You are here: HomeAfricaBBC2023 09 26Article 1851638

BBC Hausa of Tuesday, 26 September 2023

Source: BBC

Yaushe za a fara Gasar Cin Kofin Afirka a 2023?

Yan wasan Afrika Yan wasan Afrika

An tabbatar da tawagogin da za su je Ivory Coast, amma ko kun san ranar da za a fara Gasar Cin Kofin Afirka da yadda za ta shafi 'yan wasa da wadanda ke buga Premier League da duniya baki daya?

Kusan wata daya za a kwashe ana fafatawa daga watan Janairu zuwa Fabrairu, inda fitattun 'yan kwallo za su yi fatan lashe kofin babbar Gasar Kofin Afirka da hukumar Caf kan shirya.

Mai rike da kofin AfCON, Senegal Za ta kira fitattun 'yan kwallonta kamar Sadio Mane da ke wasa a Al-Nassr da na Chelsea, Nicolas Jackson, yayin da Masar, wadda ke kan gaba a yawan daukar kofin har karo bakwai - za ta kasance da kyaftin dinta mai taka leda a Liverpool, Mohamed Salah.

Ga jerin abubuwan da ya kamata ku sani har da jadawali da ma wasu 'yan wasa da ba za su buga wa kungiyoyinsu tamaula ba a lokacin Gasar.

Yaushe za a fara Afcon 2023?

Za a fara Gasar karo na 34 ta Cin Kofin Afirka daga ranar 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairun 2024.

Karo na biyu kenan da Ivory Coast za ta karbi bakuncin wasannin bayan na farko 1984.

Da farko, an tsara yin Gasar daga Juni zuwa Yulin 2023 amma daga baya aka sauya wasannin saboda fargabar da ake da ita kan buga gasar a tsakiyar damuna.

A shekarar 2024, za a yi amfani da taken Gasar da aka yi amfani da shi a 2023.

Wasan farko zai kunshi mai masaukin baki da ake kira The Elephants da za ta fito cikin rukunin farko da za a hada ta da wasu tawagogin kasashe.

Kungiyoyin da suka yi na daya da na biyu a kowanne rukuni za su kai zagayen 'yan 16 da wasu suka hada maki da yawa, amma suka kare a mataki na uku a rukuni daga shida da za a raba dauke da kasashe hudu kowanne - daga nan a buga kwata fainal da daf da na karshe da karawar neman mataki na uku da kuma fafatawar karshe.

Filin wasa na Alassane Ouattara da ke birnin Abidjan ne zai karbi bakuncin karawar karshe ranar 11 ga watan Fabrairu.

Me ya faru a lokacin neman shiga gasar?

Wannan Gasar za ta kunshi kasashe 24, kuma a karo na uku, bayan an kara fadada wasanninta a 2019.

Duk da yake Ivory Coast ce mai masaukin baki, amma ta buga wasannin neman shiga Gasar, inda ta yi ta biyu a rukuni na takwas da Zambia ta ja ragama.

Kasashen biyu sun hade da 22 da suka yi na daya da na biyu a kowanne rukuni inda jimilla suka zama kasa 24 don wasannin da za a buga.

Dukkan tawagogin da za su je Ivory Coast sun fafata a Gasar Kofin Afirka biyu a baya, in ban da Zambia, wadda ta lashe gasar a 2012, kuma za ta buga gasar a karon farko bayan 2015 da kuma wadda za ta kara karo na biyar, rabonta da gasar dai tun a 2010.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta kusan shiga Gasar a karon farko, amma ta barar da damar bayan ta yi rashin nasara a hannun Ghana, wadda ke sama da ita.

Tawagar Gabon ta Pierre-Emerick Aubameyang ita ce fitacciya da ba za ta je Gasar ba.

Yaushe za a raba jadawalin Afcon kuma wadanne matakai za a bi?

Za a raba jadawalin Afcon 2023 a birnin Abidjan ranar 12 ga watan Oktoba da karfe 7 na yamma agogon GMT.

Za a yi la'akari da kwazon tawagogin a jerin gwanayen kasashen kwallon kafa da Fifa kan fitar, kuma kasa 24 aka raba zuwa tukunya hudu.

Ko da yake, Ivory Coast yanzu haka tana mataki na tara a kan gaba a kwallon kafa a Afirka, ita ma an saka ta a tukunyar raba rukuni.

Jerin tukwane da matakin kasashe a jadawalin Fifa a cikin baka:

Tukunyar farko - Ivory Coast (*50), Morocco (13), Senegal (20), Tunisia (29), Algeria (34), Egypt (35)

Tukunya ta biyu - Nigeria (40), Cameroon (41), Mali (49), Burkina Faso (58), Ghana (60), DR Congo (64)

Tukunya ta uku - South Africa (65), Cape Verde (71), Guinea (81), Zambia (82), Equatorial Guinea (92), Mauritania (99)

Tukunya ta hudu - Guinea-Bissau (106), Mozambique (113), Namibia (114), Angola (117), The Gambia (118), Tanzania (122)

Za a raba kasashen zuwa rukuni shida da za su kunshi kasa hurhudu kowanne. Kuma za a sanar da ranaku da lokutan da za a fafata wasanni a Gasar ta Afcon 2023.

Filaye shida za a buga wasannin:


  • Alassane Ouattara Stadium, Abidjan (Mai cin 'yan kallo 60,000)
  • Felix Houphouet Boigny Stadium, Abidjan (Mai cin 'yan kallo 33,000)
  • Stade de la Paix, Bouake (Mai cin 'yan kallo 40,000)
  • Amadou Gon Coulibaly Stadium, Korhogo (Mai cin 'yan kallo 20,000)
  • Laurent Pokou Stadium, San Pedro (Mai cin 'yan kallo 20,000)
  • Charles Konan Banny Stadium, Yamoussoukro (Mai cin 'yan kallo 20,000)

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF na gayyatar fitattun 'yan kwallon nahiyar a lokacin da take gabatar da jadawalin.

Ana sa ran za a ga fitattun 'yan wasan Ivory Coast, Kolo da Yaya Toure, wadanda suka buga wa the Elephants tamaula, kuma suka doke Ghana kafin gasar a Kofi na biyu da Ivory Coast ta dauka a 2015.

Ranakun da 'yan wasa masu buga Premier League za su rasa?

Ga jerin ranakun da 'yan wasa za su rasa da kofin da ba za su buga ba, amma ya danganta da dadewar da tawagar kasa za ta yi a Gasar Cin Kofin Afirka, AFCON.

Hutu: 15-28 Janairu

Wasan kofi da za a yi a karshen mako:

Karsen makon Janairu ranar 6 ko kuma 7 (FA Cup zagaye na uku)

Karancin wasan da ba za su buga ba:

Karawa daya (Premier League)

Yawancin fafatawar da za a buga babu su:

Takwas (fPremier League hudu, FA Cup zagaye na hudu, Carabao Cup daf da karshe wasan farko da na biyu, Champions League zagayen 'yan 16 na farko)

Ranar da za su iya komawa buga wasannin:

27 ga watan Janairu (Kammala wasannin cikin rukuni), 4 ga watan Fabrairu (Zagayen 'Yan 16), 11 ga watan Fabrairu (Zagayen daf da na kusa da na karshe), 18 ga watan Fabrairu (Daf da karshe da wasan karshe)

Yaya Gasar Saudi Arabia da ta sauran kasashe?

Kwanan wata a Saudi Arabia da wasu fitattun Gasar Turai.

Saudi Pro League

Hutu: 29 ga watan Disamba - 14 ga watan Fabrairu

Ranar wasan karshe a Gasar:

28 ga watan Disamba (Pro League)

Karancin wasan da ba za su buga ba:

Babu ko daya

Yawancin fafatawar da za a buga babu su:

Wasa uku (Saudi Super Cup daf da karshe da wasan karshe, Asian Champions League zagayen 'yan 16 zagayen farko).

Ranar da za su iya komawa buga wasannin:

Saudi Super Cup games cikin Janairu (wasan karshe cikin rukuni), 17 ga watan Fabrairu (wasannin zagaye na biyu)

Spanish La Liga

Hutu: 22 ga watan Disamba - 1 ga watan Janairu

Ranar karshe a Kofi:

Karshen mako 6/7 ga watan Janairu (Copa del Rey zagayen kasashe 32)

Karancin wasan da ba za su buga ba:

Wasa biyu (La Liga)

Yawancin fafatawar da za a buga babu su:

Wasa 11 (La Liga biyar, Copa del Rey zagayen 'yan 16, kwata fainal, daf da karshe wasan farko, Supercopa de Espana daf da karshe da karawar karshe, Champions League zagayen 'yan 16 wasan farko)

Ranar da za su iya komawa buga wasannin:

27 ga watan Janairu (group stage exit), 4 ga watan Janairu (last 16), 7 ga watan Janairu (kwata fainal), 17 ga watan Fabrairu (daf da karshe da wasan karshe)

Italian Serie A

Hutu: Ba hutu

Wasan karshe a kungiya:

Karshen mako 6/7 ga Janairu (Serie A)

Karancin wasan da ba za su buga ba:

Wasa biyu (Serie A)

Yawancin fafatawar da za a buga babu su:

Wasa 11 (Serie A guda shida, Supercoppa Italiana daf da karshe da wasan karshe, Coppa Italia zagayen 'yan 16 da na kwata fainals, Champions League zagayen 'yan 16 wasan farko)

Ranar da za su iya komawa buga wasannin:

27 ga watan Janairu (Kammala wasannin cikin rukuni), 4 ga watan Fabrairu (Zagayen 'yan 16), 7 ga watan Fabrairu (kwata fainals), 17 ga watan Fabrairu (karawar daf da karshe da wasan karshe)

French Ligue 1

Hutu: 21 ga watan Disamba - 13 ga watan Janairu

Wasan karshe:

Karshen mako 6/7 ga Janairu (Coupe de France zagayen kungiyoyi 32)

Karancin wasan da ba za su buga ba:

Wasa biyu (Ligue 1)

Yawancin fafatawar da za a buga babu su:

Takwas (Ligue 1 wasa biyar, Coupe de France zagayen 'yan 32 da na 'yan 16, Champions League zagayen 'yan 16 wasan farko)

Ranar da za su iya komawa buga wasannin:

27 ga Janairu (wasan karshe na cikin rukuni), 4 ga watan Fabrairu (zagayen 'yan 16), 7 ga watan Fabrairu (kwata fainal), 16 ga watan Fabrairu (daf da karshe da wasan karshe)

German Bundesliga

Hutu: 18 ga watan Disamba - 11 ga watan Janairu

Wasan karshe a kofi:

Karshen mako 16/17 ga watan Disamba (Bundesliga)

Karancin wasan da ba za su buga ba:

Wasa biyu (Bundesliga)

Yawancin fafatawar da za a buga babu su:

Wasa bakwai (Bundesliga biyar, DFB-Pokal daf da na kusa da na karshe, Champions League zagayen 'yan 16 zagayen farko)

Ranar da za su iya komawa buga wasannin:

27 ga watan Janairu (wasan karshe a cikin rukuni), 4 ga watan Fabrairu (zagayen 'yan 16), 7 ga watan Fabrairu (kwata fainal), 16 ga watan Fabrairu (daf da karshe da wasan karshe)