You are here: HomeAfricaBBC2023 02 09Article 1711406

BBC Hausa of Thursday, 9 February 2023

Source: BBC

Yadda wani matashi ya yi kokarin halaka kansa bayan an zare kudin asusun ajiyarsa na banki

Jihar Kana na yammacin Najeriya Jihar Kana na yammacin Najeriya

Jamai'an hukumar kashe gobara ta jihar Kano sun ceto wani mutum mai shekara 27 daga saman wani dogon karfen watsa shirye hirye na gidan talabijin na ARTV da ke birnin Kano.

Rahotanni daga Kanon sun ce mutumin ya dauki matakin hawa karfen ne domin ya rasa inda zai saka kansa bayan da wasu kudade da yawansu ya kai naira 500,000 suka bace daga asusun ajiyarsa na banki.

Saminu Yusuf Abdullahi shi ne kakakin hukumar kashe gobara a Kano, ya shaida wa BBC cea mutumin ya so kashe kansa ne a dalilin bacewar kudin da wasu suka tura masa domin wasu bukatu.

"Da misalin karfe 2:30 na ranar Laraba, an kira jami'anmu na hukumar kashe gobara zuwa gidan talabijin na ARTV inda suka tarar da wani matashi mai suna Saifullahi Yahaya Abubakar a saman dogon karfen yada labarai na tashar talabijin din. Da kansa ya hau, kuma yake da'awar zai fado daga saman karfen kuma a sanadin haka zai rasa ransa."

Daga nan ne jami'an kashe gobarar suka fara kokarin ba mutumin baki domin ya sauko daga saman karfen.

Kakakin hukumar kashe gobarar ya ce, "Bayan da suka same shi, sai suka fara magana da shi, inda sanar da su abubuwan da suka tilasta masa daukar wannan matakin".

'An zare min kudi a asusun ajiyana na banki'

Matashin ya shaida wa jami'an da suka isa wurin domin ceto shi cewa akwai naira 500,000 da aka tura masa daga wani asusun ajiya na bankin Access zuwa asusun bankinsa na Ecobank.

"Ya sami sakon shigar kudaden, amma daga baya da yaje cirar kudin a bankin nasa, sai ya ga babu kudin a asusun nasa", inji Saminu Yusuf.

Wannan mawuyacin halin da matashin ya shiga ya sa ya fada cikin dimuwa da matsananciyar damuwa, lamarin da yasa ya yanke shawarar kashe kansa, kamar yadda rahotannin kafafafen yada labarai a Kano suka tabbatar.

Bayan da jami'an da suke kokarin ceto ran matashin suka fahimci lalamar da suke masa ba zai sa ya sauko ba, sai suka rika jan hankalinsa yayin da wasu abokan aikinsu suka hau karfen sannu a hanakali har suka kai inda yake a saman karfen.

"Sun sami damar yi masa nasiha, wadda ta ratsa shi har ya amince ya fara sauko wa. Amma bayan sun kusa kai wa kasa, sai ya sauya ra'ayinsa, inda yayi kokarin komawa saman karfen", inji kakakin hukumar kashe gobarar.

Jami'an su yi dabara, kuma sun toshe hanyarsa ta komawa saman karfen", wanda a akrshe ya amince ya sauko kasa.

Bayan matashin ya sauko, jami'an hukumar kashe gobarar da suka taimaka ya sauko sun tafi da shi ofishin 'yan sanda da ke Bompai inda aka mika shi ga babban jami'in 'yan sanda wato DPO na Hotoro domin su ci gaba da bincike kan lamarin.