You are here: HomeAfricaBBC2023 08 17Article 1826948

BBC Hausa of Thursday, 17 August 2023

Source: BBC

Zaben Ecuador: 'Ina sanya riga mai kare mutum daga harsashi a koda yaushe

Andrea González tana sanya riga mai kare mutum daga harsashi a koda yaushe Andrea González tana sanya riga mai kare mutum daga harsashi a koda yaushe

Yanzu Andrea González tana sanya riga mai kare mutum daga harsashi a koda yaushe.

Mako guda da ya wuce, an harbi ɗan takarar shugaban ƙasa Equador na jam'iyyar Construye, Fernando Villavicencio har sau uku a kai, bayan wani gangamin neman zaɓe a Quito babban birnin ƙasar.

Ms González, ƴar shekara 36, ta ci gaba da zaman ƴar takarar mataikiyar shugaban ƙasa, yayin da ta ke mra baya ga sabon ɗan takarar, Christian Zurita. Shi ma ɗan jarida ne wanda ya gudanar da bincike kan rashawa, kamar Fernando Villavicencio.

"Ba zan bari manufofin Fernando su rushe ba," inji Ms González a cikin shirin 'Newshour' na BBC.

Ta ce "Wannan abu ne da ya shafe ni kai tsaye kuma bankwana da abokina abu ne mai matuƙar wahala. Ina sanya riga mai bayar da kariya daga harsashin bindiga ba dare ba rana.

Mr Villavicencio, mai shekara 59, ɗan jarida ne kuma ɗan majalisar dokokin Ecuador wanda aka harbe a wajen gangamin neman zaɓe, a babban birnin ƙasar ranar laraban da ta gabata, kwana 11 kafin zaben shugaban ƙasa.

An kashe ɗaya daga cikin maharan a yayin musayar wuta da ƴan sanda, kuma wasu da dama sun gudu.

Mutruwar sa ta girgiza ƙasar wadda ta yi fama da rikicin gaggan masu safarar miyagun ƙwayoyi da kuma manyan ayyukan rashawa na gomman shekaru. An kuma samu ƙaruwar aikata laifuka a ƙasar cikin ƴan shekarun nan, lamarin da ake alaƙantawa da ƙaruwar safarar miyagun ƙwayoyi a Colombia da Mexico.

Gangamin neman zaɓen Mr Villavicencio ya mayar da hankali ga yaƙi da rashawa da kawar da masu safarar ƙwayoyi kuma yana daga cikin ƴan takara ƙalilan da suke zargin cewa wasu jami'an gwamnati suna da hannu a manyan laifukan da ake aikatawa a Ecuador.

"Mun kama hanyar zama ƙasar da tattalin arzikinta ya dogara kacokan ga safarar ƙwaya" in ji Ms González.

Ta ƙara da cewa "Mun gamsu cewa wanni kisa ce ta neman kawar da abokan hamayyar siyasa don kuwa ta fi ƙarfin irin laifukan da aka saba da su.

"Kwana uku kafin fara muhawara Fernando ya faɗi ƙarara cewa yana da muhimman bayanai da zasu iya canza akalar zaɓe mai zuwa. Ba mu samu damar jin waɗannan bayanai ba."

Ms González, wadda ta shafe tsawon lokacin aikin kan batun da ya shafi kula da muhalli ta ce irin wannan rikici n neman zama abin da aka saba da shi a siyasar Equador.

Da farko dai jam'iyyarta ta so maye gurbin Mr Villavicencio da ita a matsayin ƴar takarar shugaban ƙasa, daga baya kuma sai aka amince da bai wa Christian Zurita takara, yayin da ita kuma Ms González ta ci gaba da zama ƴar takarar mataimakiyar shugaban ƙasa. Jam'iyyar ta ji tsoron kada a yi amfani da wata kafa ta doka wajen haramta takarar su saboda ta riga ta fara takara da wani a baya.

Da yake an riga an buga takardun kaɗa ƙuri'a, sunan Fernando Villavicencio zai ci gaba da kasancewa a takardun da za a yi zaɓen da su.

Tun bayan harin da aka kaiwa ɗan takarar ake ci gaba da fama da rikici. An harbe Pedro Briones har lahira, ɗaya daga cikin jagororin jam'iyyar masu ra'ayin kawo sauyi a Esmeraldas. Ƴan bindiga suka harbe shi a cikin gidansa rnar Litinin.

"Mu duka muna fguskantar hatsarin wannan hare-hare a halin da ake ciki yanzu," inji Ms González.

"Kai yara makaranta ya riga ya zama abu mai hatsarin gaske. Duk lokacin da ka tsaya a wutar da ke bayar da hannu ga ababen hawa, kana ƙara jefa kanka ne a cikin hatsari. Ana iya dasa bam kusa da motarka.

"Ecuador ba ta taɓa shiga cikin irin wannan tashin hankali ba."

Sai dai ta ce wannan ba zai hana ta ci gaba daga wajen da ubangidanta ya tsaya ba.

Ta ce "Ina jin akwai babban nauyi rataye a wuyana"