You are here: HomeAfricaBBC2023 01 11Article 1693628

BBC Hausa of Wednesday, 11 January 2023

Source: BBC

Yarjejeniyarmu da Ronaldo ba ta ƙunshi taimaka wa Saudiyya kan Kofin Duniya ba - Al Nassr

Cristiano Ronaldo Cristiano Ronaldo

Ƙungiyar Al Nassr da ta ɗauki Cristiano Ronaldo ta musanta rahotannin da ke cewa cikin yarjejeniya tsakaninsu da ɗan wasan har da batun taimaka wa Saudiyya waje neman karɓar baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta 2030.

Rahotanni sun yi iƙirarin cewa Ronaldo zai karɓi fan miliyan 177 ƙari a kan albashinsa na fan miliyan 177 duk shekara don ya tallata yunƙurin Saudiyya da take son karɓar baƙuncin gasar.

Sai dai ƙungiyar ta ce yarjejeniyar "ba ta ƙunshi shiga harkokin neman Gasar Kofin Duniya ba".

"Abin da ya sa a gaba shi ne kan Al Nassr da kuma yin aiki da sauran abokan wasansa don taimaka wa kulob ɗin samun nasara," a cewarta.

Kyaftin ɗin na Portugal ya koma Al Nassr ta Saudiyya ne a kyauta a watan da ya gabata bayan ya bar Manchester United sakamakon hirar da ya yi inda ya caccaki ƙungiyar da mamallakanta.

Zai fara buga wa Al Nassr wasa a ranar 22 ga watan Janairu a fafatawa da Ettifaq.

Sai dai kafin nan, ana sa ran zai kara da abokin hamayyarsa Messi a wani wasan talla da PSG za ta buga.

Wasu rahotanni sun ruwaito Saudiyya na shirin neman ɗaukar baƙuncin Kofin Duniya da haɗin gwiwar Masar da kuma Girka wadda za a yi a 2030.