You are here: HomeAfricaBBC2023 11 14Article 1880978

BBC Hausa of Tuesday, 14 November 2023

Source: BBC

'Yan Arsenal 17 aka gayyata kasashensu domin buga wasanni

Yan wasan Arsenal Yan wasan Arsenal

'Yan wasan Arsenal 17 aka gayyata zuwa tawagoginsu, domin buga wa kasashensu ko dai wasan neman shiga gasar kofin duniya ko ta Euro 2024 ko na sada zumunta.

Wasu daga 'yan wasan har da Jakub Kiwior da Oleksandr Zinchenko da Jorginho da Alex Runarsson da Gabriel Martinelli da Gabriel Jesus.

Sauran sun hada da Aaron Ramsdale da Declan Rice da Bukayo Saka da Leandro Trossard da William Saliba da kuma Kai Havert.

Martin Odegaard ya hakura da buga wa Norway wasa, domin ya samu ya murmure sosai daga jinya da ya sha.

Ranar Juma'a dan wasa Jakub Kiwior zai buga wa Poland wasan da za ta kara a neman shiga gasar Euro 2024.

Ukraine ta gayyaci Oleksandr Zinchenko, haka ita ma Italiya ta kira Jorginho, domin buga karawar neman shiga Euro 2024.

Haka kuma Iceland ta gayyaci Alex Runarsson, domin fuskantar Slovakia da Portugal a wasannin neman shiga Euro 2024.

'Yan wasan Brazil da suka hada da Gabriel da Gabriel Martinelli da kuma Gabriel Jesus, suna cikin wadanda za su fuskanci Colombia da Argentina a wasan neman shiga gasar kofin duniya.

Aaron Ramsdale da Declan Rice da kuma Bukayo Saka, suna daga cikin 'yan kwallon da Ingila ta gayyata, domin buga mata wasa biyu a neman shiga Euro 2024.

Belgium ta kira Leandro Trossard don karawa da Azerbaijan a wasan shiga Euro 2024, wadda tuni ta samu gurbi, sannan za ta yi wasan sada zumunta da Serbia.

Haka kuma Fransa ta gayyaci William Saliba, domin buga mata wasa biyu da suka rage na nemna gurbin shiga Euro 2024.

Jamus ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Turai a 2024, hakan ya sa take buga wasannin sada zumunta ta kuma kira Kai Havert.