You are here: HomeAfricaBBC2023 07 17Article 1806341

BBC Hausa of Monday, 17 July 2023

Source: BBC

Ƴan Hisban Iran za su ci gaba da kama matan da ba su rufe kansu

Hoton alama Hoton alama

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ruwaito cewa ƴan hisban ƙasar sun ci gaba da sintirin mai cike da ce-ce-ku-ce domin tabbatar da matan ƙasar suna rufe gashinsu a cikin jama'a.

A jiya Lahadi ne Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ya ce "za su ci gaba da zagayawa lungu da saƙo domin tabbatar da dokar saka hijabi a Iran ta ci gaba da aiki.

Hakan na zuwa ne watanni goma bayan da wata matashiya, Mahsa Amini ta rasu a wajen da ake tsare mutane bayan an zarge ta da laifin karya dokar saka tufafi a Tehran.

Mutuwar matashiyar ta janyo gagarumar zanga-zanga a fadin ƙasar, lamarin da ya haddasa dakatar da kamen da ƴan hisban ke yi, sai dai masu tsattsauran ra'ayin Islama sun ci gaba da kiraye-kirayen dawo da sintirin.

A ƙarƙashin dokokin Iran wadanda aka tsamo daga cikin dokokin shari'ar Muslunci, dole ne mata su rufe gashin kansu da hijabi, tare da saka kayan da ba za su nuna ƙirar jikin su ba.

Ƴan hisba su ne ke da alhakin tabbatar da an kiyaye irin waɗannan dokoki tare da kuma tsare waɗanda suka karya dokar.

Mai magana da yawun ƴan hisbar Saeed Montazerolmahdi ya ce "yayin da ake irin wannan sintirin, jami'an za su fara da yin gargaɗi ga matan da suka karya dokar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tasnin ya ruwaito.

Ya ce "idan suka ƙi bin doka sai a dauki matakin shari'a a kan su."

Mahsa Amini yar shekaru 22 ta kai ziyara ne a Tehran tare da iyalanta a watan Satumban shekarar da ta gabata, a lokacin ne ƴan hisbar suka kama ta da laifin saka hijabin ta ba bisa ƙa'ida ba.

Bayan an kai ta a wajen da ake tsare masu irin wannan laifin, ta faɗi yayin da rahotanni ke cewa jami'an sun buga mata sanda a kai tare da buga kanta a jikin motar su.

Lamarin da ya haddasa gagarumar zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a fadin ƙasar, mutane kusan ɗari shida ne aka kashe, an kuma zartar da hukuncin kisa ga mutane da dama.

Bayan wasu ƴan watanni da zanga-zangar, mata da dama sun daina sanya hijabi.

Wannan shi ne bore mafi girma da kai-tsaye aka ƙalubalanci matakin malaman addini na Iran tun bayan juyin-juya hali na 1979.

Bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya nuna yadda mata a ƙasar suka mayar da rashin sanya hijabi ba komai ba a wajen su.

Sai dai hukumomi sun sake tsaurara hukunci da ya haɗa da tilasta rufe wuraren kasuwanci idan ba a kiyaye dokar saka hijabi ba.

Duk da dai mutane da dama sun goyi bayan zanga-zangar, amman duk da haka an samu wasu da suke goyon bayan tsananta dokar saka tufafi a ƙasar.

Tun a farkon wannan shekarar ne, wani faifan bidiyo ya nuna wani mutum yana jifan wasu mata da ba su saka hijabi ba da robobin yegot.

Maza da mata a ƙasar sun yi Allah wadai da matakin mutumin, yayin da daga bisani aka kama shi tare da matan.

Wani ɗalibin jami'a a ƙasar Ismail said ya ce "yana tuanin abu ne mai matukar wahala hukumomi su iya sake ƙaƙaba dokar sanya tufafi."

Ya ce " ba za su iya tabbatar da dokar kamar yadda suka yi a baya ba, saboda mutanen da suke karya dokar kullum kara yawa suke, ba za su iya da mu duka ba, sai dai daga karshe su yi amfani da karfin da ya wuce kima kan mu, wanda kuma ba zai yi aiki a yanzu ba.

Iran na da kashe-kashen ƙungiyoyin ƴan hisba tun bayan juyin-juya-hali.

Waɗannan ƴan hisban su ne na baya-bayan nan da aka kafa a 2006.

Ba'a san adadin maza da mata da ke aiki da ƴan hisban ba, sai dai suna da damar amfani da makamai, da kuma wajen da ake tsare mutane da kuma wasu wurare da suka kira da cibiyoyin sauya tunani.

A shekarar da ta gabata, a yunƙurinsu na mayar da martani kan kama-karyar da Iran ta yi kan masu zanga-zanga, Birtaniya da sauran ƙasashen Yamma sun ƙaƙaba takunkumi ga ƴan hisbar da kuma wasu mayan jami'an tsaron kasar.