You are here: HomeAfricaBBC2023 07 24Article 1811150

BBC Hausa of Monday, 24 July 2023

Source: BBC

'Yadda na haihu a hanya domin tsira da raina'

Hoton mama da yar ta Hoton mama da yar ta

Bayan kashe mata yara uku, wata mai gabatar da shirin rediyo da ke ɗauke da juna-biyu ta tsere wa yakin da ake yi a yankin Darfur a ƙasar Sudan tare da yin tafiyar kafa - inda ta haifi ɗa namiji a kan iyakar ƙasar da Chadi.

"Na haihu a kan hanya. Babu ungozoma ko wani a kusa da zai taimake ni. Kowa na tunanin kansa. Kowa na gudu domin tsira da ransa.

"Bayan da na haihu, sai na nemi wani abu na lulluɓe yaron. Ban yi tunanin komai ba. Na ci gaba da tafiya zuwa Adré," in ji Arafa Adoum, lokacin da na same ta a wani sansanin ƴan gudun hijira wanda ya zamo masauki ga dubun-dubatar jama'a a wajen wani gari da ke Chadi.

Matar mai shekara 38 ta ce ta yi tafiya cikin zafin rana na tsawon kilomita 25 daga mahaifarta, El Geneina tare da 'ya'yanta guda huɗu, yayin da mijinta kuma ya bi ta wata hanya mai hatsarin gaske kafin ya isa sansanin.

"Lokacin da na isa kan iyaka na shiga cikin ɗimuwa har sai da na samu na haihu," in ji Mrs Adoum, inda ta ce ta saka wa yaron suna Mohamed wanda sunan Manzon Allah ne.

Ta bar gawarwakin sauran yaranta ba tare da an binne su ba - waɗanda suka haɗa da mai shekara uku da bakwai da kuma shekara tara - inda ta ce dakarun RSF ne tare da ƙawayensu mayaka na kabilar Larabawa suka kashe su a yaƙi da ake gwabzawa a Sudan tun watan Afrilu.

Darfur ya kasance yankin da rikicin ya fi shafa, inda aka zargi dakarun RSF da wasu mayaka da ƙoƙarin assasa iko na Larabawa a yankin ta hanyar kawar da duka bakaken fata ƴan Afrika - ciki har da waɗanda suka fito daga al'ummar Massalit da Mrs Adoum take.

Ba abin mamaki ba ne kan ƙoƙarin iko da birnin El Geneina - wanda a tarihi ya kasance wurin da bakaken fata ƴan Afrika suka fi iko a Darfur.

"Mun yi ƙoƙarin kare kanmu, sai dai suna amfani da manyan makamai," in ji Sheikh Mohammed Yagoub, wani malamin addini mai faɗa a ji kuma shugaban al'ummar ƴan Massalit, wanda shi ma ya zama ɗan gudun hijira a garin Adré.

"Akwai wata rana da muka yi asarar mutane 82 a cikin sa'o'i uku," in ji malamin.

Dakarun RSF sun musanta hannu a rikicin, inda suka ce Darfur na fuskantar dawowar daɗaɗɗen rikici ne tsakanin kungiyoyin Larabawa da kuma ƴan Massalit.

Da take bayyana labarinta, Mrs Adoum ta ce an kashe mata yara guda uku a jami'ar birnin El Geneina - inda suka samu mafaka - bayan da dakarun RSF da ƴan tawayen Janjawee suka yi wa garin ruwan makamai.

"Harbin makamai ne ya shafi yaran, abin da kuma ya janyo mutuwarsu," in ji Mrs Adoum.

An kuma kashe wasu ƴan uwanta da dama, ciki har da surukinta wanda aka cire wa kafafu da yanke kunnensa ɗaya, inda daga bisani aka harbe shi har lahira.

Daga nan sai Mrs Adoum da mijinta suka gudu da ’ya’yansu mata guda hudu, amma sai ya dawo ya bi wasu hanyoyi don kauce wa shingayen da jami’an tsaron RSF suka yi – saboda suna kashe maza da yara na Massalit, ta hanyar zuba musu fetur da kuma cinna musu wuta.

Ma'auratan sun sake haɗuwa a sansanin, inda mijin ya ga ɗansa Mohamed a karon farko - wanɗa suke gani a matsayin albarka bayan rasa yaransu guda uku.

Matar Sheikh Mohammed, Rakiya Adum Abdelkarim, ta faɗa min cewa ta rasa juna biyun da take ɗauke da shi, kwana guda bayan isar ta garin Adré a kafa - inda ta galabaita saboda yunwa da ta yi fama da ita a kan hanya.

"Nan da nan na fara naƙuda. Daga nan kuma na fara jin ciwon kai, inda jini ya yi ta zuba. Da asuba na rasa cikin da nake ɗauke da shi," in ji ta.

Wata kungiya mai zaman kanta ta kafa wani asibiti a garin Adré, sai dai Mrs Abdelkarim ba ta samu kaiwa wurin ba domin samun kulawa.

Asibitin na cike da marasa lafiya - musamman ma mata da ƙananan yara, waɗanda yawanci ke ɗauke da raunukan bindiga.

Ɗaya daga cikin marasa lafiyan, Naima Ali, ta ce dakarun RSF sun harbe ta ita da ɗanta mai wata tara a lokacin da suke tserewa daga ƙauyensu.

"Yaron yana bayana lokacin da harbin bindiga ya same shi a kafa, ni kuma a gefe kusa da ciki na," in ji Naima.

Ta ce sun yi ta zubar da jini, amma babu wani a kusa da zai taimake su.

Labaransu marasa daɗi na zuwa ne yayin da ƙasashen gabashin Afrika guda huɗu ke ƙoƙarin ganin an tura dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa Sudan, inda shugaba William Ruto na Kenya ke nuna damuwar cewa an lalata ƙasar da kuma cewa akwai alamun kisan kiyashi a Darfur.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na haɗakar Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Kungiyar Haɗin Kan Afrika, sun janye daga yankin Darfur a 2021, shekara 18 bayan mummunan rikici da yankin ya faɗa ciki, wanda ya janyo mutuwar mutane 300,000.

Rikicin ya jawo ce-ce-ku-ce a duniya, inda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC ta zargi shugaban ƙasar na wancan lokaci Omar al-Bashir da kisan kiyashi da aikata laifukan yaƙi da take ƴancin ɗan adam, abin da ya musanta.

A lokacin da dakarun suka janye, MDD ta ce an ɗauki matakin ne domin ɗora wa gwamnatin Sudan nauyin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Sai dai tun bayan janyewarsu, Sudan ta gamu da juyin mulki, abu kuma da ya jefa ta cikin yaƙin basasa a tsakiyar watan Afrilu bayan da manyan janar-janar ɗin ƙasar guda biyu - shugaban sojojin ƙasar Abdel Fattah al-Burhan da kwamandan dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti - suka raba gari.

Saɓani da ke tsakaninsu ya sake dawo da rikicin Darfur, da tilasta wa mutane 60,000 daga al'ummar Massalit tserewa zuwa Chadi.

Ba a dai san hakikanin yawan mutane da aka kashe ba a yankin, inda aka kiyasta cewa mutanen da aka kashe a birnin El Geneina sun kai 5,000.

A cewar wata kungiyar bayar da tallafin magunguna a Sudan, ta ce an binne gawarwaki 87 a wani wagegen rami a birnin, inda wasu ƴan gudun hijira suka faɗa wa BBC cewa sun ga gawawwaki da aka jefar a cikin kogi.

Dakarun na RSF sun saci abubuwa da dama a birnin Zalingei, da ya kasance gida ga al'ummar Fur da kuma yi wa manyan biranen yankin biyu Fasher da Nyala ƙawanya.

Da yawa daga cikin 'yan Darfur na fargabar wannan shi ne karshen shirin da aka daɗe ana yi na mayar da yankin da ke ɗauke da kabilu daban-daban zuwa wani yanki da ke karkashin Larabawa.

Sun ce an kori yawancin mazauna birnin El Geneina - tare da wasu garuruwa da kauyuka - tare da lalata gine-gine da ababen more rayuwa - ciki har da asibitoci da tashoshin ruwa.

"Abin da ke faruwa ya fi abin da ya faru a 2003," in ji shehin malamin, yana mai nuni da cewa an kashe fitattun mutanen Massalit - ciki har da likitoci da lauyoyi.

Ms Adoum - mai gabatar da shirye-shirye a gidan rediyon El Geneina - ta yi sa'a ta tsira, lokacin da RSF ta kai hari ofishin gidan rediyon a farkon yakin.

“Sun shiga suka farfasa duk kayan aikin kuma suka kwashe abin da za su iya,” in ji ta.

Yanzu Mrs Adoum na zaune ne a cikin wata bukka da aka gina da sanduna da tsumma, ba tare da sanin ko za ta iya komawa gida ba.

"Mun zo ne a matsayin 'yan gudun hijira. Mutane da yawa sun mutu a hanya. Amma dole ne mu ci gaba da tafiya," in ji ta, yayin da take riƙe da jaririnta mai mako uku a hannunta.

Wani ɗan gudun hijirar ya ce ba zai taɓa komawa El Geneina ba, yana mai cewa: "Wa zan koma wurinsa? Na shafe makonni a nan, kuma ko ta ina babu abin da kake gani a kan tituna El Geneina sai gawarwakin mutane."