You are here: HomeAfricaBBC2021 05 04Article 1250716

BBC Hausa of Tuesday, 4 May 2021

Source: BBC

'Yan PSG da suka je Man City buga Champions League

Neymar tare da Mbappe Neymar tare da Mbappe

Manchester City za ta karbi bakuncin Manchester City a wasa na biyu na daf da karshe a Champions League da za su fafata ranar Talata a Etihad.

A wasan farko da suka buga a Faransa ranar 28 ga watan Afirilu, City ce ta yi nasara da ci 2-1.

Wannan shi ne wasa na biyar da za su fafata a tsakaninsu a gasar Zakarun Turai, inda City ta yi nasara a biyu da canjaras biyu.

City wadda take ta daya a teburin Premier ta lashe Caraboa Cup na bana na hudu a jere kuma na takwas jumulla.

Paris St Germain tana ta biyu a kan teburin Ligue 1 da maki 75 da tazarar maki daya tsakaninta da Lille wadda ke jan ragama.

Wannan ne karon farko da Pep Guardiola ya kai wannan matakin a Champions League a Manchester City, wadda ba ta taba lashe kofin ba.

A bara PSG ta kai karawar karshe a Champions League, inda ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Bayern Munich.

'Yan wasan Paris St Germain:

  • BAKKER Mitchel


  • DAGBA Colin


  • DIALLO Abdou


  • DI MARIA Angel


  • DRAXLER Julian


  • FLORENZI Alessandro


  • GUEYE Idrissa (an dakatar da shi, amma an je da shi Faransa)


  • HERRERA Ander


  • ICARDI Mauro


  • KEAN Moise


  • KEHRER Thilo


  • KIMPEMBE Presnel


  • KURZAWA Layvin


  • MARQUINHOS


  • MBAPPÉ Kylian


  • NAVAS Keylor


  • NEYMAR JR


  • PAREDES Leandro


  • PEREIRA Danilo


  • RAFINHA


  • RANDRIAMAMY Mathyas


  • RICO Sergio


  • SAIDANI Yanis


  • SARABIA Pablo


  • VERRATTI Marco


  • Wadan da ke jinya:

    1. BERNAT Juan


    2. FRANCHI Denis


    3. GHARBI Ismael


    4. KAMARA Abdoulaye


    5. LETELLIER Alexandre


    6. MICHUT Edouard


    7. NAGERA Kenny


    8. PEMBÉLÉ Timothée


    9. SIMONS Xavi