You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837727

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

'Yan sanda sun fara dirar mikiya kan masu yaɗa jita-jitar 'matsafa masu shan jini'

File foto File foto

Sakamakon jita-jitar da ta gauraye wasu sassan arewacin Najeriya game da wasu mutane da ake zargin masu shanye jini da 'yan shafi mu-lera, 'yan sanda sun fara yin dirar mikiya a kan wasu da ake zargin suna yaɗa irin wannan jita-jita, da kan janyo a far wa wasu mutane da ba su ji ba, ba su gani ba.

Ana ta yaɗa jita-jitar cewa wasu mata na yin sallama a gidajen mutane, inda suke roƙon ruwan sha, amma a cewar masu jita-jitar sai mutanen su zuƙe wa wanda ko wadda ta ba su ruwa jini.

A wata ruwayar kuma, an ce mutanen da ake zargi suna kwashe wa namiji mazakuta, yayin da mace take rasa mamanta.

Irin wannan jita-jita dai, ta kai ga har cincirindon mutane suna far wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a jihohi kamar Kano da Bauchi da Kaduna.

Sai dai a yanzu, hukumomi sun fara yin dirar mikiya a kan mutanen da ke yaɗa irin wannan jita-jita maras tushe.

Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar Kano ta fitar, ta ce wannan lamari ya yi ƙamari ne tsakanin ranar Juma'a zuwa ranar Lahadi 3 ga watan Satumba.

Ta yi Allah-wadai da abin da ta kira "cin mutuncin matafiya da baƙin fuska" a unguwannin da ba a san su ba.

Inda ta ce ta gudanar da bincike kan wasu daga cikin koken da aka shigar mata kuma ta gano duka zarge-zarge "ba su da tushe, balle makama, don haka, ƙarya ne".

Sanarwar da kakakin rundunar a Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta ce " wasu ɓata gari ne ke neman ta da zaune-tsaye ta hanyar haifar da gaba da ƙiyayya da jefa tsoro da firgici a zukatan mutane domin hana zaman lafiya".

A ranar Lahadi 3 ga watan Satumba rundunar ta ceto wasu 'yan mata ƙanana uku da shekarunsu bai wuce tsakanin 12 zuwa 15 ba, a unguwar Kwana Hudu da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa.

"Mun samu kira a ranar Lahadi cewa an kama wasu 'yan mata a wani gida da ke layin Ɗanfili, ana zarginsu da shan jini, nan da nan jami'ai suka garzaya suka cece su aka tafi da su asibitin Gwagwarwa aka duba su aka sallame su.

"Bayan gudanar da bincike mun gano sun shiga wani gida ne neman cajin waya, lokacin da suke cajin sai ɗaya ta nemi ta shiga banɗaki, sai matar gidan ta sanya ihu aka wo mata ɗauki, makota suka shigo suka yi wa yaran duka. Mijinta kuma ya kullesu su a ɗaki.

"Bincikenmu ya gano cewa babu wanda suka taba, kawai zargi ne maras tushe, mun kama mata da mijin sannan mun kama wasu daga cikin waɗanda suka taimaka aka yaɗa wannan jita-jita," in ji sanarwar.

Ka zalika irin wannan lamarin ya faru a unguwar Zango da ke Ƙaramar Hukumar Ungoggo, inda aka tsare wasu mata biyu da ake zargi da irin wannan lamari.

"Bayan samun kiran waya, 'yan sandan sun garzaya inda lamarin ya faru tare da ceto matan aka kuma garzaya da su wani asibiti.

"Bincike ya tabbatar mana da babu abin da suka yi, kawai an fuskanci baƙin fuska ne a unguwar, amma an shawo kan lamarin," in ji sanarwar.

Irin wannan ta faru a hotoro in ji sanarwar, shi ma an kama mutum shida dalilin zargin wasu mata da aka yi wa duka saboda sabbin fuska ne a unguwar.

Rundunar 'yan sandan ta yi alƙawarin kama duk masu yaɗa wannan jita-jita, kuma za ta ci gaba da kare dukka waɗanda suke faɗawa tarkon ɓatagarin da ke neman haifar da tashin hankali a Kano.