You are here: HomeAfricaBBC2023 01 28Article 1703774

BBC Hausa of Saturday, 28 January 2023

Source: BBC

'Yan sandan Isra'ila sun kama ɗan shekara 13 da zargin harbin Yahudawa

Dan sandan Israa-ila Dan sandan Israa-ila

An kama yaro Bafalasɗine mai shekara 13 da zargin harbin wasu Yahudawa a Birnin Ƙudus ranar Asabar, a cewar rundunar 'yan sandan Isra'ila.

Mutum biyu aka harba - uba da ɗansa - kuma aka ji musu munanan raunuka, wasu mutane suka harbi maharin kuma suka jiakkata a gefen titi.

Lamarin ya faru kwana ɗaya bayan wani Bafalasɗine ya harbe mutum bakwai da kuma raunata wasu uku a cocin Yahudawa da ke Gabashin Birnin Ƙudus.

'Yan sanda sun kama mutum 42 game da hannunsu a harin na ranar Juma'a.

Da yake magana kan harin na Asabar da aka kai a unguwar Silwan da ke wajen Ƙudus, wani mai magana da yawun 'yan sandan Isra'ila ya ce maharin ya dimfari mutum biyar lokacin da suke isa wurin ibada, inda ya ji wa biyu "mummunan rauni".

"An samu ƙaruwa sosai a hare-haren ta'addanci," in ji Dean Elsdunne, yana mai cewa ana kula da maharin a asibiti.

A martanin da suka mayar game da hare-haren, hukumomi sun girke jami'an yaƙi da ta'addanci "dindindin" a faɗin Ƙudus "don mayar da martani kan duk wani abu da zai taso".

Ma'abota shafukan sada zumunta sun bayyana maharin na ranar Juma'a a matsayin Bafalasɗine mazaunin Gabashin Ƙudus, wanda 'yan sanda suka ayyana a matsayin "ɗan ta'adda".

Da yake magana a wurin da aka kai harin ranar Juma'a, Kwamashinan 'Yan Sandan Isra'ila Kobi Shabtai ya kira abi da cewa "ɗaya daga cikin hare-hare mafiya muni da muka fuskanta tsawon shekaru".

Masu ibada a Isra'ila sun taru don yin addu'o'i a bikin Yahudawa na Sabbath a unguwar Neve Yaakov, kuma an buɗe wutar ce lokacin da mutanen ke barin wurin da misalin ƙarfe 5:15 (agogon Najeriya).

Mayaƙan gwagwarmaya na Falasɗinawa sun yi murna da harin, amma ba su bayyana ko ɗaya daga cikin mambobinsu ne ya kai harin ba.

Hankali ya fara tashi ne tun daga lokacin da aka kashe Falasɗinawa - mayaƙa da farar hula - tara yayin samamen da sojojin Isra'ila suka kai a Jenin da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ranar Alhamis.

'Yan gwagwarmayar Falasɗinawa sun mayar da martani ta hanyar harba makaman roka daga birnin Gaza zuwa cikin Isra'ila, ita kuma ta kai hare-hare ta sama kan Gaza.

Isra'ila ta ƙwace tare da mamaye Gabashin Ƙudus tun bayan yaƙin Gabas ta Tsakiya a 1967 kuma ta mayar da shi babban birninta, duk da cewa akasarin ƙasashen duniya ba su amince da hakan ba.

Falasɗinawa na kallon Gabashin Ƙudus ɗin a matsayin babban birnin ƙasar da suke fatan kafawa nan gaba.