You are here: HomeAfricaBBC2023 01 28Article 1703759

BBC Hausa of Saturday, 28 January 2023

Source: BBC

Yadda fesa turaren gwangwani ke kashe kananan yara

Hoton alama Hoton alama

Mahaifi ya gargadi al'umma bayan da 'yarsa mai shekara 14 ta mutu bayan ta shaki iskar turaren gwagwani

Iyayen wata yarinya da ta mutu bayan ta shaki iskar turaren gwangwani, sun ce ya kamata a rika wallafa gargadi mai karfi a jikin gwangwanin turare domin kare jama'a daga fada wa cikin mawuyacin halin da suka sami kansu.

Zuciyar Giorgia Green, yarinya mai shekara 14 daga garin Derby, ta daina aiki ne bayan da ta fesa wani turaren gwangwani a cikin dakinta.

Tuni dai iyayenta suka fara nuna damuwarsu kan aukuwar lamarin, inda suka gano cewa wasu matasan sun rika mutuwa bayan sun shaki iskar turaren gwangwanin.

A nasu martanin, kungiyar masu hada turaren gwangwani ta Birtaniya (BAMA), ta kare kanta, tana cewa akwai gargadi a jikin kowane gwangwanin turare da suke samarwa.

A tsarin dokokin Birtaniya, dole ne a wallafa gargadi a jikin ire-iren wadannan turarukan kamar wanda ke cewa "A kawar da wannan abin daga inda hannayen yara ka iya kai wa."

Sai dai iyayen Giorgia sun ce bakaken da aka yi rubutun gargadin sun yi kankanta matuka.

Sun kuma ce yawancin iyaye kan sayo wa 'ya'yansu irin wadannan turaren gwangwanin ba tare da sun lura da gargadin da ke jiki ba.

"Ba ma son mutuwar 'yarmu ta tafi a banza, shi yasa muke jawo hankulan jama'a kan hadarin da ke tattare da amfani da turaren gwamngwani."

Giorgia dai matashiya ce mai fama da lalurar galahanga, kuma mahaifinta yace tana da sha'awar fesa turaren gwangwani kan barguna domin kanshinsa na kwantar mata da hankali.

Ya ce 'yar tasu kan fesa turaren saboda mahaifiyarta na son kanshinsa, abin da yasa ta saba da shi.

Yayan Giorgia neya gano ta kwance cikin dakinta ba ta numfashi a ranar 11 ga watan Mayun 2022.

"Kofar dakinta bude yake, saboda haka ba karancin iska ne ya janyo mutuwarta ba", inji mahaifin nata.

Likitoci sun gudanar da bincike kan gwar Giorgia, kuma sun ce tsautsayin shakar iskar turaren ne yayi sanadin mutuwarta.

Baban nata ya ce, "Babu wanda ya san yawan turaren da ta shaka, amma a fili yake cewa yafi karfin wanda ya dace a rika fesawa. Zuciyarta ta daina bugawa bayan wani lokaci da ta shaki iskar turaren."

Ofishin Kididdiga na Birtaniya ya ce an ambacin irin wannan turaren da ake fesawa mai suna "deodorant" da turancin Ingilishi har sau 11 a katin shaidar mutuwar wasu mamata tsakanin 2001 da 2020.

Wani binciken gwamnatin Birtaniyar ya ce an sami mace-macen kananan yara da matasa bayan sun fesa turaren gwangwani.

Ciki akwai Daniel Hurley, wani yaro mai shekara 12 daga garin Derbyshire wanda ya mutu bayan ya fesa wa kansa turaren gwangwanin a dakin wanka.

A bayan nan kuma, Jack Waple, mai shekara 13 ma ya mutu, mutuwa irin ta Giorgia a 2019.

Wane irin gargadi ake wallafa wa a jikin gwangwanin turaren da ake fesawa?

Dokar Birtaniya ta tanadar da a wallafa gargadin da ke cewa a kare kananan yara daga mu'amula da ire-iren wadannan kabubuan da ake fesawa.

Akwai kuma wani gargadin da ake wallafa wa da ke cewa "yin tu'ammali da irin wannan sindarin ka iya kisa nan take" .

Doka ba ta bukaci sai masana'antu sun yi haka ba, amma kungiyar kamfanonin da ke hada turaruka da abubuwan da ake fesa su kamar maganin sauro na yin haka ne domin hana mutane shakarsu.

Ana cewa shakar su kan sa masu yin haka su rika yin maye.

Iyayen Giorgia na son a sauya sakon da ake wallafawa ya koma "tu'ammali da wannan sinadarin na kisa nan take", saboda 'yarsu ba ta rika amfani da turaren fesawar ta hanyar da ba ta kamata ba.

Kana idan abin fesawar na kama wa da wuta, tilas a awallafa wannan hadarin a jikin gwangwanin.

Kungiyar BAMA ta fitar da wata sanarwa kamar haka:

"Kungiyarmu ta BAMA ta dauki al'amarin da kan janyo rasa rai ko rauni da muhimmanci sosai, kuma muna jimamin mutuwar wannan matashiya mai kananan shekarau."

Kungiyar ta yarda da iyayen Giorgia cewa ya dace a kara bayyana wa jama'a hadarin iskar da ake fesawa, ta hanyar rubuta wasu jerin sababbin gargadi ko da kuwa doka ba ta bukaci yin haka ba.