You are here: HomeAfricaBBC2021 04 27Article 1243651

BBC Hausa of Tuesday, 27 April 2021

Source: BBC

Ƴan bindiga: An sake kashe dalibai biyu na jami'ar Greenfield da aka sace a Kaduna

An sake gano wasu daliban jami'a biyu da suka mutu, inji Gwamnatin jihar Kaduna An sake gano wasu daliban jami'a biyu da suka mutu, inji Gwamnatin jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar cewa an sake gano wasu daliban jami'a biyu da suka mutu a arewacin Najeriya.

Tun da farko masu garkuwa da mutane sun kashe wasu dalibai uku a ranar Juma'a.

An sace dalibai 20 a ranar Talatar da ta gabata tare da wasu ma'aikata uku na Jami'ar Greenfield na yankin Chikun da ke jihar Kaduna.

Gwamnatin Kaduna ta ce ta yi bakin ciki da abin da ta kira 'ta'asar da aka aikata a kan daliban da ba su ji ba ba su gani ba' da aka sace yayin da suke neman iliminsu don samun daukaka nan gaba.

Ba kamar wasu jihohin da ke makwabtaka da ita ba gwamnatin jihar Kaduna na da manufar kin tattaunawa da masu satar mutane ko biyan kudin fansa.

Gwamna Nasir el-Rufai a maimakon haka burinsa shi ne a cafke tare da gurfanar da masu satar mutane.

Yawan sace-sacen dalibai da ake yi domin biyan kudin fansa na karuwa a Najeriya yayin da hukumomi ke kokarin shawo kan rashin ingantattun kayayyakin tsaro.

Mafi yawan jihohin arewa maso yamma sun rufe makarantu don bai wa hukumomi lokaci su samar da mafita kan rikicin.