You are here: HomeAfricaBBC2021 05 11Article 1258048

BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Za a kori Juventus daga buga gasar Serie A

An ja kunnen Juventus cewar za a koreta daga gasar Serie A domin alaka da European Super League An ja kunnen Juventus cewar za a koreta daga gasar Serie A domin alaka da European Super League

An ja kunnen Juventus cewar za a koreta daga gasar Serie A, idan ta ci gaba da hada gwiwa kan kikkirar European Super League.

A makon jiya Real Madrid da Barcelona da kuma Juventus suka fayyace makomarsu kan gasar da cewar suna fuskantar barazana daga hukumar kwallon kafar Turai.

Tun farko kungiyo 12 ne suka amince don fara gasar European Super League, wadda ba ta samu amincewar Fifa da Uefa da 'yan wasa da masu ruwa da tsaki ba.

Nan da nan kungiyoyin Ingila shida suka janye daga tsarin da suka hada da Manchester United da Manchester City da Liverpool da Chelsea da Tottenham da kuma Arsenal.

Daga baya ne AC Milan da Inter da kuma Atletico Madrid suma suka ce ba za su buga gasar ta European Super League ba.

Sauran ukun sune suka ci gaba da tsara yadda gasar za ta samu karbuwa, yayin da hukumar kwallon kafar Italiya ke kara matsi ga Juventus da ta fice daga tsarin.

Shugaban hukumar kwallon Italiya, Gabrile Gravini ya fadawa manema labarai cewar ''Da zarar Juventus ta ci gaba da sa hannu kan sabuwar gasar European Super League zuwa badi, ba za ta shiga wasannin Serie A ba''.

Inter Milan ce ta lashe kofin Serie A na bana, kuma na farko tun bayan shekara 11 da hakan ya kawo karshen kaka tara a jere da Juventus ke cin kofin na Italiya.

Kawo yanzu Inter Milan ce ta daya a kan teburi da maki 85, sai Atalanata ta biyu mai maki 72, iri daya da wanda AC Milan take da shi.

Kungiyar Napoli ce ta hudu a teburi mai maki 70, sai Juventus ta biyar da maki 69, kuma sauwa wasa uku-uku a karkare kakar bana.