You are here: HomeAfricaBBC2023 09 14Article 1844360

BBC Hausa of Thursday, 14 September 2023

Source: BBC

'Za mu kawo wa Najeriya gudunmawar dala biliyan 2.5 don yaƙi yunwa'

Hoton alama Hoton alama

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta alƙawarta samar da dala biliyan 2.5 domin taimaka wa Najeriya wajen cimma burinta na yaƙi da yunwa da wadata al'umma da abinci a ƙasar.

Daraktan hukumar a Najeriya, Mista David Stevesson, ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci ayarin jami'ansa don kai ziyara ga ministar jin ƙai da yaƙi da fatara, Dakta Betta Edu a Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Ya ce "mun tattauna game da yaƙi da yunwa a Najeriya, da kuma ayyukan jin ƙai a kowacce ƙaramar hukuma a faɗin ƙasar, sannan mun tattauna kan shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya .

Ya ce za a gudanar da shirin ne ta hanyar tallafa wa ƙananan hukumomi wajen sayen abinci domin rarraba wa mabuƙata, da kuma ba su tallafin kuɗi da na abincin kai tsaye.

"Don haka nake son bayyana cewa Hukumar Samar da Abinci ta Duniya za ta kashe dala biliyan 2.5 domin yaƙi da yunwa a Najeriya cikin shekara biyar masu zuwa', in ji daraktan.

Mista Stevesson, ya kuma ce hukumarsa ta ɗauki sunayen mutum miliyan biyu da dubu ɗari ɗaya waɗanda za su ci gajiyar shirin.

Ya kuma bayyana fatan ci gaba da aiki kafaɗa-da -kafaɗa da ma'aikatar jin-ƙai ta Najeriya domin cimma wannan buri.

Jami'in ya dai bayyana aniyar hukumar wajen tallafa a gwamnatin tarayya don magance matsalolin jin-ƙai tare da yaƙi da yunwa, musamman ta fuskar wadata ƙasar da abinci.

”Muna farin ciki kan matakan da shugaban Najeriya ya ɗauka na kawar da yunwa tare da rage buƙatar ayyukan jin-ƙai a Najeriya", in ji shi.

Ya ci gaba da cewa ”sabbin tsare-tsare da ministar jin-ƙai ta zo da su, za su bai wa hukumarsa damar cimma nasarori masu yawa tare da ma'aikatar".

Tun da farko Ministar jin-ƙai da yaƙi da fatara ta ƙasar, Dakta Betta Edu, ta ce tallafin da hukumar WFP za ta bayar, zai taimaka wajen magance buƙatun jin-ƙai da Najeriya ke fuskanta.

Ta ƙara da cewa "kakkaɓe yunwa' a ƙasar na ɗaya daga cikin manyan ayyukan da ma'aikatarta ta ɓullo da su, don magance matsalar yunwa da buƙatun jin-ƙai a ƙasar.

"Don haka muna kira da hukumar WFP ta haɗa hannu da ma'aikatarmu domin cimma wannan buri", in ji ministar.

Ta ci gaba da cewa ”za a gudanar da wannan shiri ne domin magance wasu manyan matsalolin da ƙasarmu ke fuskanta".

Edu ta faɗa wa jami'an hukumar samar da abinci ta duniya cewa fiye da 'yan Najeriya miliyan 133 ne fama da talauci ta fuskoki daban-daban a ƙasar.

Ta ce shirin ciyar da 'yan firamare abinci, na ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen hukumar na kakkaɓe yunwa a Najeriya.

”Ma'aikatarmu za ta yi aiki da hukumomin ba da agaji da ke samar da abinci mai gina jiki da za a riƙa raba wa masu juna-biyu da ƙananan yara 'yan ƙasa da shekara biyar da 'yan firamare'', in Edu.

Ta ƙara da cewa burin ma'aikatar jin-ƙai shi ne ciyar da mutanen da ke buƙatar tallafi, ciki har da 'yan gudun hijira.

”A halin yanzu muna da sama da mutum 80,000 da ke zaune a matsayin 'yan gudun hijira a sassan Najeriya daban-daban", in ji Ministar.

Misis Edu ta ce ma'atarta ta ɓullo da wasu sabbin hanyoyi na bayar da tallafin jin-ƙai a ƙasar.

“Daga ciki akwai batun kafa cibiyoyin jin-ƙai a ƙananan hukumomin ƙasar 774 da ke faɗin ƙasar", in ji ta.