You are here: HomeAfricaBBC2023 05 15Article 1767602

BBC Hausa of Monday, 15 May 2023

Source: BBC

'Yan fashin daji sun kashe mutum 18 a Zamfara kuma sun sace gommai a Neja

Hoton alama Hoton alama

'Yan fashin daji sun kashe a ƙalla mutum 18 a wasu hare-hare da suka kai kan wasu ƙauyuka ranar Lahadi, a cewar rahotanni daga jihar Zamfara arewa maso yamma.

Wani kansilan mazaɓar Ɗankurmi, Hon Salisu Daraga ya ce maharan sun far wa ƙauyukan Matse-matsi da Katoge da Taɓanni da Matankari, inda suka kashe mutum goma.

"Kawai sai bandit suka fito musu, to a take dai suka kashe mutum goma," in ji shi.

A jihar Neja maƙwabtaka ma, mazauna wasu ƙauyuka na ƙaraamar hukumar Rijau na ci gaba da tsere wa gidajensu, bayan wani harin ‘yan fashi, abin da ya kai ga sace kimanin mutum 50.

Wasu ‘yan bijilante a Rijau, sun ce cikin waɗanda ‘yan bindigar suka tafi da su, har da mata da ƙananan yara.

Haka kuma rahotanni na cewa an sace Mallam Abdullahi Zaure, wani dagaci a yankin.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun ya ce jami'ansu na tattara bayanai a kan hare-haren na Rijau, kafin fitar da cikakken ƙarin haske.

Kansilan Ɗankurmi dai ya ce 'yan fashin sun kuma tare hanyar Ɗankurmi inda suka kashe mutum takwas, waɗanda tuni aka yi jana'izar su a garin Ɗankurmi.

Ya kuma ce maharan sun raunata a ƙalla mutum 30.

Tun ranar Laraba suke kai hari Rijau

Wani ɗan bijilante da ya nemi kada a ambaci sunansa ya shaida wa BBC cewa 'yan bindiga sun far wa ƙauyuka kamar Jama’are da Shammo da Jama'are da Rafin Mota Dugge da Mariri da Homo Jama’are.

"Daga Jama'aren ne suka wuce makarantar 'yan mata ta tsohon garin Rijau wato Rafin Mota, inda suka kashe mutum biyu. Gaskiya, yawansu zai kai 800 zuwa 1,000 a kan babura," in ji jami'an tsaron yankin.

A cewarsa, suna satar duk waɗanda suka ga dama su sata, sannan sukan gamu da wasu, su yi musu fashi, amma su bar su, su wuce.

"Sun kwashi shanaye, sun kwashi dukiyar mutane, sun faffasa shaguna. Sun sace wani sarki, ana ce da shi sarkin Dugge".

Ya dai yi zargin cewa 'yan fashin dajin sun yi wa wata yarinya fyaɗe har sai da ta mutu.

Jami'in tsaron ya ce tun ranar Laraba suka fara kai harin har zuwa ranar Asabar da ta wuce.

A cewarsa, sai a daren Asabar ne jami'an tsaro suka isa yankin.

Ya ce jami'an tsaro sun yi nasarar fatattakar 'yan fashin, "saboda har mashinoninsu, sun kama mashin ɗinsu kusan guda sittin".

Jami'in tsaron ya ce hankula sun tashi a tsakanin mutanen ƙauyukan, abin da ya sanya suka tsere wa gidajensu zuwa garin Rijau. "Sun dawo sun cika garin Rijau, sun maida Rijau kamar kasuwa".

Mata duk tsere wa ƙauyuka

Kansilan Ɗankurmi ya ce maharan sun fara kai farmaki tun misalin ƙarfe 10 na safe har zuwa ƙarfe 3 na ranar Lahadi.

Ya ce an kai mutum tara da suka ji raunuka zuwa wani asibitin kuɗi da ke Ɗankurmi.

"Akwai asibitin gwamnati, inda muke da mutum goma. Sannan akwai mutum bakwai waɗanda harbin nasu ya yi nauyi, an wuce da su babban asibiti da ke jihar Kebbi, wanda ke Bena da Wasagu".

A cewar Hon Salisu Daraga, 'yan fashin sun ci karensu babu babbaka sun tafi, kafin zuwan jami'an tsaro yankin.

Ya ce mafi yawan matan da ke cikin ƙauyukan Taɓanni da Katoge da Jan ƙarfi da Matse-matsi da Ɗan kaɗe sun yi gudun hijira, saboda matsin lambar 'yan fashi.

"Ga su nan Ɗankurmi duka sun yo gudun hijira. Akwai Katoge, ita Katoge, ina tabbatar maka cewa sun kasa garin kashi uku, sun ƙone guda."