You are here: HomeAfricaBBC2023 08 17Article 1826903

BBC Hausa of Thursday, 17 August 2023

Source: BBC

Zargin cin hanci ya yi wa kotun zaɓen Kano dabaibayi

Hoton alama Hoton alama

Dambarwa ta ɓarke, bayan Mai shari'a Flora Ngozi Azinge, shugabar kotun sauraron ƙorafin zaɓen 'yan majalisun tarayya da na jihar Kano, ta sake fitowa ta koka game da yunƙurin bai wa alƙalan kotun cin hanci da nufin tauye adalci.

Manyan jam'iyyun siyasar jihar guda biyu NNPP mai mulki da APC, babbar mai hamayya a Kano suna nuna wa juna yatsa.

Rahotanni dai sun ambato Mai shari'a Flora Azinge na cewa karo na biyu kenan wani alƙalin kotun na kai mata ƙorafi a kan yadda wasu lauyoyi da ke cikin ƙararrakin da kotun ke sauraro, suna ƙoƙarin ba su cin hanci.

Zargin na babbar alƙaliyar, na nuna tsananin rufewar idon 'yan siyasa, ta yadda wasu ke ƙoƙarin sayen nasarar da suka kasa samu ta halastacciyar hanya daga jama'ar da za su mulka.

Ba a saba jin wani alƙali ko wata alƙaliya sun fito bainar jama'a suna kokawa a kan ƙoƙarin ba su toshiyar baki ko cin hanci a Najeriya ba.

Sai dai kamar yadda aka saba, a wannan karo ma, duk manyan masu ruwa da tsaki sun fito bainar jama'a suna tsame kansu daga zargin da mai shari'ar ta yi.

Gwamnatin jihar ta Kano ce dai ta fara fitowa tana nesanta kanta, sai dai ba ta tsaya a nan ba, ta riƙa yin ishara da sashen takwararta mai adawa wato APC.

Amma su ma 'yan adawar na Kano, APC sun sa ƙafa sun yi watsi da wannan al'amari, sun ma ƙara da zargin gwamnatin NNPP da yunƙurin ɓata sunan jam'iyyar tasu da ma na mai shari'ar.

Zarge-zargen ba da cin hanci ga alƙalan dai ga alama ya damu, ƙungiyar lauyoyi ta Kano, wadda shugabanta na jihar, Barista Sagir Sulaiman Gezawa ya rubuta wata wasiƙa ga kotun, yana neman ta bayyana sunayen lauyoyin da suka yi yunƙurin bai wa alƙalai toshiyar baki.

Ya dai ce za su gudanar da bincike don sanin irin matakin ladabtarwa da za su iya ɗauka a kan masu yunƙurin ba da cin hanci da kuma ganin yadda za su kai lauyoyin da ake zargi gaba.

Ya kuma ce tuni sun aika kwafin wasiƙa ga majalisar alƙalai ta ƙasa da shugabar kotun ɗaukaka ƙara da kuma shugaban ƙungiyar lauyoyi na Najeriya a kan batun.

A cewarsa, ƙungiyar da yake jagoranta ta kuma nemi ganawa da alƙalan kotun zaɓen ta Kano, sannan ya nanata alƙawarin ƙungiyarsa ga yaƙi da cin hanci da rashawa.

Gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike - NNPP

Mai shari'a Flora Azinge dai ta koka da cewa "kuɗi yana ta giggilmawa".

Ta ce "a shekarun baya-bayan nan, zarge-zargen lauyoyi suna bai wa alƙalai cin hanci sun dusashe ƙimar ɓangaren shari'ar najeriya, wani batu da ya zama mai sarƙaƙiya wanda har yake barazanar zaizaye yardar da jama'a suka bai wa kotu wajen bin duk wani kadi nasu.

A sanarwar da ta fitar ta hannun kwamishinanta na labarai, Baba Halilu Ɗantiye, gwamnatin Kano ta ce ta damu matuƙa game da wannan batu.

A cewarta, akwai raɗe-raɗi mai ƙarfi na cewa wasu jiga-jigai a jam’iyyar APC, da hankalinsu ke kan zaɓen Kano, inda suke son maimaita abin da ta ce sun yi a 2019.

Ta yi zargin cewa 'yan adawar sun duƙufa wajen yin duk abin da za su iya don ganin an yi rashin adalci a shari'ar, kamar yadda ta ce an yi a baya.

Gwamnatin ta ce ba ɓoyayyen abu ba ne cewa, waɗannan jiga-jigai da ta ce an san su sosai saboda ɗabi’arsu ta rashawa, suna aiki ba ji ba gani don ƙwace ikon da ta samu cikin gwagwarmayarf siyasa, daga al’ummar Kano don mulkarsu.

Ta dai ce ta ɗauki batun a matsayin zakaran-gwajin-dafi ga gwamnatin Najeriya don ta fito ta nuna wa ‘yan ƙasar gaskiyar niyyarta ta yaƙi da rashawa da kare muradan dimokraɗiyya.

Gwamnatin ta kuma nemi a gudanar da bincike kan lamarin tare da gurfanar da waɗanda duk aka samu da laifi a gaban shari’a.

Ta ƙara da cewa, tana sa ran ganin ƙungiyoyin yaƙi da cin hanci da rashawa su zabura don gudanar da aiki game da wannan zargi, musamman ma ganin cewa ya fito ne daga mai shari’a da ke da babban matsayi da ƙima.

Sanarwar ta ce duk da haka ma, gwamnatin jihar Kanon tana ganin abin da Mai shari’a Azinge ta yi na fitowa ta bayyana wannan zargi, alama ce da ke nuna cewa har yanzu kotunan Najeriya, ababen dogaro ne, kuma akwai alkalai masu gaskiya da amana.

Tsarguwa NNPP ta yi - APC

Jam’iyyar APC reshen Kano ta yi gargaɗin cewa bai kamata gwamnatin jihar ta ɓata sunan kotun zaɓen ba.

A sanarwar da shugaban ma'aikata na shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Malam Muhammad Garba ya fitar, jam'iyyar adawar Kano ta ce gwamnatin NNPP ta yi zargin ne saboda abin da ta kira rashin taɓuka abin-a-zo-a-gani wajen gabatar da hujjojin da za su kare zargin murɗiyar zaɓe da suke yi mata a gaban kotu.

Jam’iyyar ta ce, gwamnatin tana yunƙurin ɓata sunan shugabar kotun ne ta hanyar ƙirƙirar labarin ƙarya, da jirkita maganar mai shari’ar, saboda fargabar cewa hukuncin shari’ar, ba zai yi musu daɗi ba.

Tsohon kwamishinan na Kano ya ce, a zargin da Mai shari’a Flora ta yi, ba ta ambaci sunan jam’iyya ko babban lauyan da ta ce ya yi ƙoƙarin bayar da cin hanci da ɓangaren da yake tsayawa a gaban kotu ba.

Amma duk da haka, in ji shi don gwamnatin NNPP ta ɓata sunan APC shi ne ta nuna cewa 'yan adawan ne suka bayar da cin hanci.

Mallam Garba ya ce, abin da gwamnatin Kano ta yi na nuna cewa tana son ɓata sunan kotun ne, domin ta yaudari jama’a su tausaya mata, idan ta yi rashin nasara a shari'ar da ke gaban kotu.

Ya ce duk da alamun nasarar da suke gani a shari’ar, APC ba za ta taɓa bayar da cin hanci ga duk wani da ke da hannu a shari’ar ba, saboda ta san ta gabatar da ƙwararan shaidu da bayanai a lokacin sauraron ƙararsu.

Bugu da ƙari, a cewar Mohammed Garba gwamnatin NNPP ta kasa gabatar da wata ƙwaƙƙwarar shaida da za ta kare zarge-zargen da aka yi mata.

Zuwa yanzu dai ba a ji wani martani daga wata hukuma mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta tarayya ba, sannan ba a ji wani bayani daga ɓangaren shari'a na Najeriya ba.

Zarge-zargen bayar da cin hanci a kotu, duk da yake ba sabon abu ba ne a Najeriya, amma abu ne da zai tayar da hankalin dubban ɗaruruwan Kanawa, masu ƙwarin gwiwar cewa kotu za ta jingina matsayinta a kan gaskiya kuma ta tabbatarwa da mai gaskiya, gaskiyarsa, a dukkan hukunce-hukuncen da za ta yanke game da zaɓukan da aka yi a jihar tun farkon wannan shekara.