You are here: HomeAfricaBBC2021 03 17Article 1206811

BBC Hausa of Wednesday, 17 March 2021

Source: www.bbc.com

Yadda za a kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga a yankin Sahel

Wasu jerin hare-hare da ƴan bindiga suka kai yankin yankin Banibangou na jahar Tillabery a jamhuriyar Nijar sun yi sanadin aƙalla rayukan mutum 58 kamar yadda sanarwar gwamnatin kasar ta ambato.

Maharan dai sun kai hare-haren ne kan motocin fasinja kuma tuni gwamnati ta yi tir da faruwar lamarin.

A halin da ake ciki, gwamnati ta ayyana zaman makoki na kwanaki 3 a fadin kasar.

Amma masana harkokin tsaro na ganin akwai hanyoyi da dama da za a bi domin fitar da yankin Sahel daga hare-haren ƴan bindiga masu iƙirarin jihadi da ke ci gaba da ƙaruwa.

Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a Najeriya da yankin Sahel ya ce haɗin kai tsakanin ƙasashen da ke fama da wannan matsala zai taka rawa wajen kawo maslaha.

A cewarsa kusan duka yankin Sahel na fama da wannan matsala, "a Nijar inda abin ya banbanta, tana tsaka mai wuya ne, ta yamma akwai ƙasashe irinsu Mali da Libya waɗanda dukkansu suna da matsalar tsaro da ke da nasaba da ƴan bindiga, ta Gabas ta ɓangaren Najeriya akwai matsalar Ƙungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad da Ƙungiyar ISWAP".

Dalilin da ya sa ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare

Dakta Kabiru Adamu ya ce a ganinsa, abin da ya sa ake samun ƙaruwar hare-hare a Nijar duk da irin matakan da ake ɗauka shi ne girman iyaka da ƙasar take da shi da rauni na tattalin arziki da sauran matsaloli da suke zama silar samun ta'addanci a ƙasa irinsu talauci da rashin ilimi da yawan ƴan kasa da ba su da ayyukan yi.

Ya bayyana cewa akwai matsaloli da dama da suke da nasaba da hakan - "akwai horon da jami'an tsaro suke da shi, akwai matsala wadda ita gwamnatin take da shi na tabbatar da iko a wuraren".

Masanin ya ƙara da cewa ƙasashen da suke aikin samar da tsaro a Nijar kamar Faransa da Amurka suna da wata manufa da suke karewa.

Mafita

A cewar Dakta Kabiru Adamu haɗin kai tsakanin ƙasashen yankin wurin tabbatar da kare iyakokinta, hakan zai rage matsalar ƴan bindiga da ke kai hare-hare.

Ya kuma ce idan har aka samu nasarar ƙwace makamai a hannun masu ta'annatin, hakan zai taimaka sosai wajen kaso sauƙi a yawan hare-haren da ƴan bindigar ke kaiwa.

"Ya kamata Nijar ita ma ta shiga yunƙuri da duniya da sauran ƙasashen ECOWAS da AU suke yi na ƙwace makaman don kusan duk ɓarnar da za a yi da waɗan nan makaman ake yi"

Join our Newsletter