You are here: HomeAfricaBBC2023 07 28Article 1814189

BBC Hausa of Friday, 28 July 2023

Source: BBC

'Yadda 'yan bindiga suka sace mana zawarawa da 'yan mata 23 a Zamfara'

Hoton alama Hoton alama

A tsakiyar makon nan ne, wasu 'yan bindiga suka sace zawarawa da 'yan mata da ƙananan yara, wadanda yawansu ya kai 23, a yankin Ƙaramar Hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

A ranar Laraba ne lamarin ya faru, amma nisa da rashin samun yadda bayanai za su fita ya sa ba a ji labarin sace matan ba sai a jiya Alhamis.

Mazauna yankin Muradun na kukan cewa ayyukan 'yan fashin daji da ake ta yaɗa cewa sun ragu "ba haka abin yake ba" kawai dai ji ne ba a yi.

Wani magidanci da BBC ta zanta da shi da ya nemi a ɓoye sunansa saboda tsaro, ya ce "matan sun fita bayan gari ne yin itace suka ci karo da 'yan bindigar.

"Duk safiya suna tafiya daji yin itace, a wannan karon tawaga ce ta zawarawa da 'yan mata da matan da mazajensu suka mutu da kuma ƙananan yara abin ya rutsa da su.

"Da wannan itacen da suke yi, da shi suke samu su ci abinci," in ji wannan magidanci.

Ya ce suna zuwa ko da yaushe, amma a wannan karon ne rana ta ɓaci gare su.

"Tawagar matan tana da yawa amma ya zuwa yanzu mun tabbatar da cewa babu 23 cikinsu.

"Su ma maharan suna da matuƙar yawa ne, ga makamai. To kuma waɗannan mata ne ba za su iya gaba da gaba da su ba.

"Sun yi amannar maharan ba su da kau da kai za su iya kashe su, shi yasa ba su yi masu tunjiya ba," in ji wannan bawan Allah.

Mutumin ya ce har yanzu babu su babu amonsu. Kuma su ma waɗanda suka sace su ba su neme mu ba balle mu san halin da suke ciki.

Cikin baƙin ciki da damuwa mutumin ya ce ido na ganin ido aka sace waɗannan mata, domin lokacin da abin ya faru bai wuce ƙarfe 11:30 safe ba.

Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da rashin tsaro matuƙa gaya.