You are here: HomeAfricaBBC2023 03 27Article 1738820

BBC Hausa of Monday, 27 March 2023

Source: BBC

Yadda matan Indiya suke amfani da allura domin kariya daga cin zarafi

Hoton alama Hoton alama

Kusan kowace mace a Indiya tana da labarin da za ta bayar na cin zarafin da ya faru a wajen taron mutane-Ko dai wani ya taba mata mama ko taba mata duwawunta, ko ya zunguri mamanta ko ya mata goge.

Domin kare kansu, matan suna amfani da duk wani abu da suka samu-misali, a matsayinmu na daliban kwaleji da muke yawan tafiya a motocin bas da suke cika da mutane a Gabashin birnin Kolkata a gomman shekarun da suka gabata, mukan yi amfani da lema ne.

Da yawanmu kuma mukan bar farcemu su yi tsawo da kaifi domin mu kyarce hannun wadanda ba sa ji; wasu sukan yi amfani da tsinin takalmansu su murje kafar mazan da suke amfani da taron mutane wajen goga al’aurarsu a bayan mata.

Amma wasu matan suna amfani ne da wani abun wanda ya fi wadannan-wato allura.

Tun lokacin da aka kirkiri allurar a shekarar 1849 mata suke amfani da ita a fadin duniya domin kama tufafinsu.

Amma kuma wasu matan suna amfani da allurar ce domin magance masu yunkurin cin zarafinsu ta hanyar tsira musu, wani lokacin har su zubar musu da jini.

A wasu watanni da suka gabata, wasu matan Indiya da dama sun bayyana a twitter cewa suna yawo da allurar a cikin jakunkunan hannunsu, kuma suna amfani da ita a matsayin makamin yaki da masu amfani da taron mutane domin cin zarafin mata.

Wata mai suna Deepika Shergill ta rubuta wani al’amari da ya faru da ita, inda ta cira wa wani allurar har jini ya fito. Ya faru ne a motar bas da take yawan shiga idan za ta je aiki, inji Mis Shergill a zantawarta da BBC. Lamarin ya faru a gomman shekaru da suka gabata, amma har yanzu ba ta manta ba.

A lokacin tana ’yar shekara 20 ne, shi kuma mutumin yana kimanin shekara 40, kuma yana yawan sanya kwat din safari (irin shigar da aka fi sani da ma’aikatan gwamnati a Indiya) da takalmin sandal, sannan yana yawan zuwa rike da jakar hannu.

“Yana yawan zuwa ya tsaya kusa da ni, ya dan kwanta a jikina, yana dan goga cinyarsa a bayana, sannan a duk lokacin da direban motar ya taka birki, sai ya kwanto a jikina.”

A wadannan kwanakin, a cewarta ta kasancewa, “cikin fargaba kuma ba ta so ta jawo hankalin mutane,” wanda hakan ya sa ta rika shiga damuna ita kadai.

Amma watarana, lokacin da, “ya fara wasa da gabansa da hannu har maniyyinsa ya zuba a kafadata,” sai ta yanke shawarar kawo karshen lamarin.

“Sai na ga ai ya ci zarafina ne. Ina zuwa gida, sai na shiga wanka na dade ina wanke jikina. Ban ma ko fada wa mahaifiyata abin da ya faru da ni ba,” inji ta.

“A wannan daren, sai na kasa barci har na fara tunanin ko in daina zuwa aiki ne, amma sai na fara tunanin yadda zan rama. Burina shi ne in masa wani rauni a jikinsa da zai ji zafi domin in hana shi sake tunanin yi min haka.”

Washegari, sai Mis Shergill ta sanya takalmi mai tsini maimakon wanda ta saba zuwa da shi aiki mara tsini, sai ta shiga bas din, sannan tana dauke da allura a jakarta.

“Yana shigowa, sai ya zo ya tsaya kusa da ni, sai na mike na murje yatsunsa da tsinin takalmina. Ina jin lokacin da ya numfasa saboda radadi, wanda hakan ya saka ni farin ciki. Sai kuma na yi amfani da allurar na tsira masa a hannu, sannan na yi maza na sauka daga bas din.”

Ta ce duk da ta cigaba da hawa bas din, amma tun ranar ba ta sake ganinsa ba.

Labarin nan na Mis Shergill akwai daure kai, amma ba ita kadai ba ce ta taba fuskantar irin hakan.

Wata abokiyar aiki mai kimanin shekara 30 ta bayar da nata labarin irin wannan, inda ta ce akwai wani mutum da yake yawan kokarin shafar jikinta a bas din dare a tsakanin Kudancin birnin Cochin da Bengaluru (Bengalore).

“Da farko ban damu ba saboda na yi tunanin ba da gangan yake yi ba,” inji ta.

Amma da ya cigaba, sai ta gane manufarsa-kuma allurar da take amfani da ita wajen kama mayafinta ne ya ‘tseratar’ da ita.

“Da na tsira masa, sai ya janye jikinsa, amma sai ya cigaba ba sau daya ba biyu ba, amma a duk lokacin da ya matso, sai nima in tsira masa. A karshe dai sai ya janye baki daya. Na ji dadin kasancewar ina da allurar a lokacin, amma na ji haushi da ban juya na gaura masa mari ba,” inji ta.

“Amma lokacin da nake karama, na shiga damuwar cewa idan na jawo hankalin mutane ba dole ba ne su yarda da ni,” inji ta.

Masu fafutika sun ce tsoro da kunyar da mata suke ji ne ya sa masu wannan dabi’ar suke cigaba, sannan yake kara ta’azzara lamarin.

A wata kididdiga da aka yi a yanar gizo na mata 140 a biranen Indiya a shekarar 2021, kashi 56 na matan da aka tambaya, sun ce an taba cin zarafinsu a motar bas, amma kashi biyu ne kacal suka kai kara wajen ’yan sanda. Mafi yawansu sun dauki mataki ne da kansu, wasu kuma suka ki yin komai, inda suke zabi su yi shiru saboda ba sa so su jawo hankalin mutane, ko kuma suna tsoro kada lamarin ya ta’azzara.

Sama da kashi 52 sun ce sun hakura da karatu da aiki saboda fargabar abin da zai iya faruwa da su saboda rashin aminci.

“Tsoron fuskantar cin zarafi yana shafar tunanin mata da zirga-zirgarsu sama da cin zarafin na zahiri,” inji Kalpana Viswanath, wadda take cikin wadanda suka assasa Sfetipin, wadda kungiya ce da take aikin tabbatar da mata suna cikin aminci a ko’ina.

“Mata sun fara takaita wa kansu zirga-zirga wanda hakan yana hana mu samun damarmaki daidai da maza. Wannan fargabar na da matukar tasiri ga rayuwar mata sama da cin zarafinsu a zahiri.”

Mis Viswanath ta kara da cewa cin zarafin ba a Indiya kadai ya tsaya ba, inda ta ce lamari ne da ya shafi matan duniya.

A wata kididdiga da Gidauniyar Thomson Reuters ta gudanar na mata 1,000 a Landan da New York da Mexico da Tokyo da Cairo ya nuna cewa, “motocin haya sun zama matattara maza masu neman matan da za su ci zarafinsu wadanda suke amfani da lokacin da ake rige-rigen shiga mota a matsayin uzuri idan an kama su.”

Mis Viswanath ta ce, mata a kasashen yankin Amurka da Afirka sun fada mata cewa suna yawo da allurar domin kariya. Sannan Mujallar Smithsonian ta ruwaito cewa a Amurka, mata sun kasance suna amfani da allura domin kare kansu tun a shekarun 1990s domin tsira wa mazan da suka matse su sosai.

Amma duk da cewa kasar ta Indiya ce take kan gaba a yawancin kididdigar da aka yi game da cin zarafin mata a bainar jama’a, har yanzu kasar ba ta dauki lamarin a matsayin wata babbar matsala ba.

Mis Viswanath ta ce hakan bai rasa nasaba da rashin bayar da labarin lamarin yadda ya kamata, wanda hakan ya sa bai shiga cikin kididdigar manyan laifuka ba, da kuma tasirin sinimomi da ke koyar da cewa cin zarafin wata hanya ce ta jawo hankalin mata da sunan soyayya.

Amma a shekarun baya, Mis Viswanath ta ce an fara samun saukin lamarun a birane da dama.

A Babban Birnin Delhi, motocin haya sun sa karaurawa da kamarori, sannan an horar da mata da yawa tuki sannan an shirya taruka da dama domin wayar da kan direbobi da kwandastocinsu su kasance masu mutunci da mutunta fasinjoji mata, sannan an tura masu lura da ababen hawa a cikin motocin haya. Suma ’yan sanda sun kirkiri wasu manhajoji da lambobin kar ta kwana wadanda mata za su iya amfani da su idan suna neman dauki.

Sai dai Mis Viswanath ta ce ba wai matsalar sanya musu ido ba ne.

“Ina tunanin hanya mafi muhimmanci da za a bi wajen kawo karshen wannan lamari shi ne dole mu yawaiti yin maganar lamari. Ya kamata jaridu su yada lamarin nan sosai domin tunatar da mutane halayen da suka kamata da wadanda ba su kamata ba.”

Idan ba haka aka yi ba, Mis Shergill da abokiyar aikina da miliyoyin matan Indiya ba su da wata mafita face su cigaba da amfani da allurorinsu.