You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837760

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

'Yan wasan Barca da suka je gidan Osasuna buga La Liga

Yan wasan Barcelona a cikin murna Yan wasan Barcelona a cikin murna

Barcelona ta je gidan Osasuna domin buga wasan mako na hudu a gasar La Liga da za su kara ranar Lahadi.

Wasan da suka kara a bara a tsakaninsu:

Kakar 2022/2023

Spanish La Liga Talata 2 ga watan Mayun 2023

  • Barcelona 1 - 0 Osasuna


  • Spanish La Liga Talata 8 ga watan Nuwambar 2022

  • Osasuna 1 - 2 Barcelona


  • Ranar Asabar Barcelona ta gabatar da Joao Cancelo da kuma Joao Felix a gaban magoya bayanta.

    Tuni kuma koci Xavi Hernández ya saka Cancelo, wand zai sa riga mai lamba biyu da Joao Felix da zai sa riga mai lamba 14 cikin wadanda za su fuskanci Osasuna.

    Haka kuma Inigo Martínez, wanda ke jinya, an damka masa riga mai lamba biyar, yayin da aka bai wa Alejandro Balde riga mai lamba uku.

    Haka kuma a karon farko Barcelona za ta sa riga mai ratsin layuka a filin wasa na Pamplona, kayan da za ta dinga amfani da su a fafatawar da ba a gida ba.

    'Yan wasa 22 da Barcelona ta je da su gidan Osasuna:

    Ter Stegen, Joao Cancelo, Balde, I. Martínez, Gavi, Ferran, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña, João Félix, Christensen da kuma Marcos A.

    Sauran sun hada da Romeu, S. Roberto, F. De Jong, Gündoğan, Kounde, Lamine Yamal, M. Casadó, Kochen, Fermín da kuma Cubarsí.