You are here: HomeAfricaBBC2023 12 11Article 1896686

BBC Hausa of Monday, 11 December 2023

Source: BBC

'Yan wasan Man United na goyon bayan Ten Hag - McTominay

Scott McTominay ya ce suna goyon bayan Erik ten Hag Scott McTominay ya ce suna goyon bayan Erik ten Hag

Scott McTominay ya ce suna goyon bayan Erik ten Hag kan yadda yake gudanar da aikinsa, bayan kalubale da Manchester United ke fuskanta a bana.

Ranar Asabar ne Bournemouth ta doke United 3-0 a Old Trafford yayin karawar Premier League karo na 11 daga wasa 23 da ta yi rashin nasara a dukkan wasannin da ta buga kenan.

Ya zama wajibi United ta doke Bayern Munich, idan tana son kai wa zagaye na biyu a Champions League a kakar nan.

Bayern Munich, wadda ta kai zagaye na biyu a gasar zakarun Turai za ta ziyarci Man United mai maki hudu ta karshen teburi ranar Talata.

''Hakki ne na dukkan 'yan wasa, shi ne kan gaba kuma mafi muhimmanci,'' in ji McTominay.

''Muna da fitattun 'yan wasa, yanzu haka muna kara kaimi don ganin mun koma kan ganiya.''

''Muna da kwararrren koci da masu taimaka masa. Muna so mu mayar da kungiyarmu kan ganiya. Wannann shi ne fatanmu.''

McTominay, mai shekara 27, ya fara buga wa Manchester United wasa a 2017 karkashin Jose Mourinho.

A makon jiya ne Ten Hag, wanda yake kakarsa ta biyu a Old Trafford, ya yi watsi da cewar rabin 'yan wasan United ba sa tare da shi, ya ce dukkan 'yan kwallon kansu a hade yake.

Wasu tsoffin koci-kocin United, David Moyes da Louis van Gaal da Mourinho da Ole Gunnar Solskjaer da kuma Ralf Rangnick, sun samu kansu cikin matsalar rashin jituwa da 'yan wasa.

United tana mataki na shida a teburin Premier League kuma ta karshe a teburin Champions League, wadda ke bukatar doke Bayern Munich kafin ta kai zagayen 'yan 16.