You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811927

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Yawan waɗanda ake bautarwa a Birtaniya ya ninka sosai

Hoton alama Hoton alama

An samu karuwar mutanen da ake sanya wa cikin sabon nau’in bautar zamani a Birtaniya, inda yawan ya ninka sama da kashi biyu na alkaluman da ake da su a shekarar da ta gabata.

A wani bincike da BBC ta yi ne ta gano cewa akwai mutane da dama wadanda ake ganin an sa su cikin wannan nau’in bauta, ko dai domin samun kudi ko kuma domin amfanin kai, a fannin kula da masu wasu larurori na lafiya ko kuma tsofaffi.

An samu bayanan ne daga wasu alkaluma da wata kungiya da ke yaki da lamarin, mai suna Unseen, ta bai wa BBC.

Wadanda suka gudanar da binciken sun ce a yanzu an fi samun mutanen da ake jefawa a wannan salon bautar zamani a wannan fannin.

Wata kungiya ta masu fafutukar kare ma’aikata daga bautarwa ko ci da gumi, a fadin Birtaniya (The Gangmasters and Labour Abuse Authority (GLAA)), ta bayyana cewa a yanzu akwai sama da mutum 300 da take gudanar da bincike a kan halin da suke ciki da ya danganci bautar.

Kungiyar ta Unseen ta ce dalilin da ya sa aka samu karin kiran waya da mutane ke yi wadanda ke aiki a irin wannan fanni na bayar da kulawa a cikin wata 12 da ya gabata shi ne saboda gwamnati ta saukaka yadda ma’aikata da ke wannan fanni ‘yan kasashen waje suke samun aiki a Birtaniya bayan ficewarta daga Tarayyar Turai, inda suke cike dubban guraban aiki.

Kungiyar ta ce ganin yadda ake samun mutane da dama masu wannan aiki sai kuma ake ci da gumin wasu ta fuskar bautar zamani.

Binciken da BBC ta gudanar ya nuna cewa daga shekarar da ta wuce zuwa watan Maris gwamnati ta bayar da takardar iizinin shiga Birtaniya ga kwararrun ma’aikata har 102,000, a fannin kula da lafiya da kuma masu bayar da kulawa a gida.

Wato karin kashi 171 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

A wata sanarwa da fitar gwamnatin ta ce an kashe sama da fam miliyan 17 da dubu 800 wajen sanya ido a kan batun na bautar zamani tun 2016.

Ba dai safai mutanen da ke samun kansu a bautar ta zamani ba kan yi magana su fadi halin da suke ciki.