You are here: HomeAfricaBBC2023 12 07Article 1894559

BBC Hausa of Thursday, 7 December 2023

Source: BBC

Ziyarar Putin da ba a saba ganin irinta ba a kasashen Larabawa

Vladimir Putin, shugaban Rasha Vladimir Putin, shugaban Rasha

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya kai wata ziyara da ba saba ganin irinta ba a kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Tattaunawar da ake sa rai za su yi ta shafi batutuwan da suka kunshi yakin Gaza da na Ukraine da kuma harkokin samar da man fetur da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa.

Hadaddiyar Daular Larabawa a yanzu haka tana karbar bakuncin taron kolin Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP28.

Mista Putin, wanda da kyar idan ya bar Rasha tun cikin watan Maris lokacin da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta fitar da sammacin kama shi, zai kuma gana da shugaban Iran nan gaba a birnin Moscow.

Kotun ta zarge shi da iza keyar kananan yara 'yan Ukraine zuwa Rasha ba bisa ka'ida ba - wanda laifin yaki ne - sai dai daga Hadaddiyar Daular Larabawa har Saudiyya babu, kasar da ta yarda da hurumin kotun.

Shugaban na Rasha ya kaurace wa halartar sauran tarukan kasashen duniya a baya-bayan nan cikinsu har da na kungiyar BRICS - kasashe masu yunkurowa a watan Agusta cikin Afirka ta Kudu da kuma taron kungiyar kasashen G20 a watan Satumba da aka yi cikin kasar Indiya.

Ziyarce-ziyarcen na zuwa ne yayin da Rasha ke alla-alla ta fito da tasirinta da kuma takalar kokarin Kasashen Yamma na mayar da kasarsa saniyar ware.

Mista Putin ya samu tarba a Hadaddiyar Daular Larabawa da rakiyar cikakken hawan keken doki da kuma kwambar motoci yayin da sojojin saman kasar suka yi wasa da jiragen sama tare da fitar da launin tutar Rasha da hayakin jirage.

Daga bisani, shugaban na Rasha ya kai ziyara kasar Saudiyya don ganawa da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman.

Yayin wani takaitaccen jawabi ta kafar talbijin, Mista Putin ya gayyaci yarima mai jiran gadon don ya kai ziyara birnin Moscow.

Yarima mai jiran gado ya ce hadin gwiwar kasashen biyu ya "taimaka wajen kawar da zaman tunzuri mai yawa a Gabas ta Tsakiya".

An kuma hangi shugaban Jamhuriyar Chechen da ke Rasha wanda ke yawan janyo takaddama, Ramzan Kadyrov, yana halartar taro tsakanin Shugaba Putin da kuma jagoran na Masarautar Saudiyyan.

Gabanin taron, an ba da rahoton cewa shugabannin biyu za su yi "nazari kan hanyoyin da za su rage zafafar" yaki tsakanin Isra'ila da Hamas da kuma rikice-rikice a Siriya da Yemen da Sudan, wadanda za a tattauna su a Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.