You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824800

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

Za mu kai Bazoum kotu saboda cin amanar ƙasa - Sojojin Nijar

Sojojin Nijar da suka juya mulki Sojojin Nijar da suka juya mulki

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun ce sun tattara isasshiyar shaidar za a iya gurfanar da hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Mohamed a gaban kotu, bisa laifin cin amanar ƙasa.

Sun kuma tuhume shi da yi wa tsaron cikin gida da na wajen ƙasar, zagon ƙasa.

Kakakin sojin Kanal Amadou Abdramane ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ta tashar talbijin ta ƙasar.

Sojojin na tsare da Bazoum da iyalansa a wani ɗaki na ƙarƙashin ƙasa a fadar gwamnati da ke birnin Yamai, tun bayan hamɓarar da shi a ranar Lahadi 26 ga watan Yulin bana.

Baya ga shugaban sojojin sun kuma kama wasu daga cikin jiga-jigan gwamnatinsa da ma na jam’iyyarsa ta PNDS Tarayya.

Mai magana da yawun gwamnatin sojin ya ce tuni sun riga ma sun tattara duk wasu bayanai da shaidun da suke buƙata domin gurfanar da Bazoum a gaban shari’a.

A sanarwar, kakakin ya ce, za su gurfanar da Bazoum tare da waɗanda ya kira masu haɗa baki da shi a cikin ƙasar da ma ƙetare a kan laifukan da suka zayyana, saboda musayar bayanan da ya yi tsakaninsa da wasu ‘yan ƙasashen waje da shugabannin ƙasashe da kuma shugabannin ƙungiyoyin ƙasashen duniya.

Bayan karɓe mulki tare da rushe zaɓaɓɓiyar gwamnatin tuni suka naɗa majalisar ministoci, tare da yin biris da duk wani kira na neman sasanta rikicin ta hanyar diflomasiyya, daga ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO da sauran ƙasashe da hukumomi masu rajin kare dimokraɗiyya na duniya.

Wannan ya janyo suka daga ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya.

Biris da halin ko-in-kula tare da ƙara kankane iko da kuma riƙe hamɓararren shugaban da sojin ke yi, ya sa ECOWAS ɗaukar matakai daban-daban a kan lamarin ciki har da sanya rundunar sojojinta ta ko-ta-kwana cikin shiri domin ɗaukar matakin soji a yunƙurin mayar da gwamnatin dimokraɗiyyar.

A ranar Litinin ɗin nan 14 ga watan Agusta, ECOWAS ake sa ran za ta ƙara matsa lamba ga sojojin na Nijar domin tattaunawa, kuma daman tuni sabbin masu ikon sun fara nuna sassauci a kan tattaunawa da ƙungiyar.

Sojojin Nijar sun amince su tattauna da ECOWAS

wasu bayanai na nuna cewa sojojin na Nijar a yanzu sun dan sassauto inda suka nuna alamun yarda su tattauna da ECOWAS.

A baya sojojin sun ma ki bayar da dama ga wata tawaga ta musamman da ECOWAS ta tura Nijar karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar domin tattaunawa.

A ranar Asabar majalisar dokokin kungiyar ta kasashen Afirka ta Yamma ta ce za ta tura wani kwamiti babban birnin Nijar din Niamey.

Sai dai kuma ba ta sanar da ainahin lokacin da za ta tura kwamitin ba.

Haka kuma a ranar Litinin din ne kwamitin tsaro na kungiyar kasashen Afirka ta AU, kasashe 55 zai gana domin tattauna yanayin na Nijar.

Ana ganin wannan wata alama ce ta nuna damuwa kan wannan juyin mulki, wanda ya kasance na bakwai a tsakanin kasashen Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya a cikin shekara uku.

Wani abu da ke daukar hankali a kan halin da nahiyar ke ciki dangane da juyin mulkin da ake samu shi ne ba wai makomar Nijar ba kadai, wadda kasa ce mai arzikin sinadarin yureniyom, da kuma kasancewarta kawar kasashen Yamma a yaki da masu ikirarin jihadi, akwai fargabar gogayya da ake samu da sauran manyan kasashen duniya abokan hammayyar Yamma, domin samun tasiri a nahiyar.

Kungiyar Tarayyar Afirka da majalisar Dinkin Duniya da kuma Tarayyar Turai dukkaninsu sun mara baya da ECOWAS a kan duk matakin da za ta dauka na mayar da dumukuradiyya da kuma Shugaba Bazoum kan mulki.

Kungiyoyin har ma da Amurka sun nuna damuwa game da lafiyar shugaban kan halin da aka ce yana ciki, saboda yadda yake tsare.

A ranar Asabar ne wata tawaga ta shugabannin addinin Musulunci karkashin jagorancin Sheik Bala Lau, na kungiyar Izala ta je Yamai domin tattauna batun na Nijar.

Tawagar wadda ta samu ganawa da sabon Firaministan da sojoji suka nada, Ali Mahaman Lamine Zeine, ta kuma samu ganawa da jagoran juyin mulkin wanda ya nada kansa sabon shugaban kasa Janar Abdourahamen Tchinai.

Bayanai sun nuna cewa tawagar ta shugaban na kungiyar Izala ta je Nijar din ne bisa izinin kungiyar ECOWAS da kuma shugabanta wanda kuma shi ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, domin kwantar da hankali ganin yadda lamarin ke neman haifar da tashin-tashina saboda matakin soji da ECOWAS ke cewa za ta dauka.

Ganin yadda matakin da ECOWAS ta dauka na sanya wasu jerin takunkumai a kan Nijar din na neman haifar da tsama tsakanin kasashen biyu, malaman sun nuna wa sojojin cewa wannan mataki ne na kungiya amma ba Najeriya ba, kamar yadda bayanai suka nuna.

A makon da ya gabata ne Sheik Bala Lau da ‘yan tawagar tasa suka gana da Shugaba Tinubu a Abuja, inda bayanai suka ce a wannan zama ne aka tsara zuwa ganawa da shugabannin juyin mulkin na Nijar.

ECOWAS ta jaddada cewa har yanzu dukkanin wata kofa ta sasanta rikicin na Nijar a bude take, kuma matakin soji zai ci gaba da kasancewa zabi na karshe idan komai ya ci tura.

Ministan harkokin waje na gwamnatin Nijar da sojojin suka hambarar, Hassoumi Massaoudou, y ace matakin soji da ECOWAS ke cewa za ta dauka a kan masu juyin mulkin ba yaki ne a kan Nijar da ‘yan kasar ba, matakin tabbatar da doka ne a kan wadanda ya kira masu garkuwa da mutane da masu taimaka musu.