You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776842

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Za a mayar da gidan Hitler wurin horar da ƴan sanda kan ƴancin ɗan'adam

Gidan Hitler Gidan Hitler

Za a yi amfani da gidan da aka haifi Adolf Hitler da ke Austria wurin horar da 'yan sanda kan abubuwan da su ka shafi 'yancin dan'Adam a cikin sabon cece-kuce da ake yi kan abin da za a yi da gidan.

Gwamnati ta siya gidan wanda ke yankin Braunau am Inn kusa da iyakan kasar Jamus a karkashin wani tsari a shekara ta 2016 bayan an dade ana jayayya.

An haifi dan mulkin kama karyan a wani dakin haya a saman bene a shekara ta 1889.

Ana sa ran za a fara aikin sauya tsarin gidan a kakar wannan shekaran.

Amma tsare-tsaren sun janyo cece-kuce. wasu 'yan kasar Austria na son a rusa gida gaba daya, kuma wani kwamitin kwararru ya yanke shawarar ruguje gidan saboda gudun kar ya zama wa 'yan akidar Nazi matattara.

Amma masu sukan wannan shawaran sun ce hakan zai iya zama kaman musanta tarihin Austria, a inda wasu ke cewa za a yi amfani da gidan a matsayin wani gidan yin sulhu ko kuma na masu aikin agaji.

A karkashin wannan sabon tsarin, ana sa ran kammala aikin gidan nan da shekarar 2025 a inda 'yan sanda za su fara amfani da shi idan shekara za zagayo, a cewan kamfanin yada labaru na ORF.

A lokacin mulkin Nazi, an maida gidan ya zama wurin karrama Hilter-wanda 'yan watannin kadan ya yi yana zama a gida-hakan ya sa garin ya yi farin jini wurin masu yawon bude ido

Amma yayin da karfin 'yan Nazi ya fara karewa a 1944, sai aka rufe gidan.

Gwmantin kasar Austia ta kwashe shekaru ta na karban hayan gidan daga wace ta mallaki gidan mai suna Gerlinde Pommer, a kokarin ta na hana yawon bude idon masu tsatsauran ra'ayi.

Masu aikin agaji sun yi amfani da gidan a matsayin wurin kula da gajiyayyu kafin Mrs Pommer ta hana a cigaba da gyaran gidan.

A shekarar 2016, gwamnati ta yi wata dokar da ta kwace gidan daga hannun ta bayan biyan diyyan sama da €800,000.

Bayan shekara uku ma'aikatar cikin gida ta kasar ta yi bayanin cewa za ta maida gidan ofishin 'yan sanda.

A karkashin mulkin Nazi Jamus ta mamaye kasar Austria a shekarar 1938, kuma ta shafe shekarau ta na ikirarin cewa ita ce kasa ta farko da ta fara shan wahalan Mulkin Nazi.

Amma akasarin mutane a lokacin sun amince da yunkurin wanda aka fi sani da 'Anschluss' ko 'connection', kuma yanzu Austria ta fara magana kan hannun da ta ke da shi cikin laifukan da aka aikata a karkashin mulkin Nazi.