You are here: HomeAfricaBBC2023 02 13Article 1713557

BBC Hausa of Monday, 13 February 2023

Source: BBC

Yadda matasa a Koriya Ta Kudu ke ado da takunkumi duk da wucewar Korona

Hoton alama Hoton alama

Koriya Ta Kudu ta yi watsi da mafi yawan dokokin da ta sanya na amfani da takunkumi, a matakan da riƙa ɗauka na sassaurta dokokin da ke da alaƙa da Korona.

A watan Mayun 2022 aka cire dokar sanya takunkumi a fili, amma an gabatar da riƙa amfani da su a cikin gida ko ɗakuna a watan Janairu, amma da wasu 'yan togaciya, ciki harda motocin haya da asibitoci.

Duk da haka da yawa daga cikin matasan Koriya Ta Kudu sun ce za su ci gaba da sanya takunkumin, ko a cikin wurare ko a waje, dalilinsu na haka kuma zai iya baka mamaki.

'Kyau da takunkumi'

A Koriya Ta Kudu, takunkumi ya zama wani babban abu lokacin annobar korona kamar dai yadda ayke a faɗin duniya. Nau'in KF94 ya fi zama ya karɗe ko ina.

Babu shakka kan cewa takunkumi ya kan hana a yi numfashi yadda ya kamata, akwai iyalan da kowa yana sanya takunkumi cikinsu ba yara ko manya.

Dalilan da ya sa ya yi shuhura a bayyane yake: mutane ba sa son kamuwa da ko su gogawa wani cutar.

Kimanin mutum miliyan 30 ne suka kamu da cutar korona a Koriya Ta Kudu kuma sama da 33,000 suka mutu sanadiyyarta.

An samu nasarwar ɗage sanya takunkumi a cikin ɗakuna shekara uku bayan samun wanda ya kamu da cutar na farko a kasar.

Amma matasa a ƙasar sun ce suna da dalilinsu na sanya takunkumi sama da wannan.

Shiga mai kyau na taka rawa tsakanin matasa, har cewa suke yi mutane suna matukar yin kyau idan suka sanya takunkumi, wani yare da suke yi a junansu na nuna ƙauna ga takunkumin a kafafen sada zumuntar ƙasar.

Kalmomi biyu ne ake haɗawa su tayar da ma'ana alfahari" da yaren Koriya.

Abin da hakan ke nufi, kana cewa wanda ya sanya takunkumin ya yi matuƙar kyau, kuma abin alfahari ne a wajensa.

Wani yaren da matasan ke amfani da shi, shi ne Maskfishing. Yawanci matasa ne da yara ke amfani da shi.

A Tiktok dubban bidiyo aka wallafa da hashtag na #maskfishing. Wani kalubale ne da matasa ke yi a tsakanins da suke cewa: "Ina da kyau da takunkumi?"

Wata 'yar koriya abin koyi da ke a tasiri, Hanna Kim, wadda ta lashe gasar mafi kyau ta Koriya a 202, ta shaida wa BBC itama hakan ta taɓa faruwa da ita lokacin da suka fita da wani namiji.

"Daga ƙarshe sai da na kira na ce masa ya yi hakuri, ba na zaton za mu ita tafiya tare," bayan da mutumin ya cire takunkuminsa taga bayi mata ba.

Sauyin yanayi na daga cikin abubuwan da suke sa a rika amfani da takunkumi.

Sai dai matasa da dama sun yi amannar lokaci kan sauya yadda ake amfani da abubuwa.

"Tun da ya ɗauki lokaci da yawa kafin mutane su fara amfani da takunkumi, dan haka zai dauki dogon lokaci kafin a daina amfani da shi, " ta kara da cewa.