You are here: HomeAfricaBBC2023 01 30Article 1704821

BBC Hausa of Monday, 30 January 2023

Source: BBC

Yadda mahaifiyar Dogo Giɗe ta roƙe shi ya sako ɗaliban sakandaren Yauri

Hoton alama Hoton alama

Shekara ɗaya da rabi ke nan da sace 'yan makarantar Kwalejin Tarayya ta Yawuri, kuma har yanzu akwai sauran 'yan mata da suka rage a hannun 'yan fashin daji.

Rahotanni na cewa akwai wadanda suka haihu daga cikin wadanda suke hannun na 'yan bindiga, baya ga waɗanda 'yan bindigar suka ce sun aurar.

Hakan ne ya sa masu ruwa da tsaki da haɗin gwiwar iyayen yaran suka fara wani yunkuri domin ganin an kuɓutar da sauran yaran.

Wannan lamari dai, na daɗa jan hankula game da gazawar gwamnatin tarayya da ta jihar kebbi, waɗanda aka damƙa wa amanar yaran da suka fita neman ilimi amma rayuwarsu ta ɓalɓalce a hannun 'yan fashi.

Tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kaduna, Kanal Abubakar Ɗangiwa Umar, mai ritaya na cikin waɗannan masu ruwa da tsakin, inda a wata tattaunawa da BBC, ya ce za su yi duk abin da za su iya domin ganin sun kuɓutar da 'yan matan.

Kanal Abubakar Ɗangiwa ya ce sun samu labarin cewa cikin 'yan mata 11 da suka rage, 'yan bindigar sun aurar da su, inda babbansu Dogo Giɗe ya auri ɗaya daga ciki.

Ya ce iyayen yaran sun bayyana cewa mahaifiyar Dogo Giɗe din ta sa baki inda ta buƙaci ya saki sauran 'yan mata da ke hannunsa, sai dai duk da haka ya gindaya wasu sharudda na kai kudade kafin ya sake su.

Ya ce iyayen yaran na nan suna fafutikar ganin sun nemi abin da za a yi amfani da shi domin karbi ƴaƴan nasu.

"Hukumomi sun ce za su iya ƙwato yaran amma suna tsoron ta ya ya za a yi wannan aiki ba tare da an samu rasa rai ba, don haka an yadda da batun tara kuɗin,'' in ji shi.

Ya ce tashin hankali da bakin ciki da kuma kunci ya kai ga har wasu uwaye guda uku sun rasa ransu.

Matsalar garkuwa da mutane dai na ci gaba da zama babbar barazana a Najeriya inda alkaluma ke nuna cewa an sace sama da dalibai 1,000 da malamansu a hare-hare daban-daban da masu garkuwa suka kai makarantunsu a fadin arewacin Najeriya.