You are here: HomeAfricaBBC2023 01 18Article 1697657

BBC Hausa of Wednesday, 18 January 2023

Source: BBC

Za a buga wasan Real Madrid da Real Sociedad 29 ga watan Janairu

Yan wasan Real Madrid Yan wasan Real Madrid

Mahukuntan gasar La Liga sun bayyana ranar da za a kara a fafatawar mako na 19 tsakanin Real Madrid da Real Sociedad.

An tsayar da ranar 29 ga watan Janairu domin Real Madrid ta karbi bakuncin Real Sociedad a Santiago Bernabeu.

Real Madrid tana ta biyu da maki 38 a teburin La Liga da tazarar maki uku tsakaninta da Barcelona mai jan ragama.

Ita kuwa Sociede tana mataki na uku mai maki 35, wato da tazarar maki uku tsakaninta da Real Madrid.

Kafin nan Real Madrid za ta buga Copa del Rey ranar Laraba, inda za ta ziyarci Villareal.

Wasan da kungiyoyin suka fafata a 2021/2022

Spanish La Liga Asabar 5 ga watan Maris din 2022  

  • Real Madrid       4 - 1  Sociedad  


  • Spanish La Liga Asabar 4 ga watan Disambar 2021        

  • Sociedad   0 - 2  Real Madrid