You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811951

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Zaman kashe wando tsakanin matasan China ya kai matuƙa

Hoton alama Hoton alama

Rashin aiki ya ƙaru ga matasa a China inda ya yi munin da ba a taɓa gani ba tun bayan da ƙasar ta fara farfaɗowa daga koma bayan da cutar korona ta haifar.

Rashin aikin ya fi yawa ne a tsakanin matasa ƴan shekaru 16 zuwa 24 da ke rayuwa a manyan biranen ƙasar inda adadinsu ya kai kashi 21.3 a watan da ya gabata, kamar yadda bayanai a hukumance suka nuna.

Hakan na zuwa ne yayin da ƙasar da take ta biyu a ƙarfin tattalin arziki a duniya, ƙarfin tattalin arzikinta ya ƙaru da kashi 0.8 a cikin watanni uku zuwa karshen watan Yuni.

Masu sharhi na cewa ana sa ran hukumomin ƙasar su fitar da sababbin matakan haɓɓaka tattalin arzikin ƙasar.

Hukumar ƙididdiga ta China ta ce "waɗannan bayanan sun nuna yadda tattalin arziƙin ƙasar ke farfaɗowa."

Kamar yadda bayanai a hukumance na ranar litinin suka nuna, tattalin arziƙin China ya ƙaru da kashi 6.3 a rubu'i na biyu na wannan shekarar. Sai dai duk da haka ƙasar ta gaza cimma matakin da masu hasashe suka yi na ci gaban da za ta samu.

"Za'a iya ganin hakan ƙarara a ɓangaren saye da sayarwa da kuma zuba jari a a ɓangaren gidaje" inji Qian Wang wata masaniya kan tattalin arziƙi.

"Hakan kuma yana da nasaba da hauhawar farashi da kuma rahotannin basussukan da suka ƙara jaddada hasashenmu na koma-baya da ake samu a ƙasar" inji ta.

Buƙatar da ake da ita ta kayan da China ke samarwa ta ragu.

Masana tattalin arziƙi na sanya ido sosai kan rashin aikin yi ga matasa, inda matasan da suka gama jami'a miliyan 11.58 ake sa ran za su shiga sahun masu neman aiki a wannan shekarar.

Rashin aikin yi na ƙara yawa ne a cikin birane a watannin baya bayan nan.

Sai dai hakan ba ya rasa nasaba da banbancin da ake samu wajen kwarewar da matasan suka yi yayin da suke karatu da kuma guraben ayyukan da ake da su a ƙasa.

Hukumomi sun ce akwai yiwuwar ci gaba da samun ƙaruwar rashin aiki yi a tsakanin matasa har zuwa watan Agusta.

Wata mai sharhi kan tattalin arziƙi, Dan Wang ta yi ƙiyasin cewa adadin matasan da ke zaman kashe wando a biranen China ya kai kashi 1.4.

Ta kuma shaida wa BBC cewa "rashin aikin yi na buƙatar gwamnati ta fitar da tsare-tsare kai tsaye saboda mutanen da abun ya shafa na yawan ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.

China ta fara wallafa adadin marasa aikin yi a shekarar 2018. Sai dai kuma ba ta fitar da bayanan adadin matasan da ke fuskantar matsalar a yankin karkara ba.

A watan Maris, Firaiministan China, Li Qiang ya ce "akwai buƙatar ƙasar ta ƙara ƙoƙari wajen ganin ta cimma ƙudurinta na haɓɓaka tattalin arziƙinta da kashi 5 a wannan shekarar.

Ya ce "Hakan ba abu ne mai sauƙi ba, saboda yadda tattalin arziƙin ke kwan-gaba kwan-baya".

A watan da ya gabata, babban bankin China ya rage yawan haraji a karon farko a wannan shekarar domin bayar da kwarin guiwa ga mutane wajen saye da sayarwa.

Sai dai Masana na ganin cewa akwai hanyoyi da dama da suka kamata gwamnati ta bi idan har ba'a samu ci gaba a ɓangaren ba.