You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837733

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Yaushe mutum-mutumi za su fara yi wa ɗan'adam gyaran gado da ayyukan gida?

Hoton alama Hoton alama

Ka taɓa yin tunanin wata gagarumar kasuwar kayayyaki a duniya, kana tunanin kasuwar wayoyin hannu ko ta ƙananan motoci ko ta wasu abubuwa?

Duka waɗannan kasuwanni ne da ke kan ganiyarsu a yanzu, to sai dai cikin gomman shekaru masu zawa za a samu wata haja da za ta shigo kasuwa ta kuma zarta su a tashe, kamar yadda Geordie Rose babban sakataren kamfanin Sanctuary AI.

Kamfanin wanda ke ƙasar Canada na ƙera mutum-mutumi da ake kira 'Phoenix', waɗanda idan an kammala su, za su iya fahimtar abubuwan da muke buƙata, su fahimci yadda duniya ke aiki, sannan za su iya fahimtar umarni daga gare mu.

"Fasahar da aka ɗauki lokaci mai tsawo ana ƙerawa, ita ce babbar fasaha irinta ta farko a harkar fasahar zamani," in ji shi.

Mista Rose bai bayyana takamammen lokacin da yake ganin mutum-mutumin za su fara shigowa kasuwa ba, domijn gudanar da ayyuka kamar wanki da gyara gado. Amma wasu da na yi magana da su a kamfanin sun ce watakila nan da shekara 10 masu zuwa.

Akwai gomma kamfanonin fasaha a duniya da suka duƙafa wajen ƙera irin waɗanna mutum-mutumin.

A birtaniya, Dyson na zuba jari a harkar ƙirƙirar basira ta AI, inda yake ƙra mutum-mutumi da nufin yin ayyukan gida.

A yanzu babban kamfanin da ke kan gaba wajen ƙera irin wadannan na'urori shi ne kamfanin Tesla mallakin Elon Musk.

Mista Musk ya ce kamfanin zai fara sayar da na'urorin nan da 'yan shekaru masu zuwa.

A halin da ake ciki kamfanonin fasaha na gasa a fannin ƙirƙirarriyar basira ta AI ta hanyar ƙera mutum-mutumin da za su iya yin ayyukan da ɗan'adam zai yi.

"FasahaTr zamani na ci gaba da bunƙasa cikin shekara 10.A yanzu kusan kowane wata sai an samu wani gagarumin ci gaba a fannin fasahar AI a duniya'', in ji Mista Rose.

A shekarar da ta gabata ne kamfanin Mainstream ya nuna sha'awa a fannin fasahar AI a lokacin da aka fito da shafin mai fassara bayanan mabambantan harsuna. Shafin na fassara rubuce-rubuce da hotuna zuwa mabambantan harsuna.

To amma yadda fasahar AI ke ƙara bunƙasa a duniya, ta hanyar samar da mutum-mutumin da za su iya yin ayyuka irin na ɗan'adam.

Saɓanin shafin ChatGPT da takwarorinsa, su wadanna mutum-mutumi za su iya fahimtar duniya da irin alaƙar da tsakanin abubuwa da ke cikinta.

Duka ayyukan da ɗan'adam ke yinsu cikin sauki, mutum-mutumin za su iya yinsu da ƙwarin gwiwwa.

Alal misali a wani gwajin na'urorin da kamfanin Sanctuary ke yi, mutum-mutumin da ake kira 'Phonix' na ta ninke kaya tare da sanya su cikin leda a wani shagon wankin kaya a Canada.

"Wannan abu ne mai ɗan wahala, domin kuwa akwai abubuwa masu rikitarwa domin kuwa ledojin na da santsi, kuma farare ne ta yadda za aka iya ganin abin da ke cikinsu, amma akwai wurin da ake buɗe su, kuma duk da haka mutum-mutumin da fahimtar duka waɗannan'', in ji shi.

Kamfanin Sanctuary na da tsarin bayar da horo ga mutum-mutumin da suke ƙerawa game da ayyukan da yake so su yi, kmaar sanya abu cikin leda tare da liƙe shi.

Daga nan sai a yi gwajinsu a duniya, domin ganin yadda suka fahimci abubuwa a duniya da yadda alaƙa tsakanin abubuwan ke gudana.

A wannan mataki akan horas da 'Phoenix' yin abubuwa daban-daban har aƙalla 20.

Mita Rose na kallon wannan matsayin hanyar inganta ayyukan mutum-mutumin - fahimtar wani aiki na musamman a harkar kasuwanci. Mutum-mutumin za kuma su iya yin ayyukan gida, lamarin da zai iya kawo cikas ga masu ayyukan.

Daya daga cikin manyan ƙalubalen da za a fuskanta shi ne yadda za a bai wa mutum-mutumin damar taɓa abubuwa.

Akwai bukatar yin nazari mai zurfi a wajen ƙera wadannan na'urori, ta yadda za su iya fahimtar dimbim abubuwa n da ke faruwa a gidaje da kasuwanni.

"Ba zai yiwu ka sanya mutum-mutumi a wani wuri da ba ka yi masa horo ba, sannna ka yi tunani zai yi maka yadda kake buƙata, ba tare da ya lalata maka abubuwa ba. Lokaci ne na baje-koli fasaha," kamar yadda Farfesa Alireza Mohammadi, wanda ya kafa wani ɗakin gwaje-gwajen ƙera mutum-mutumi a jami'ar Michigan-Dearborn.

Ya ce za ka iya bai wa na'urorin horokan miliyoyin abubuwa, amma duk da haka dole wata rana su hadu da wasu abubuwan da ba a ba su horo a kansu ba.

Daya daga cikin matsalolin shi ne, mutum na da saurin fahimtar wani yanayi da ya same shi ko ya shiga. Misali kana cikin tafiya kwatsam! sai kare ya ɓullo gabanka, yana yi maka haushi, irin razanar da za ka shiga a wannan lokaci tare da matakin da za ka dauka cikin gaggawa abu ne da baya buƙatar dogon nazari ko tunani, kawai zuwa suke yi.

Cusa wa mutum-mutumin irin wannan yanayi a bu ne mai matuƙar wahala.

"Cikin shekara 10 masu zuwa za mu iya samun na'urorin da za su iya yawo a tsakaninmu ta hanyar taimakon da muke ba su, to amma ba a kowanne wuri ba," in ji Farfesa Mohammadi.

Barazana ga ayyukan mutane

To amma Idan aka magance waɗannan matsaloli, shin na'urorin za su iya gudanar da ayyukan da mutane ke yi yanzu?

Mista Rose ya ce akwai ƙarancin ma'aikata a fadin duniya masu yawa, kuma yana mafarkin wata rana mutum-mutumin da yake ƙerawa za su cike giɓin da ake da shi na ma'aikata.

Stewart Miller shi ne shugaban hukumar samar da mutum-mutumi - da ke haɗin gwiwwa da jami'ar Heriot-Watt da jami'ar Edinburgh - da ya mayar da hankali wajen samar da mutum-mutumi na fasahar AI.

"Haƙiƙa, akwai ayyukan mutane da mutum-mutumi za su riƙa yi, abin tambayar a nan shi ne me hakan ke nufi?'', in ji shi.

"Mutane za su fuskanci ƙalubale. Amma idan muka yi nazari a kan haka, sai mu mayar da hankali kan abubuwan da ɗan'adam yake yi, domin kara inganta su ta yadda za mu riƙa yinsu cikin sauri ba kamar yadda na'urorin za su ɗauki lokaci ba."