misalin karfe 3:00 agogon GMT a ranar Litinin.

Wanda ake zargin ya je makarantar ne cikin wata mota, inda ya fasa wata kofar shiga makarantar kafin ya samu damar kutsawa, bayan da ya samu duka kofofin a rufe.

Hotunan bidiyo da ƴan sandan Nashville suka fitar daga baya, sun nuna Hale na amfani da bindiga wajen fasa gilasai da kofofi, kafin ya afka ciki.

Bidiyon ya kuma nuna shi sanye da wata karamar rigar kariya, kuma riƙe da bindigoginsa a hannu.

Hale ya fara harbi a gini na farko kafin ya haura zuwa ta biyu.

Lokacin da ƴan sanda suka isa wajen, ɗan bindigar ya yi ta harbi a kansu, inda harsashi ya faɗa kan gilasai, a cewar ƴan sanda.

Fashewar gilashin ya raunata wani jami'in ɗan sanda, inda ba tare da wata-wata ba, ƴan sanda suka shiga cikin ginin tare da harbe wanda ake zargin da misalin karfe 10:27.

Binciken da ƴan sandan suka gudanar, ya gano cewa Hale tsohon ɗalibin makarantar ne.

Mai magana da yawun ƴan sandan ya yi magana da mahaifin maharin lokacin da ake gudanar da bincike a kusa da wani gida da aka bayyana cewa gidansu ne.

Shugaban ƴan sandan birnin Nashville John Drake ya ce masu bincike sun gano wata taswira da ta nuna yadda Hale ya tsara kai harin, ciki har da yadda zai shiga da kuma fita daga makarantar.

Ya kuma ce ɗan bindigar ya gudanar da bincie kafin ya kai harin.

Bayan harin, iyaye sun taru a kusa da wani coci domin sake ganin 'ƴa'yansu.

Lokacin da motocin bas ɗauke da ɗalibai suka isa, sun yi ta daga hannayensu zuwa iyayensu ta tagogin mota a cewar jaridar Tennessean.

Makarantar na a kan wani karamin tsauni da ke kudancin birnin Nashville.

Mahaifiyar ɗaya daga cikin ɗaliban ta ce ɗanta ya shiga garari bayan harin da aka kai makarantar tasu.

"Ina ganin hankalinsa ya fara kwanciya a yanzu da ya gano cewa maharin ya mutu," in ji Shaundelle Brooks yayin tattaunawa da BBC.

"Bai kamata mu riƙa yin irin waɗannan zantuka ba,". "Mun gaza a wajen 'ƴa'ƴan mu."

A daren ranar Litinin, mashigar makarantar ya kasance kamar na sauran coci-coci da ke da makaranta a cikinsu.

Akwai wata alama a waje da ke bayyana cewa ana rajistar fara karatu na bazara.

"Lokacin da na ji abin da ya faru, na kasa yin komai. Na cika da takaici," in ji Mark daga kudancin Nashville.

"Kawo furanni shi ne hanyar da na ɗauka na yin bankawana da kuma girmama rayukan da aka rasa."

A cikin wata sanarwa, magajin birnin Nashville John Cooper ya ce birnin ya shiga cikin jerin al'ummomi da suka fuskanci hare-hare musamman kan makarantu.

Shugaba Joe Biden ya kira harin a matsayin "mummunan mafarki".

"Ya kamata mu yi iyaƙar kokari wajen dakatar da hare-hare da ake kai wa da bindiga," in ji Biden, inda ya yi kira ga majalisar dokoki da ta bijiro da kudurori kan amfani da bindiga.

Ya ce buɗe wuta da ƴan bindiga suke yi na salwantar da rayukan Amurkawa kuma ya zama dole a dakatar da hakan.

A cewar alkaluma da aka tattara a makon-nan, sun nuna cewa akwai hare-hare 12 da aka kai kan makarantu waɗanda suka yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkata mutane a Amurka a wannan shekara.