You are here: HomeAfricaBBC2021 04 10Article 1228684

BBC Hausa of Saturday, 10 April 2021

Source: BBC

Yarima Philip: Shugabannin kasashen duniya na mika sakon ta'aziyyar rasuwar mijin Sarauniya

Yarima  Philip, Duke na Edinburgh wanda ya mutu yana da shekaru 99 Yarima Philip, Duke na Edinburgh wanda ya mutu yana da shekaru 99

Sarakuna, shugabannin kasashe da firaiministoci a fadin duniya, na yanzu da wadanda suka gabata, suna ta aike wa da sakon ta'aziyya kan rasuwar Yarima Philip, Duke na Edinburgh wanda ya mutu yana da shekaru 99.

Sarki da Sarauniyar Sifaniya sun aike da sakon telegram da ke cewa "Ya ke mai girma Goggo Lilibet" domin yin alhinin rasuwar "Mai girma Philip".

Shugabannin kungiyar kasashen rainon Ingila sun jinjina masa bisa ayyukan da ya yi na ci gaban jama'a.

Sun gode masa bisa yadda ya tafiyar da rayuwar a kan aiki tukuru da sadaukarwa ga Sarauniya.

Shugaban Amurka Joe Biden shi ma ya mika sakon ta'aziyyarsa, inda ya yaba wa marigayin a kan sadaukarwarsa "ga al'ummar Birtaniya, da kungiyar kwamanwel da iyalansa", da ma gudunmawar da ya bayar lokacin Yakin Duniya na Biyu, da rajin inganta muhalli da kuma karfafa wa matasa gwiwa.

Mijin sarauniyar, wanda Fadar Buckingham ta sanar da mutuwarsa ranar Juma'a, ya yi wa Sarauniya rakiya a tafiye-tafiye daruruwa da ta yi zuwa kasashen waje.

'Jin dadin zama'

Yarima Philip yana da dangantaka ta jini da gidajen sarautar kasashen Turai da dama, na da da na yanzu, kuma da yawa daga cikinsu sun aiko da sakon ta'aziyya.

A sakon telegram daga Sarki Felipe da Sarauniya Letizia na Sifaniya suka aika, sun bayyana "dukkan soyayyarmu da kaunarmu" zuwa to Aunt Lilibet (sunan da mijin sarauniya yake kiranta da shi) da Dear Uncle Philip.

"Ba za mu taba mantawa da zaman da mua yi tare da shi ba da kuma abin alherin da ya bar wa Masarautar Birtaniya da ma kasar ba," in ji sakon da suka aika wa Sarauniya.

Sarkin Sweden Carl Gustaf ya bayyana alhinin rasuwar Yarima Phillip, yana mai cewa shi "babban aboki ne ga iyalina shekara da shekaru, kuma muna mutunta wannan abota".

Mai magana da yawun masarautar Sweden Margareta Thorgren ta shaida wa BBC cewa sarkinsu da yarima sun taba shiga jirgin ruwa zuwa wani waje a Ingila, tana mai karawa da cewa: "Daga wannan lokacin abota mai kwari ta kullu a tsakaninsu."

Iyalan masarautar Netherlands sun ce ba za su manta da Yarima Philip saboda yadda suke girmama shi, suna masu karawa da cewa: "Ya sadaukar da rayuwarsa mai tsawo wajen bauta ga al'ummar Birtaniya da kuma ayyukansa masu dama."

Sarkin Belgium Philippe ya ce shi da Sarauniya Mathilde za su "ci gaba da tuna abubuwan alherin da ya yi musu yayin da suka hadu".

'Madogarar Sarauniya'

Kungiyar Kwamanwel - guda 54, wadanda akasarinsu kasashe rainon Ingila ne da ke da mutum biyan 2.4, ta aike sakon ta'aziyyarta.

Firaministan Australia Scott Morrison ya bayyana a wata sanarwa cewa: "Yarima yana cikin 'yan mazan jiya da ba za mu taba ganin kamarsu ba."

Ya yaba wa yariman bisa kasancewarsa uba ga kungiyoyi da dama a Australia.

Ita ma Firaiministar New Zealand Jacinda Ardern ta yaba wa marigayin, tana mai cewa "dubban matasa sun cimma manufofi da dama" ta hanyar lambar yabo ta Hillary Award wadda yariman ya assasa.

Firaministan India Narendra Modi shi ma ya mika ta'aziyyarsa game da "ayyukan ci gaban al'umma da dama" da yarima ya yi.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya ce rayuwar yariman "wata alama ce ta kaunar iyali da kuma hadin kan Birtaniya da ma kasashen duniya" - mutumin da ya yi aiki tukuru wajen "tabbatar da zaman lafiyar dan adam".