You are here: HomeAfricaBBC2023 05 25Article 1773893

BBC Hausa of Thursday, 25 May 2023

Source: BBC

'Yan Real Madrid da ke jinya kafin wasa da Sevilla ranar Asabar a La Liga

Vinicius Jnr tare da Karim Benzema Vinicius Jnr tare da Karim Benzema

Real Madrid da Sevilla za su buga wasan mako na 37 a gasar La Liga ranar Asabar 27 ga watan Mayu.

Kungiyoyin sun fara karawa ranar 22 ga watan Oktoba a Santiago Bernabeu, inda Real ta yi nasara da cin 3-1.

Wadanda suka ci mata kwallyen sun hada da Luka Modric da Lucas Vazquez da kuma Federico Valverde.

Ita kuwa Sevilla ta zare kwallo daya ta hannun Erik Lamela.

Real Madrid na fatan cin wasa biyu a jere, inda za ta kara da Sevilla wadda za ta buga fafatawar karshe a Europa League a kakar nan.

Kungiyar Santiago Bernabeu ta koma kan ganiya da cin Rayo Vallecano ranar Laraba, bayan da ta yi rashin nasara a gidan Valencia 1-0 ranar Lahadi.

Kawo yanzu kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama tana ta biyu a kan teburin La Liga da maki 74 da tazarar maki daya tsakaninta da Atletico ta uku mai maki 73.

Tuni dai Barcelona ta dauki La Liga na bana na 27 jimilla na farko tun bayan da Lionel Messi ya bar Camp Nou zuwa Paris St Germain da taka leda.

To sai tun kafin fuskantar Sevilla, Real tana fama da 'yan wasan da ke jinya da suka hada da Mariano Diaz da Vinicius Junior da kuma Karim Benzema.

Diaz, bai yi wa Real karawa biyu ba, wanda yarjejeniyarsa za ta karkare a karshen kakar nan.

Vinicius Junior bai buga wa Real wasa da Vallecano ranar Laraba ba, wanda aka soke jan katin da aka yi masa a gidan Valencia ranar Lahadi a La Liga.

Shi kuwa Karim Benzema ya ji rauni ranar Laraba a wasan Vallecano, wanda ake tantamar karawar ta ranar Asabar.

Sai dai a cikin makon nan likitocin Real Madrid za su tantance ko 'yan wasan za su iya buga mata wasan na babbar gasar tamaula ta Sifaniya.