You are here: HomeAfricaBBC2023 07 05Article 1798604

BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

Source: BBC

Yadda wata ɗaliba ta ƙara wa kanta maki a JAMB

Kungiyar jarrabawar shiga jami'a ta JAMB Kungiyar jarrabawar shiga jami'a ta JAMB

Masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi a Najeriya sun bayyana cewa labarin ɗalibar nan da ake zargi da yin runto game da sakamakon jarrabawar shiga jami'a ta JAMB a Najeriya ba abin mamaki ba ne.

Ɗaliba mai suna Ejikeme Mmesoma daga Jihar Anambra ta sanar da cewa ta samu maki 362 a jarrabawar da ta zauna a bana, wanda ya sa kamfanin ƙera motoci na Innoson Motors ya ba ta tallafin karatu na naira miliyan uku.

Sai dai hukumar Joint Addmission and Matriculatiomn Board (JAMB) da ke shirya jarrabawar ta shiga manyan makarantu ta musanta iƙirarin ɗalibar, tana mai cewa sakamakon boge ta ƙirƙira don yaudarar al'umma.

"Miss Ejikeme Joy Mmesoma, maki 249 ta samu, ba 362 ba kamar yadda ta yi iƙirari," a cewar Fabian Benjamin mai magana da yawun hukumar, cikin wata sanarwa.

Ya ƙara da cewa ɗalibai da dama na amfani da fasahar zamani wajen shirya sakamako na ƙashin kansu, kuma ya shawarci al'umma da "su dinga tuntuɓar hukumar kafin girmama irin waɗannan ɗalibai".

Jami'o'i da kwalejoji a Najeriya sun sha korar ɗalibai sakamakon kama su da laifin gabatar da sakamakon jarrabawa na boge, lamarin da wasunsu suka ce ba sabon abu ba ne.

Rahotanni sun ce asirin Ejikeme ya tonu ne lokacin da gwamnatin Jihar Anambra ke shirin girmama ta, inda a lokacin ne wani jami'i ya kira hukumar don tabbatar da sahihancin sakamakon nata.

JAMB ta ce za ta ƙwace jarrabawar tata sannan kuma ta gabatar da ita a gaban kotu.

Bugu da ƙari, hukumar ta tabbatar da cewa ba wannan ne karon farko da ta kama masu ƙirƙirar sakamakon boge ba a jarrabawar da ake yi duk shekara.

"Irin wannan ta faru da wani mai suna Atung Gerald a Kaduna, wanda ya yi iƙirarin cin maki 380. 'Yan ƙabilarsa sun yi ta kuruwar a girmama shi kafin daga baya hukumar ta gabatar musu da hujjar cewa Atung bai yi rajistar JAMB ta 2023 ba balle ma rubuta jarrabawar."

Duk shekara akan samu ɗalibai aƙalla miliyan ɗaya da ke rubuta jarrabawar, inda miliyan 1.45 suka zauna a 2022 daga cikin 1.7 da suka yi rajista.

Mun samu lambar yabo kan gano sakamakon boge - BUK

Hukumomin Jami'ar Bayero ta Kano (BUK) na ganin wannan lamari ya kwana biyu yana damun jami'o'i, inda har lambar yabo aka bai wa jami'ar daga hukumar JAMB a 2022 game da yadda suke tunkarar lamarin.

"Babu wani abin mamaki saboda ɗaliban yanzu na yin abubuwa da yawa don su samu ɗaukaka, rashawa ta yi wa abin katutu," kamar yadda mai magana da yawun BUK Lamara Garba Azare ya faɗa wa BBC Hausa.

Duk da ya ce lamarin da sauƙi a BUK, JAMB ta kira shugaban makarantar kuma ta girmama shi a madadin jami'ar da zimmar sauran jami'o'i za su yi koyi da ita.

Shahararren farfesa na tsangayar sadarwa a BUK, Abdallah Uba Adamu, ya tuna labarin wani ɗalibi da ya zauna jiran a kafe sakamako kafin ya tafi gida hutu.

"Bayan an kafe sakamako, sai ya ga an ce an dakatar da nasa sakamakon. Da ya je domin jin bahasi sai aka shaida masa cewa an bincika an gano cewa bai ci jarrabawarsa ta sakandare ba," in ji farfesan.

Ya ƙara da cewa abin da ya faru da Miss Ejikeme ba zai shafi martaba da kimar JAMB ba "saboda a ko'ina a duniya ɗalibai na satar jarrabawa, inda ake kama wasu kuma wasu na tsallakewa".