You are here: HomeAfricaBBC2023 07 17Article 1806434

BBC Hausa of Monday, 17 July 2023

Source: BBC

Yajin Aikin Jaruman Hollywood ya zamo tarnaƙi ga fina-finai

File foto File foto

Waɗanne fina-finai yajin aikin ya shafa?

Yajin Aikin Jaruman Hollywood wanda ya ƙunshi Marubuta da ƴan wasan kwaikwayo zai iya dakatar da samar da mafi yawan fina-finai da kuma shahararrun shirye-shiryen talabijin.

A watan Yulin shekara ta 1980 Ƙungiyar Ma`aikatan Telebijin da Rediyo da Wasannin Kwaikwayo (SAG-AFTRA) ta yi yajin aiki a Amurka.

A wancen lokacin an samu takaddama tsakanin mambobi da ƙwararru a fina-finan nishaɗi game da ribar da aka samu daga siyar da shirye-shirye da fina-finai da aka yi don talabijin kamar yadda jaridar New York Times a lokacin.

Bayan shekaru 43 sabon yajin aikin ya zo a lokacin da Kungiyar Marubuta fina-finai suke yajin aiki, bangarorin biyu sun baki ɗaya kan ƙyamar batun ƙirƙirarriyar basira.

Ƙungiyar Ma`aikatan Telebijin da Rediyo da Wasannin Kwaikwayo (SAG-AFTRA) ta shaidawa manema labarai cewar yajin aikin zai shafi fina-finai da shirye-shiryen da mambobinta su ka yi tun a shekara ta 2020.

Manyan fina-finan da su ka samu karɓuwa waɗanda kuma har yanzu ba a kammala ɗaukar su ba sun haɗa da Ghostbusters na 4 da Mufasa Lion King da Avatar na 3 da na 4.Database.

Akwai fina-finan da aka shirya fara yin su, amma hakan ba zai yiwu ba a yanzu kamar yadda masu shirya fina-fianan su ka sanar. Daga cikinsu akwai Paddington da Paddington in Peru.

Duk irin shiri da tanadin aka yi kafin wannan dambarwa, a yanzu ya zama tilas a dakata saboda ba za a samu Jarumai ba.

Daga cikin shirye-shiryen da aka yi a Burtaniya da abin ya shafa akwai Deadpool na 3 tare da jaruman fina-finan Hollywood irinsu Ryan Reynolds da Hugh Jackman, akwai kuma kashi na uku fim ɗin Marvel antihero amma yajin aikin na iya canza abubuwa yanzu.

Ƴan kallo na iya jira tsawon lokaci don sauran fina-finai masu kamar Beetlejuice sequel na Tim Burton.

Beetlejuice 2, wanda zai ƙare a watan Satumba na 2024, Jaruman fim ɗin su ne Michael Keaton da Winona Ryder da kuma Jenna Ortega, sun fara yin fim a Vermont wannan makon lokacin da aka sanar da yajin aikin.

An fara ɗaukar fim din wicked a Burtaniya, Jaruman fim ɗin su ne Ariana Grande da Cynthia Erivo, an yi tanadin fara fitowa da fim ɗin a shekara ta 2024.

Fina-finan da aka shirya a ƙasashen ƙetare irinsu Gladiator sequel mai Jarumai irinsu Paul Mescal da Denzel Washington, su ma abin ya shafe su.

Ana ɗaukar sabon fim din Gladiator a Ƙasashen Morocco da Malta to amma da dama daga cikin waɗanda su ke aikin shirya fim ɗin Ƴan Burtaniya ne.

Yajin aikin ya shafi talle-talle da bukukuwan girmamawa da fim ɗin matasa na Disney Haunted Mansion da Mutant Ninja Turtles da A Hunting In Venice waɗanda aka shirya fitowa da su a watan Satumba.

Ko Jaruman Birtaniya sun shiga Yajin Aikin?

Wannan yajin aiki dai bai shafi Ƙungiyar Equity ba, takwarar Ƙungiyar Ma`aikatan Telebijin da Rediyo da Wasannin Kwaikwayo (SAG-AFTRA) a Burtaniya.

Equity ta gargadi mambobinta cewar duk wanda ya shiga yajin aiki, ba za ta kare shi daga kora ko Shari`a ba.

Ko abin zai shafi shirye-shiryen Telebijin?

Dangane da shirye-shiryen Telebijin wanda Warner Bros Discovery suke ɗaukar nauyi akwai yiwuwar kulla yarjejeniya don ba da damar wasu ayyuka su ci gaba.

A cikin Amurka sauran shirye-shiryen telebijin da ake tsammanin za a samar a wannan bazara sun haɗa da Family Guy da Simpsons.

An riga an dakatar da aiki a kan wasu manyan shirye-shiryen kamar Stranger Things da Last of Us da Yellow jackets saboda yajin aikin marubuta.

Bukukuwan Emmy Awards da Toronto da kuma bukukuwan fina-finai na Venice suna iya ci gaba.

Me zai faru a gaba?

A shekara ta 1980, yayin yajin aikin ƴan wasan na karshe wanda aka kwashe makwaonni 10 ana yi an yi ƙiyasin asarar dala miliyan 370 a yau.

A shekara ta 1960 marubuta da ƴan wasan kwaikwayo sun gudanar da yajin aiki tare.

A yanzu dai sulhu zai iya yin wahala sakamakon kiraye-kirayen da Jarumai su ke yiwa ƙungiyoyinsu da su tsaurara dalilan tafiya yajin aikin.

A nasu ɓangaren ma`aikatan Hollywood sun bayyana takaicin kan Ƙungiyar Ma`aikatan Telebijin da Rediyo da Wasannin Kwaikwayo (SAG-AFTRA) wacce su ka ce ta ci zarafin tarihi.

Ƙungiyar dai ta yi nadamar zabin hanyar da za ta haifar da matsalar kudi ga dubban mutanen da suka dogara da masana'antar.