You are here: HomeAfricaBBC2023 06 26Article 1793054

BBC Hausa of Monday, 26 June 2023

Source: BBC

Za mu yaƙi katsalanda a harkokin shugabancin majalisa - 'Yan adawa

Sanatoci a Najeriya Sanatoci a Najeriya

Sanatocin jam'iyun adawa sun sha alwashin kin amincewa da duk wani yunkuri na kawo cikas ga shugabancin marasa rinjaye a majalisar dattawa.

Manyan mukamai hudu da aka ware wa jam'iyyun adawa a Majalisar Dattawa su ne shugaban marasa rinjaye da mataimakinsa da mai tsawatarwa da kuma mataimakinsa.

A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da sanatocin suka fitar, sun ce ɓangaren marasa rinjaye na majalisar dattawan za su zaɓi shugabanninsu bayan tuntubar jam'uyyunsu ba tare da katsaladan daga wurin wasu da ke adawa da tsarin mulkin dimokuradiyya ba.

Sun nanata cewa har yanzu babu wani sanata da aka amince da shi ko aka zaɓa a matsayin wanda za a bai wa waɗanan mukamai.

Sanatocin da suka saka a hannu a cikin sanarwar sun haɗa da Mohammed Adamu Aliero da Henry Seriake Dickson da Aminu Waziri Tambuwal da Abdul Ningi da Patrick Abba Moro da Ezenwa Francis Onyewuchi da Kawu Sumaila da kuma Ifeanyi Ubah.

Sanata Kawu Sumaila ya yi ikirarin cewa wasu ne suke son su raba kawunan 'yan majalisar dattawan amma ba za su lamunta da shi ba.

"Wasu mutane daga bayan gida, suna so su raba kawunan ‘yan jam’iyyar adawa, su naɗa shugabanni, shiyasa suke neman haɗin kan sabon shugaban majalisar dattawa."

Sanatocin sun yi gargadin samun babbar ɓaraka muddin aka yi mu su katsalandan a cikin tsarin zabar shugabannin marasa rinaye.

"Kaidar dokoki ya fadi yada za a yi, a fitar da wannan shugabancin, in ma ɗan takara za su tsayar a tsakaninmu, su tsayar da ɗan takarar, in da zaɓe ne ko yarjejeniya ne aka sa nasu da yardamu, to shi kenan mun yada.

"Amma ba a zagaya ta bayan gida, ayi domin biyan wata bukata ba, wanda idan aka yi wannan, dukaninmu mun faɗa mu su cewa zai janyo mumunar ɓaraka a cikin tsarin zaman takewa ta majalisar da tsarin tafiyar da gwamnati, in ji Sanata Kawu.

Sai dai sanatocin ba su ambaci sunnayen wadanda suke zargi da kokarin kawo baraka a cikin majalisar ba.

Rahotani sun ce rikicin na da nasaba da yunkurin da tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi na ganin ya samar wa wasu abokan siyasarsa mukamai a shugabancin da aka ware wa jam'iyyu marasa rinjaye.

Rahotanin sun kuma ce Mista Wike ya gana da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio a ranar Alhamis na tsawon sa'oi kuma ya fita daga cikin majalisar ba tare da ya yi wa 'yan jarida bayani ba.

An ce tsohon gwamnan ya yi nasarar samar wa wani da ya ke da kusanci da shi, Kingsley Chinda mukamin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai.

Sai dai sanatocin 'yan adawa sun sha alwashin nuna tirjiya akan duk wani yunkuri na kawo mu su shugabanci da bai da ce ba a majalisar dattawan kasar.