You are here: HomeAfricaBBC2023 09 19Article 1847282

BBC Hausa of Tuesday, 19 September 2023

Source: BBC

'Yan Barca 12 da za su kara da Royal Antwerp a Champions

Yan wasan Barcelona a cikin murna Yan wasan Barcelona a cikin murna

Barcelona za ta karbi bakuncin Royal Antwerp a wasan farko a rukuni na takwas a Champions League da za su kara ranar Talata a Sifaniya.

Sauran kungiyoyin da suke rukuni tare da Barcelona a babbar gasar tamaula ta Zakarun Turai ta bana sun hada da FC Porto da Shakhtar Donesk.

Wannan shi ne wasa na uku da za a kara tsakanin kungiyoyin biyu

Kakar da suka yi wasan 1965/1966

Fairs Cup Laraba 1 ga watan Disambar 1965

  • Barcelona 2 - 0 Royal Antwerp


  • Fairs Cup Laraba 17 ga watan Nuwambar 1965

  • Royal Antwerp 2 - 1 Barcelona


  • Tuni dai kociyan Barcelona, Xavi Hernández ya bayyana 'yan wasa 21 da zai fuskanci Royal Antwerp da su.

    'Yan wasan Barcelona:

    Ter Stegen, Joao Cancelo, Balde, I. Martínez, Gavi, Ferran, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña, João Félix, Christensen da kuma Marcos A.

    Sauran sun hada da Romeu, S. Roberto, F. De Jong, Gündoğan, Kounde, Astralaga, Lamine Yamal, M. Casadó da kuma Fermín.