You are here: HomeAfricaBBC2023 02 06Article 1709315

BBC Hausa of Monday, 6 February 2023

Source: BBC

Yadda 'yan bindiga suka kashe 'yan sintiri fiye da 100 a Katsina

Hoton alama Hoton alama

Akalla 'yan sintiri 71 ne aka yi jana'izarsu a karshen mako sannan kuma ana ci gaba da neman karin wasu fiye da 70 da aka hikkake su ma sun mutu a harin 'yan bindiga a Katsina.

'Yan sintitin sun rasa rayukansu ne a wani dauki ba dadi tsakaninsu da 'yan bindiga a dajin 'Yargoje da ke yankin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa "an kwashe fiye da awa 48 ana wannan artabu tsakanin bangarorin guda biyu".

Al'amarin dai ya shafi mazauna kauyukan da ke kusa da dajin na 'Yargoje wanda kuma ya hada kananan hukumomin Bakori da Kankara da kuma Malumfashi a jihar ta Katsina.

A yankin Jargaba na Malumfashi ma an yi jana'izar mutum fiye da 10 sakamakon wannan artabu.

'Kwantan ɓauna'

'Yan sintirin da aka kashe dai sun bi sahun wasu shanu da barayin daji suka sace, inda 'yan bindigar suka yi musu kwantan ɓauna.

"Su barayin na dauke da manyan bindigogi amma, yan sintiri na dauke da bindigogin toka da sauransu. Shi yasa suka samu nasara akan ‘yan sintirin."

Sai dai al'ummar yankunan sun ce sun nemi dauki amma ba su ga kowa ba.

Tuni Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alla-wadai da wannan hari na dajin.

Dajin na 'Yargoje ya zamo mafaka ga barayin daji da ke barazana ga yankin da ake kira Katsina ta Kudu.

Yankin Katsina ta Kudu dai ya hada da kananan hukumomin Bakori da Malumfashi da Kafur da Kankara da Faskari da ma Funtua.