BBC Hausa of Saturday, 28 January 2023

Source: BBC

Yadda masu haɗa akwatin gawa ke caɓawa a China saboda dawowar korona

File foto File foto

Masu haɗa akwatin gawa da ke Arewacin Shanxi sun kasance cikin aiki ba dare ba rana.

Mun ga yadda kafintocin suke ta haɗa akwatunan gawa daga ɗanyen itatuwa.

A watanni kadan da suka gabata, sun ce aiki kawai suke yi babu kakkautawa.

Wani mazaunin kauyen wanda ya bayyana mana cewa wasu lokutan ma akwatunan gawar karewa suke yi.

Ya bayyana a cikin dariyar mugunta cewa masu aikin binne gawa, “suna cin kasuwarsu.”

Har yanzu ana musayar yawu kan asalin adadin wadanda cutar Covid ta kashe a China tun bayan barkewar annobar da ta tsayar da kasar cak.

Annobar ta shafi kusan kashi 80-sama da mutum biliyan 1-na mutanen kasar tun bayan da ta dage dokokin kariya a watan Disamba, kamar yadda wani likita mai suna Wu Zunyou ya bayyana.

A makon jiya, China ta sanar da mutuwa 13,000 da suke da alaqa da Covid a maka data, wanda ya kara a saman adadin mutuwa 60,000 da aka sanar tun daga watan Disamba.

Amma wadannan mutuwa na asibitoci ne kawai. A kauyuka babu ingantaccen kiwon lafiya, kuma a lokuta da dama ba a kirga wadanda suka mutu a gida.

Babu ma kididdigar wadanda suka mutu a kauyuka a hukumance, amma BBC ta gano alamomin da ke nuna an samu mutuwa da dama.

Mun ziyarci wuraren kona gawa, kuma mun same su suma a cikin aiki ba kakkautawa, inda muka ga masu binne ’yan uwansu suna shiga sanye da fararen kaya dauke da kananan akwatuna da ke alamta a ciki akwai tokar dan uwansu.

A wani kauyen, mun ga wasu mutane: mace da miji suna loda tsuntsuyen da aka hada da takardun bandaki a bayan motar daukar kaya. “Guzuri ne wannan da za su tafi da su lahira,” inji matar.

Bayan sun kammala loda kayayyakin, sai wani hoton abun bautar Buda da aka hada da takardar ya bayyana, inda suka ce suna samun masu bukatar aikinsu da yawa domin su yi musu kwalliyar bikin binne mamatansu, inda suke ce an samu karin masu neman aikinsu ninki biyu ko uku.

Duk wanda muka hadu da shi a yankin Shanxi yana da alaka da wani aikin binne gawa da yake samun kuxi, sannan ya tabbatar da labarin yadda suke samun aiki ba kakkautawa saboda karuwar mutuwa masu alaka da coronavirus.

“Jikin wasu marasa lafiya ya riga ya yi sanyi,” inji wani mutum a lokacin da yake cigaba da loda kaya a motar daukar kayana. “Sai kuma su kamu da Covid, wanda jikin tsufansu ba ya iya dauka.”

Mun bi motar zuwa inda suke kai kayayyakin zanen, inda muka hadu da wani mai suna Wanga Peiwei, wanda bai dade da rasa surukarsa ba.

Surukar tasa mai shekara kusan 50 da ta rasu ta bar ‘ya’ya biyu ta sha fama da ciwon sukari, kafin ta kamu da cutar Covid.

“Bayan ta kamu da Covid, sai zazzabi mai zafi ya biyo baya, sai kuma muhimman gabbobinta suka fara daina aiki. Garkuwar jikinta ba su da karfi sosai,” inji Mista Wang.

A lokacin an fara cika gidan da kayayyakin ado domin biki binne ta. Mista Wang ya fada mana cewa akwai sauran furanni da hotunan da za a kawo.

A tsaye a gaban wata rumfa a gidan da ake ajiye gawar, ya ce a ranar binnewar mutum 16 ne za su dauki akwatin gawar su binne ta kamar yadda al’adarsu ta tsara.

Ya ce duk da cewa bikin binne mamata ya kara tsada saboda karuwar mutuwa masu alaka da Covid, dole za su biya kudin duk tsadarsa domin girmama ta.

“Mutumiyar kirki ce, dole mu girmama ta wajen ban-kwana da ita. Wannan shi ne abun da ya fi dacewa da ita,” inji shi.

Duk shekara, daruwan miliyoyin matasa suna komawa garuruwansu domin murnar karshen shekara. Wannan ne lokaci mafi daraja a China.

Yanzu kauyukan sun fara komawa wuraren da tsofaffi suka fi zama-wadanda kuma su ne cutar za ta fi saurin kamawa.

Akwai fargabar cewa tafiye-tafiyen bana zai iya kara yada cutar coronavirus zuwa kauyuka.

Gwamnati ta gargadi wadanda suke zama a birane da kar su koma gida a bana idan dattawan ’yan uwansu ba su taba kamuwa da cutar ba.

Dokta Dong Yongming wanda yake aiki a wani karamin asibiti da ke wani kauye, yana tunanin akalla kashi 80 da ke kauyan sun taba kamuwa da cutar Covid.

“Dukan  ‘yan kauyen suna zuwa mana ne idan ba su da lafiya,” inji shi, sannan ya kara da cewa, “Mu kadai ne asibiti a nan.”

Yawancin wadanda suka rasu, dama suna da wata cutar daban, inji shi.

A game da yadda suke yin maganin wadanda suka kamu da cutar a kauye, Dokta Dong ya ce ba sa sayar da magani fiye da bukatar mara lafiya.

“Misali, ina bayar da Ibuprofen hudu ne kawai ga mutum daya,” inji shi. “Ba sa bukatar kulli biyu baki daya, domin za a barnatar da shi ne kawai.”

Sai dai ya ce yana da yakinin an riga an wuce lokaci mafi bala’i na cutar. “Kwana biyu ba mu samu mara lafiya ba.”

Wadanda suka mutu a yankin ana binne su a filin Allah. Manoma kuma su cigaba da shuka da kiwo a kan mamatansu.

Da muke tafiya a hanya, mun ga wani waje da aka sanya jar tuta a sama. Wani makiyayi a wajen ya tabbatar da cewa yawancinsu sababbin kaburbura ne.

“Ana yawan binne tsofaffin mutane a nan idan sun rasu. Mutanen suna da yawa sosai,” inji shi.

A kauyen da ya fito mai mutane ’yan dubbai, ya ce sama da mutum 40 sun rasu a barkewar annobar ta kwanan nan.

“Idan yau wani ya rasu, gobe sai ka ji wani ma ya rasu. Haka aka ta yi a watan da ya gabata ba tsayawa,” inji shi.

Amma a yankin, suna bin rayuwa da mutuwa a hankali. Manomin ya ce mutane za su yi bukukuwansu na Sabuwar Shekara kamar yadda suka saba. “Dana da surukata ma suna nan zuwa,” inji shi.

Na tambaya mutanen yankin ko suna fargabar dawowar ’yan uwansu daga birane domin gujewa kara yada cutar.

“Kar mutane su ji tsoro, ba matsala,” inji shi. “Ko ka boye ma za ka iya kamuwa da cutar. Yawancinmu mun riga mun kawo, mun warke muna cigaba da harkokinmu.”

Shi da wasu suna fata an riga an wuce lokaci mafi bala’i na cutar, sannan suna fata akalla ko ba komai, za su yi amfani da lokacinsu da karfinsu domin wasu abubuwan ba wai binne mamatansu kawai ba.