You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853984

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

'Yan sandan Sifaniya sun kai samame ofishin alƙalan wasa kan zargin Barcelona da ba su cin hanci

Filin wasan Camp Nou ta Barcelona | Hoton alama Filin wasan Camp Nou ta Barcelona | Hoton alama

Ƴan sandan Sifaniya sun kai samame hedikwatar alƙalan wasan ƙasar a wani ɓangare na binciken zargin cin hanci da ake yi wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona.

Barcelona na fuskantar zargin cin hanci kan wasu kuɗaɗe da ta tura wa Jose Maria Enriquez Negreira, wani tsohon mataimakin shugaban kwamitin alƙalan wasan, don a dinga yi musu alfarma a wasanninsu.

Barcelona ta musanta zargin kuma ba a kama kowa ba a lokacin samamen a birnin Madrid.

An faɗa wa BBC Sport cewa alƙalin da ke sauraron shari'ar ya buƙaci a kwamatin alƙalan wasan mai suna Technical Committee of Referees (CTA) ya gabatar masa da wasu takardu.

Ba a kai takardun ba kuma dalilin da ya sa aka ɗauki matakin kai samamen ke nan a ranar Alhamis.

Tun farko, ofishin shigar da ƙara na Barcelona ne ya tayar da batun a watan Maris, inda ita ma hukumar ƙwallon Turai ta ƙaddamar nata binciken jim kaɗan bayan haka.

Ana zargin Barca ta biya Negreira da kamfaninsa Dasnil 95 yuro miliyan 8.4.

Ƙungiyar ta biya jimillar kuɗi yuro miliyan 1.4 tsakanin 2016 da 2018, kuma ta biya Negreira kusan miliyan bakwai tsakanin 2001 da 2018, wato shekarar da ya bar muƙaminsa da kwamitin alƙalan wasan.