You are here: HomeAfricaBBC2023 01 18Article 1697651

BBC Hausa of Wednesday, 18 January 2023

Source: BBC

Yadda 'yan siyasa ke ba wa masu fada a ji a shafukan sada zumunta kudi don ɓata abokan hamayya

Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar plus Peter Obi (middle) Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar plus Peter Obi (middle)

Wani binciken BBC ya gano cewa jam'iyyun siyasa a Najeriya na ba wa masu fada a ji a shafukan sada zumunta kudi a boye domin su yada bayanan karya a kan abokan takararsu gabanin zabukan da ke tafe.

Tawagar sashen yada bayanan karya na BBC ta tattauna da masu kwarmata bayanai da ke yi wa wasu jam'iyyun siyasa biyu aiki da kuma masu fada a ji a kafafen sada zumunta.

Masu kwarmata bayanan sun ce jam'iyyun siyasar na ba su kudi da kyautuka da kwangilolin da kuma wani lokaci mukamin siyasa don su yi musu aiki.

BBC ta sakaya sunan wadannan mutane saboda dalilai na tsaro.

"Yemi" fitacciya ce mai kuma dabaru yayin da "Godiya" kuma 'yar siya ce.

Godiya ta ce," Muna ba wa masu fada aji a shafukan sada zumunta kudi har dala 45, wato kwatankwacin naira miliyan 20 don yi mana aiki.Sannan mu kan ba su kyautuka. Wasu kuwa kan so a tambaye su me suke so a gwamnati? mukami ko kuma me?

Cibiyoyin tattara bayanai ba sabbin abubuwa ba ne a lokacin zabe.

A nan ne jam'iyyun siyasa ke dukkan kulle-kulle da tsare-tsare da kuma duba yadda yakin neman zabensu ya samu nasara.

To amma a wannan daki, masu kwarmata bayanai sun bayyana mana cewa wasu abubuwa da ake yi.

Yemi fitacciya ce kuma mai dabaru, ta ce anan ne ake kirkirar labaran karya don wasa dan takara.

Su kuwa masu kwarmata bayanai sun ce anan ne ake ba wa masu fada aji a kafafan sada zumunta ayyukan da za su yi don ko da dan takara da kuma ba su kudi don yin wannan aiki.

Yemi ta ce ana kirkirar labaran karya don wasa dan takara wani lokaci ma har da bayar da bayanai na karya a kansa wanda babu shi.

BBC ta tattauna da masu fada aji a kafafan sada zumunta da suka tabbatar cewa ana biyansu kudade don wallafa labaran karya da ake yadawa.

Daya daga cikinsu da ya nemi a sakaya sunansa da ke da masu bibiyarsa a shafin Facebook dubu 150, ya shaida wa BBC cewa, an ba shi kudi don ya wallafa labarin karya a kan abokan takara.

A bangare guda kuma, Rabi'u Biyora, fitacce ne kuma mai fada aji a shafin zumunta wanda kuma ke goyon bayan jam'iyyar APC ya shaida cewa jam'iyyar adawa ta bukace shi da ya daina goyon bayan APC, ya koma goyon bayan dan takararta.

Ya wallafa a shafinsa a Facebook, inda ya tabbatar da hakan.

Ya shaida mana cewa ba a ba shi komai ba.

To amma mun gano wani abu da ya wallafa a 2019, inda ya ce ya karbi kyautar mota da kudi daga jam'iyyar da ya koma saboda abin da ya yi.

Mun fada masa haka amma sai ya daina ce mana komai.

Dabaru

Kiyasi ya nuna cewa akwai 'yan Najeriya miliyan 80 da ke amfani da kafafan sada zumunta, kuma suna taka muhimmiyar rawa a muhawar da ake yi a kan siyasa a kasar.

Bincikenmu ya gano ana amfani da dabaru da dama wajen kaiwa ga mutane a shafin Twitter.

Wasu kan yi amfani da abubuwa da suka hadar da na addini ko al'ada.

A watan Yuli, masu fada a ji a shafukan sada zumunta sun yada wasu bayanai da suka shafi dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar APC, Kashim Shettima da kuma 'yan Boko Haram.

Wannan labari na karya an bibiyeshi a shafin Twitter har ma aka yada shi sauran shafukan sada zumunta kamar WhatsApp.

Da BBC ta bibiyi hotunan da aka yadan na Kashim Shettima da 'yan Boko Haram din, an gano cewa wadannan mutanen ba wasu ba ne illa fulani makiyaya iyaye da 'ya'yansu, ba 'yan Boko Haram ba ne.

Bayan wata guda, irin wadannan mutane da ke fada a ji a shafukan sada zumunta suka kara wallafa labarin da ba shi da tushe cewa Dan takarar shugaban kasa a Jam'iyyar Labour, Peter Obi, na da alaka da 'yan kungiyar IPOB, to amma jam'iyyarsa ta musanta.

Daga cikin wadanda suka yada wannan labarin har da Reno Omokiri, mai bayar da shawara ga tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda ke da mabiya miliyan biyu a Twitter.

Ko da aka tuntube shi, Reno Omokri, ya ce ya yarda da zarge-zargen da ya yi, to amma ya hakikance ba wanda ya ba shi kudi ko wata kyauta don ya wallafa bayanin.

Kazalika, an sha wallafa labarin an garzaya da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar zuwa asibiti a kasar waje a shafin Twitrer wanda kuma karya ne.

'Yar siyasa Godiya, ta ce jam'iyyun siyasa na fada wa masu fada a ji a shafukan sada zumunta cewa su kirkiri labaran karya ciki har da na ban tausayi su yada saboda a biya su.

Ta ce, " Mukan yi amfani da hotunan da ba su da alaka da labari idan muna so mu taba wani".

A cewar masu kwarmata bayanai, masu fada a ji a shafukan sada zumuntar da ake haya, a wasu lokutan akan ba su satar amsa a kan kalmomin da za su yi amfani da su wajen bata mutum.

Sun ce ana biyan irin wadannan mutanen ne da tsabar kudi don gudun samun wata matsala.

Ba laifi ba ne ga jam'iyyun siyasa su yi hayar masu fada a ji a kafafan sada zumunta a Najeriya, to amma yada bayanan karya shi ne ya saba wa dokokin kasa na Twitter.

BBC ta tambayi manyan jam'iyyun siyasar Najeriya da suka hada da APC da PDP da kuma Labour, a kan zarge-zargen da ake yi wa masu kwarmata bayani.

Ba suce komai ba a kai.

Sakamakon binciken da muka yi, Twitter ta goge wasu daga cikin shafukan da muka yi korafi kansu inda Twitter din ya ce yana da alhakin kare batutuwan siyasa daga kutse da juya zance da watsa labaran karya.

Sakamakon binciken da muka yi, Twitter ta goge wasu daga cikin shafukan da muka yi korafi kansu inda Twitter din ya ce yana da alhakin kare batutuwan siyasa daga kutse da juya zance da watsa labaran karya.

Akwai damuwa a game da yadda za a magance yada bayanan karya a Afirka bayan Elon Musk ya sayi kamfanin.

 BBC ta tuntubi Twitter a kan sauye-sauyen da aka samu a kamfanin, amma ba su ce komai ba.